ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

abdallah ta taras yayi daidai yana kwasar garar abinshi,bata ce komai ba ta juya ta bar gurin ta shige bangaren mamin
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:54 PM] 80k: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶3⃣3⃣
????????????????????????
godiya ga masoya na????????????❤????
masu qaunar rubutuna????✍????
qaunar da kuke min bazaiyu na manta da ku ba,na yaba qwarai da gaske????????
gaisuwa ban girma da jinjina mai qima ga
huguma novels room and huguma conversation room
maman aysha novels group
hausa novel group by umar dalha 1&2
zama na amana group facebook
khafinga group 2012 class
gaisuwa kai tsaye zuwa ga GARKUWAR ABADAN SISTER RABI’ATU HARUNA????????
Allah ya barmu tare ya samu cikin masu son juna saboda shi da zuciya guda ameen
rabbanag fir lana wa li ikwaninallazina sabaquna bil eman wala taj’al fi qulubina gillal lil lazina amanu rabbana innaka ra’ufur rahim????????
Sau biyi tana zuwa dubawa taga ko ya kammala sai tazo ta tarar bai gama ba,sai a zuwa na ukun ya sameshi ya ture kwanonin gefe alamun ya kammala kenan,bata ce da shi komai ba ta soma hada plates din guri guda tq zuba cikin kwandon
”ji mana”taji yace da ita,a hankali ta dago kai suka jada ido,ya kafeta da zaratan idanunshi sai ta kau da kanta gefe
”idan kin koma kuma ki sake hada ni da mami na kice ni naci abincin,ko da yake ko kin fada din dama ai aikina aka dauko ki yi ba wai ki dafawa wani qato ba,a qa’ida ma idan kika kuma gigin yiwa wani girki ba da izini na ba ma a albashinki”
ya ture kujerar da yake kai baya ya miqe ya kewayeta ya wuce,ta biahi da kallo tsanarsa da tsanar halyenhi na takura matsi da girman kai na addabar zuciyarta,sai da ta tabbatar ya ahige bangarenshi sannan ta shiga nasu bangaren
????????????????????????
da yake azumi ne qarfe tara ta shirya taje gida,ita da hindatu suka tattauna abinda za’a shirya don ‘yan kawo kudi da zasu zo jibi da safe,ruwan roba ta siya carton biyar na lemo ma haka,sai maltina itama carton uku,kujerun da aka fidda dakin mama su aka maida sitroom dinsu wanda rashin wadata yasa yake fanko babu komai a ciki,babu abinda kujerun sukayi tunda ba’a dade da yi musu kwaskwarima ba ta qarin katifa da canza yadin kujerar kuma ba yara gareta ba balke su lala ce da wuri,ko dama can ita mamsn mai tsumi tattaku da tanadi ce,ta siyi leda da labulaye duka aka sanya,sai sitroom din yayi kyau daidai talaka,tuni dama kayan gadon maman aka shiryashi bedroom din baban sun zama nashi
muqullin ta danqa hannun hindatu don tana jin su kula na rawar kan yau a ciki zasuyi zance don duka babu wanda yasan me za’ayi da dakin aka gyara shi haka,wannan rufewa fa da tayi sai taso zama dan zani sukayi dafifi a tsakar gidan suna basu amince ba ai gida dai na ubansu ne babu wanda ya isa ya musu shamakivda wani bangare na gidan,shigowar baban ya tambayi ba’asi wannan karon hindatu ce tayi uwa tayi makarbiya ta masa bayani
to shi din ma wannan karon bai basu goyon baya ba yadda suka saba samu,hakab ba qaramin qullacinsu maryam ya sake sa musu ba,da azahar sukayi sallama don tana so ta leqa raliya,mama ta dakatar da ita tana fiddo da dararen borikan fenti uku daga uwar dakanta
”me wannan a ciki mama?”ta fada tana budewa
botikin farko alkaki ne a ciki
na biyu dubulan
na uku nakiya ce
ta dago ta dubi maman
”duka na meye wannan?”
”saboda ‘yan kawo kudin nsn nasa akayi,kinga za’a kuma fita kunya ko”qauna da tausayin mamanta ya sake shigarta,Allah sarki mama,farincikin dake zuciyarta Allah kadai ne ya sani,a haka ma tana alkunya tana danne farincikin nata sabida kara irin ta dan fari
”Allah ya saka da alkhairi mama sunyi,Allah ta qara arziqi,amma mama banason ki dinga tatse kudin hannunki haka,yanzu wannan kayan ai sunci kudi da yawa”
”ai aikina ne maryamu,idan da da akwai cikakkiyar wadata ma baki cancanci ki kiyi komai ba”
????????????????????????
qarfe biyu da rqbi suna falon raliyan su biyu sai fadil dake kwance kujerar geansu yana baccinshi hankali kwance,cikin farinciki raliyan take tamkar ma itace maryam din
”wani hanin ga Allah baiwa ne maryam,yau gashi Allah ya musanya miki da jabir,sun sanya bawan Allah a tsaka mai wuya har yau yana cikin damuwa,shekaran jiya yazo gidan nan yake tambayar abban fadil ke,yana son ya nemeki amma wai kunyarki yake ji,shegiyar yarinya marasa tsoron Allah itavda uwarta,duk jabir ya fita hayyacinshi kmar bashi ba,roqon Allah ne masa ya dawo cikin tuna ninshi cikin lokaci qanqani haka”
ajiyar zuciya ta saki
”duk wanda ya debo da zafi ai bakinsa raliya,nikam wanna ya riga ya wuce tamkar wani mafarki na daukeshi”
ta zura hannunta cikin jaka ta soma laluben wayarta dake ringing hade vibration ta cirota,kiran abdur rahim ne tasan shi dinne tun kafin ta ciro saboda special tune da ta sa masa
”ranki ya dade duka yau ban jiki ba ko cigiya ta baki yi anya kuwa”ya fada cikin salin zolaya bayan sun gama gaisawa
murmushi ta saki
”yau na tashi ne cikin sabgogi amin afuwa”
”ayyah,da kinyi magana ai da nazo na tayaki,ina fata basu wahalmin da ke ba”
”alhmdlh tunda tuni na kammala yanzun nake shirin in koma gida”
sai ya danyi duf kana yace
”me yasa baki tambayeni ba da zaki fita,saiki dinga fita kanki tsaye maryam ana ganemin ke”
murmushi ta saki
”mantuwa nayi ashe fa yanzun ina da miji,baza’a sake ba”
”matsalar ban iya fushi dake maryam,yanzun dai sgikenan kimin kwatancen gidan da kike zanzo yanzun nan na maidake gida,naga hadari na haduwa kada ruwa ya dakarmin ke ya barni da zazzabi”
ba qaramin nishadi maganar ta saka ta ba ,take ta masa kwatancen inda take din sukayi sallama ta ajjiye wayar
suka hada ido da raliya tare suka saki murmushi
”gaskiya na fuskanci ba qaramin ji dake abdul din nan yake yi ba,Allah ka nuna mana wannan rana”
dariya tayi gami da dukan gefan cinyar raliyan tace
”har ya kama qafar nasir abban fadil”suka sake sa wata dariyar raliyan na fadin haba wane mutum
minti goma wayar ta sake kadawa,abdur rahim tayi tsammani shi dinne kuwa
”kiyi min afuwa maryam zuwa na bazai samu ba wani aiki ne na gaggawa yanzu aka turamu dole kuma na kasance aciki idan ba haka ba akwai matsala,amma kiyi sauri don Allah ki koma gida hadari ne sosai a garin kada ruwa ya tabaki”
macace mai sauqin kai da fahimta don haka tace masa
”babu damuwa Allah ya bada sa’a”
ya saki ajiyar zuciya
”na gode da kika fahimceni sai munyi waya”
ta dubi raliya bayan ta miqe tana hada jakarta,ta tavbata hadarin ne don tuni garin ya lumshe har ta soma jin quginsa
”wucewa zanyi raliya an samu matsala abdul bazai samu zuwa ba aikin gaggawa nebya taso muau yanzu a office”
”a’ah,yanzu da uban hadarin nan zaki tafi?ki jira abban fadil ya dawo sai ya kaiki”kama baki tayi bayan ta gama rolling mayafinta
”girkin kuma na barwa wa?,so kike kenan yau abdallah ya samu nayi ko,cikin watan nan ya tairi wani abu ko kunu ne idan bani nayiba sai ya gane,yanzun sai yace a salary dina”
ta dage girarta sama
”haka ne fa,muje in taka miki,amma jirani in shiga in fito”cewar raliyan tana shigewa bedroom dinta na qasa