ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

kwalbar turare ta fito da shi hade da baqar leda qarama ta miqa mata
”turaren da kike ce min kina son irinsa nasa abbn fadil ya aiyo manaamma kiriqe da kyau saboda yana leeking,sai bra din nan qualitative one da mukayi maganarta jiua da muka fita na siyo mana”
”kai qawata,bani da bakin magana,Allah ya raya mana fadil ya bar mana zumuncinmu,ya tsone idon maqiya”
”ameen raliyan ta fada tana bin bayanta,haduwar jadarin ya sake rudata har ta kasa saka kayan cikin jaka,a bakin get suka rabu ta soma sauri gashi ita ba gwanar saurin bace

har ta kai bakin titin su raliyan bata ga abun hawa na haya ba,kusan dama haka yanayin unguwar tasu yake ko jama’a baka fiya gani ba,bare yanzu yanayi na azumi kowa yayi likimo cikin gida,hankalinta bai daga ba sai data tsaya atitin,taga motoci dake karakaina ma baifi ka irga au ba,adaidaita uku ne suka wuce biyu daga cikinsu duk cike take da mata dayarkuma maza ne cike har gaba kusa da mai tuqin,a hankali iska ta soma kadawa mai qura alamun dake nuna hadarin ya gama nuna a sama sauka kawai yake da buqatar yi,addu’a kawai takeyi cikin zuciyarta a haka ruwan saman ya soma sauka

tsamo tsamo tayi don ya fara jiqata ta soma hade jikinta guri daya,motoci uku ne qirar land cruisser baqaqe wul hatta da glass dinsu suka tsaya a gabanta,gabanta yayi mummunan faduwa,tuni ta somacwaige waigen neman inda zata fake idan gudun ceton rai ya kama

glasan motar farko nagaba mazaunin mai tuqi suka sauka qasa,hassan ta gani daya daga cikin direbobin abdallah,sai a likacin taji ta samu nutsuwa,murmush yayi nata itama ta maida masa
”madam yi sauri ki shigo kina ta jiqewa”
taji dadi sosai kuwa,da saurinta ta qaraso ta bude mazaunin gaba ta shiga tana fadin
”na gode qwarai,amma ba tare kuke da og…..”
”me muka tsaya yine hassan?”
muryar data fito daga sit din baya ta katsse mata sauran magan
”nun dauko madam ne”ya fadi yana qoqarin tayar da motar
”waya baka izini ko tsabar iya sayawa mutum raini ne?”
”sorry sir,naga gida zamu ne,kuma itama gidan zata…..”
”ni na gaya maka haka?”ya tambaya murya a kaurare

”am sorry sir naga madam nada kirk…….”
abdallah ya katseshi ta hanyar fadin
”mtswee,shutup malam sauka ka barmin mota ka koma motarsu auwal”
da saur maryam ta kuma riqe jakarta wadda garin saurin ledar hannun ta har ta subuce ta fadi qasan motar bata sani ba
”kayi haquri,ni ya kamata na fita ba hassan b…..”
”hey,bana son iyayi shi nace ya fita din bake ba”

tuni hassan ya bude motar ya fice ganin hakan ya sanya itama ude na bangarenta tana qoqarin fita
”idan kija sake kika fita sai na karya sillar qafar taki inga ta rashin kunya”
tilas tana ji tana gani ta koma ta zauna
”rufemin mota malama don idan ruwa ya jiqata sai kin busar da ita tas a yanzu yanzu”taja qofar garam ta rufe cikin haushi,tana iya gano ragowar motocin suka zagayesu suka wuce

mujallar da yake research kanta tun dazun ya sake janyowa ya bude yaci gabavda karuntunshi hankalinshi kwance tamkar yana cikin dakinshi ne,sanyin a c din motar ya soma takurata gashi tayi mata kusa da yawa,tuni kanta ya fara sarawa ta qudunduna gu guda tarw da jingina jikin makarin motar ta lumshe idanunta tana ci gaba da jin yadda ciwon kan ke dada yin gaba

‘yar qaramar qara taji tamkar ta waya ”siiit”a hankali sai dumi ya maye gurbin sanyin ac din,bata tantama maidashi akayi banaren dake bada dumi,duk da taji dadin hakan amma babu abinda ya rage mata daga ciwon kanta

mintina kusan arba’in basu tafi ba kamar yadda ruwan bai tsagaita ba,ta bude idanunta a hankali ta miqe ta zauna daidai,a karo na biyu ta kuma sanya hannunta kan mabudin qofar don ta qudiri aniyar ficewarta zatayi kome zaiyi mata saidai yayi,saidai taqi buduwa da alamu an saka lock,ya ajjiye mujallar hanun nashi ya jawo baqin space ya mannawa idanunshi sannan ya bude ‘yar qaramar kyakkyawar baqar lemar dake kusa dasji ya fito ya dawo mazaunin driver

amadadin ysyi hanyar gida sai taga sun csnza titi,batason kulashi amma ya zama mata dole
”ina cewa gida zammu ko”
banza yayi da ita,ta qufula amma bata fasa sake fadin
”girki fa na can na jira na gashi yanzu hudu harda rabi”
”karki cika ni da hayaniya,baki da zance sai na girki kamar dinshi aka halicceki,ai bake daya kika iya girku cikin gian ba ko”
ya fada udanunshi na bisa kwalta,bata sake tofawa ba ta maida kanta gefe daya

cikin wata unguwar taga sun shiga wadda take kama da tasu mamun wajen kyau da tsari,qofar wani katafaren gida taga ya tsaya,ita kanta sai da ta bi gidan da kallo,duk kyau na gidansu mamin wanna ya dokeshi,bude motar yayi yay ficewarsa ba tare da da yace mata komai ba

zaman kusan awa guda da rabi tayi kafin ta sake ganin fitowarsa,a dan bakin qofar ya tsaya kafin ya qaraso tana iya hango jikin wanda suke magana tare,da alama macece don ga gefan mayafi nan,ba qaramar qufula tayi,ba cikin zuciyarta
”zance yazo kenan ya barni a mota ko yaya?”ranta sai ta kuma ji ya baci,ya bude motar ya shigo
”zance da ranar Allah cikin watan azimi,wanne wane irin tsari ne”ta ja tsaki,saidai cikin subutar baki tsakin ya fito

juyowa yayi kalleta
”wa kike ma tsaki?”sai ta juyo tana kallonshi itama
”idan kika sakemin tsaki sai kin fita min a mota tunda bada kudinki aka siya ba”sai idanunta suka wal
”daina kallona”ya fada bayan ya dauke kanshi da sauri daga cikin idanunta
”kada ki cuceni”ya fadi can qasa yana lumshe idanu tarw da yiwa motar key,bata kawo komai cikin ran ta ba ta dauke idonta cike da jin haushinsa

????????????????????????

Ashirin ga azumi mami ta bata kayan sallarta,a dinke suke dinki ne na gayu wadanda suka mata cif a jiki,atamfofi uku lace daya material daya,sai codelace shima daya,duka atamfofin dogayeb riguna aka mata don mamin ta fuskanci tana sonsu,jaka biyu takalmi biyu sai mayafi biyu hijabi daya,sannan tace ashirin da biyar ga azumi zasu fita sai ta zabi fashion da zatayi amfani da su,bata fasa yiwa mami gidiya ba duk da ta gaya mata diyarta ta yiwa no need tace sai ta gode mata,godiya kuwa ai tamkat wajibi ne tayi mata don ko daga gurin mahaifinta bata taba samun makamancin irin wannan gatan ba

abida kam akwati guda medium abdallan ya hada mata bayan takurawar da mami tayi masa kan ya hada matan,don shi totally baiyi niyyar mata komai ba

cikin irin kyautar da mamin ke yawan yi mata ta fidda atamfa biyu ta baiwa tela ya dinkawa mamanta,ta siya mata mayafi takalmi da jaka,albashinta na watan ciki ta cira ta baiwa hibdatu tayi siyayyar salkarta babanra ma shadda ta siya masa kala biyu ta hada mishi da kudin dinki da takalmi da hula daidai,kai kada ksso kaga baqinciki,ina wuta a saka maman da iyalsnta,godiya kam gun baban ba’a magana
”sai yanzu nasan na haifa,yanzu ne na fara cin albarkar haihuwa”baban ya fada lokacin da yake gwada hular da ta kawo masan

”oho dai,wlh malsm ka guji ranar da zaka karbi shegen jika cikin gidan nan,ka gama cin dadin dai wuyar na tafe,shi yasa gata nan har yau babu mashinshini yo kowa yasan aikin tsiyar da take aikatawa”
inji baba hadizar don daga ita har huwailsn babu wanda yasan da zancan kawo kudinta,ranar kamar Allah ya kadasu duk suka fice unguwa suda qananun ‘ya’yansu,huwaila tayi gurin boksn boginta ita da uwale hadiza ma ta bazama ga nata bokan,sunacan yawon asara har yan kawowar suka tafi,’yammatan da zawarawan kuma na nade a gado suna bacci don wadan nan sukan kai sha biyu da rabi zuwa daya basu tashi ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button