ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

huwaila kuwa cewa tayi”mu namu ai shegensu mukayi muka shigo dasu gidan ko,ko ince tsinannu ne”shidai babu wadda ya kula cikinsu ya kwashe kayanshi ya shige dakinsa
????????????????????????
Qarfe goma suka dawo daga siyan kayan kwalliya da suka fita harda mami da abida,tayi sallama da mamin ta shige dakinta don da wuri take son yin bacci ta tashi akan lokaci sallar dare saboda yau an kai azimi ashirin da shida zuwa anjima daren ashirin da bakwai zai shi daren da akesa ran dacewa acikinsa
zuwa sha daya na dare takammala komai ta haye gado bayan ta gama addu’o’in kwanciya ta karanta saqon abdur rahim fuskarta fal da murmushi,kusan cikin watn gaba daya wayarsu bata fi aqirga ba sai tex akai akai,yace shikam bazai iya jurar jin muryarta ba,tana shirin kashe wayar kira ya shigo,ta zubawa lambobin ido tana kallonsu,tana tunanin inda ta taba saninsu
tabbas ta taba sanin numbers din,har wayar ta tsinke ta kasa dagawa,second biyar tsakani wani kiran ya kuma shigowa,jiki babu qwari ta sanya hannunta ta daga ta kara akunnenta
”assalamu alaikum wa rahmatullah”itace abinda yavdaki sodon kunnenta,mummunar faduwa gabanta yayi,babu inda zata ji muryar ta kasa ganeta,amma tan tama take kiran nata ne ko batan kaine,ta sake cire wayar akunnen ta tayi ta kuma duba screen din wayar mai kiran dai na bisa layi kuma ita din aka kirar
mrs muhammad ce????
????????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:54 PM] 80k: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶3⃣4⃣
daga abu hurairah Allah ya qara yarda da shi yace:an tambayi manzan Allah s a w wanne musulmi ne yafi falala?,sai yace:wanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da sharrin hannunshi(ma’ana bai cutar da kowa da harshensa ta hanyar magana,ko kuma da hannunshi ta hanyar ayyukansa,daure ka/ki zama daga cikin musulmin da suka fi falala,abun ba wuya ????????matuqar ka jajirce kafi qarfin zuciyarka,Allah ta bamu iko ameen)
”wa alaikumus salam”ta fada asanyaye
shiru ya dan ratsa tsakani kadan
”da alamu baki ji dadin jina da kika yi ba ko maryamu?,hala ma kin manta da ni?”
”ko daya,ban kuma mance da kai ba”
”da fari kafin nace momai maryam,nasan bani da kalmomin da zasu gamsar da ke gurin ban haquri,amma duk da haka ina roqarki don Allah don annabi ki yafemin,ba da gangan abinda ya faru tsakaninmu ya faru ba,bada sani na bane maryam,ki yafewa jabir masoyinki”
tausayinshi ya kamata ta dan kumshe idonta kadan ta bude
”kada ka bata bakinka gurin bani haquri jabir,tuntuni gaskiya ta dade da yin halinta,anyi walqiya komai ya bayyana”
yaja dogin numfashi kana ya sauke ajiyar zuciya
”alhamdulillahi rabbil aalamin,dukkan godiya ta tabbata ga Allah,babu shakka ke din jaruma kuma nagartacciyar masoyiya ce,bana tantama zaki zama mace ta gari uwa ta gari gurin ‘ya’yanta,bazanyi nauyin baki ba ba kuma zanyi qauro ba maryam inason ki bani damar fitowa neman aurenki karo na biyu,tare da cikakken fatsn babu wani da ya sha gabana”
sai da gabanta ya fadi,tayi shiru tana son daidaita bugun zuciyarta sannan daga bisani tace
”qaddara ta riga fata jabir,Allah ya qaddara run da dama ni ba matarka bace,hakaza matar mutum kabarinsa,bai wuce sati biyu da kawo kudin aure na da wani ba”
”la haula wala quwwata illah billah”ita ya dinga maimaitawa tsawon mintina biyar
”yanzu kina nufi maryam na rasa ki kenan,zaki auri wani na?,ki bani dama maryam mai rabo shi zaya samu tunda har yanzu ba’a daura aurenku ba balle kice kin haramta a waje na”
”kai mai sani ne jabir bakin gwargwado,ka sani cewa nema akan nema haramunne,baya ga haka ma daga ni har kai babu wanda aka bawa qudirar rubuta kundin qaddararsa da kansa,kuma buwayin sarkin dake rubuta msna din mai dumbin adalci ne,babu yadda za’ayi ya rubuta mana abinda zai zama zalunci ne a garemu”
”haka ne maryam,alhndlh Ala kulli hal,na gode maryam,na gode matuqa da gaske,bazan taba iya mantawa dake cikin kundin rayuwata ba,na barki lafiya”
tafi minti biyar riqe da wayar ra kasa ajjiyeta,tausayin jabir dinne kadai ke dawainiya da ita,babu shakka bazata iya manta dumbin alkhairansa gareta ba,koda ta tashi sallar dare bata mantashi cikin addu’o’inta ba,ta roqa masa alkhairi mai yawa kamar yadda a baya yayi nufinta da shi
????????????????????????
Washegari mai lalle tazo yi musu,babu yadda mami batayi da abida ba amma qememe taqiya,tabe baki tayi
”nifa mami ba za’a batan hannu ba hakakawai da wannan abun”
”banda abinki ai shi jan lalle ga mace sunna ce baya ga haka ma ado ne”inji mami
ta sake ya mutsa fuska
”um um,a muku dai,mukam a turkey bamu irin wannan abun”ba wanda ya kuma tanka mata cikinsu nanta kwanta tun tana kallin qunshin har bacci yayi awon gaba da ita
kamar ko yaushe suna table don cin abincin buda baki u ukun maryam mami da abdallah,ta zubawa mami da abida ta soma zuba na abdallah,ya dago da sauri don yaga iya wanda zata zuba din don vaiso ta cika masa plate kamar na jiya,idanunshi suka sauka kan zara zaran fararen yatsunta da qunshin yayi kwanciyarshi kai ya sake fidda kyawun hannunta,farar fatarta ta sake shar
Zanen ya burgeshi duk da ya saba gani lokaci lokaci gun maminshi,duk kuwa sanda tayi din tun yana yaro ya dinga cewa tayi kyau kenan,maryam ta janye hannunta bayan ta ajjiye nasa plate din ta koma mazauninta,sam babu wanda ta lura sai abida,kishi ya cikata har taji kamar ta guntike hannun maryam din,ya janye idanunshi daga kan lalken suka hada udanu da abidan
”ke ina naki kwalliyar?”
”abida kam ai ta manta gargajiyar al’adarta,tace bataso bata mata hannu za’ayi,bayan shi kanshi ma ganine”
caraf abidan tace
”naga kamar ya burgeka ko,ba damuwa sai amun gobe”
tabe baki yayi ta daga kafadarshi hade da ware ya tsunshi
”no,idan ta nine kada ki sauya ra’ayinki ki bata hannunki”ya qarashe zancan yana jan plate dinshi ta soma cin abincin
zahariyya ce tayi sallama hannunta duka biyun dauke da foodflask masu azabar kyau da tsada,fuskarta a washe da faea’ar data qiqirarwa kanta ta qaraso gun,ta fara da dora flask din duka saman teburin wadanda tunda aka shigo dasu maryam take jin matsananciyar faduwar gaba ta kuma kasa daina kallonsu,mami ta gaida kana abdallah,tsakanin ita da abida kuwa babu wanda ya kula wani kowa na ji da danbanzan girman kanshi rawanin tsiya
”favourite food na ya abdallah nene ra tashemu sai da mukayi masa wai yadda ta saba sanda alhj baaba(alh abdulkareem mai nasara kenan mahaifin abdallah)yana raye wai yanzun ma ba zata fasa ba”
murmushi mami tayi tana janyosu gabanta tare da fadin
”kai kice mata kam mun gode qwarai,kamar kuwa tasan yau bamuyi girki ba nace maryan ta bari sai sahur aikin yayi yawa”inji mami sanda take hude flask din,rake kuwa qamshi ya cika gurin
”ki mata godiya”inji mami sanda zahariyyan ke nufin fita
”zata ji kam”ta amsa mata lokacin da take qoqarin sanya qwayar idanunta cikin ta maryam a fakaice,cikin sa’a kuwa suka hada idon,wanu mummuna kallo mai cike da gargadi da jan kunne tayi mata kana ta fice