ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba daya ta saki cin abincin ta zurfafa cikin tunanin yadda zata salwantar da abincin ba tare da tabar kowa ya dandana ba,tayi imani komai zasu mata ba zata iya bari tana gani gaban idonta wannan ahli su salwanta ba,qarshen butulcin da zata musu kenan wanda ba zata iya yafewa kanta ba har abada,cikin haka taga mami na kiciniyar bude food flask din zata zuba,da sauri ta miqe tana fadin
”mami barshi in zuba miki mana ”tuni har ta isa gabanta ta karba don kada ta yanke mata hanzari tace ta barshi,ta jawo flask din miyar gaban table din sosai ya zama rabi kan tebur din yake zaune rabi kuma free ba matokari,sai ta jawo na abinci ta bude,da plate a gabanta amma sau tayi dabarar miqa hannunta tavdauko na can sashen da abida ke zaune
Tana daukar plate din ta sakeshi kan flask din miyar take nautin tangaran din ya rinjayeshi sukayi qasan table din suka tarwatse kan tiles,tangaran din ya koma piece,taja baya da sauri tana salati tate da kallon gun da abincin suka kife
”subhanallahi ya haka maryam?”
”for god sake mami yanzu wannan wane irin kidahumanci,ita din qaraman yarinyace da zata kifar da abinci flask biyu,kayi magana kuma yanzun mami ta ji haushinka ta saka a black list”ya qarashe maganar cikin bacin rai yana yayyarfa hannu da jujjuyawa hagu da dama kan kujerar da yake zaune
harara ta balla masa sannan ta kalli maryam
”ina fata baki ji ciwo ba maryamu”
kai ta gyada zuciyanta na wani irin gudu gefe daya kuma tana hamdala ga madaukakin sarki da ya bata nasara a sauqaqe ta rabasu da abinda zaya hallakasu,ita ta tsaya ta gyara gurin duk da momi tace ta bari sai ta huta tukyn amma sam ta qiya,bazata iya ba don ko quda bata fata ya dandana abincin,balle ma ta tabbata ban da awa biyu ko uku indai da gubar abincin zai fara ratattakewa
ta gyara gurin tsaf ta kwashe bayan ta rage kadan ta samu yar roba ta zuba hade da miyarshi ta shige da shi dakin gadonta ta tura ahi qasan gado,sai da ta gama komai kafin ta kwanta ta jawo robar don dubawa,cikin awa uku abincin ya fita kamanninsa kamar wancan,batasan lokacin da hawaye suka soma zuba daga idonta ba
mutum abun tsoro Allah abun tsoro
yanzu dan uwanka bil’adama kake da buri yaci wannan abun?
waishin wanne rin laifi ne abdallqh ya yiwa mutanen nan ne haka da zafi da suke da burin rabashi da soron duniya?
sai kace mudin an mana wahayin tabbata acikinta?
kwana nawa ne kaima ka hada ya naka ya naka ka qara gaba?
koda shekara miliyan zakayi wataran dai sai sun qare din ka tafi.
itakam ko kadan batq ga abun morewa ba wajen cutar da wani bayan ka san cewa Allah bazai taba qyaleka ba sai yabi kadi,duk wanda yaci nanin nanin dole ta cishi
cike da kasala da mutuwar jiki ta shige toilet dinta tayi plushing din duka abincin ta wanke robar ta wullar a dust bin
????????????????????????
Sallah bikin daya rana,cike da walwala farinciki bikin sallah ya soma gudana cikin duniyar musulmi baki dayanta,sai a lomacin mayama ta dinga ganin dangin su mami da na mahaifin Abdallah,don kusan kullum ne sai sunyi baqi,saboda haka bata samun zama aosai,damuwarta daya ma kada abdur rahim yace zaya zo ya samu bata da lokaci sai gashi bai ma nemi zuwanba iyakaci waya sai saqon,barka da sallah daya turo mata na credit din dubu goma yace kuma ta jirayi kayan salarta duk ranar da zaya zo
Ta fuskanci ba kadan bane maso sun abdallah cikin danginsa daga na mamin har na abbaanshi,kishi ke hana abida zama ciin gidan tayi ficewarta yawo sai dare
”rashin sani yafi dare duhu”maryam kan fadi hakan cikin zuciyarta ko kuma tace
”bonono rufin qofa da barawo”a duk sanda taga abida na wannna haukar kishin nata don bata da masaniyar kai kudi abdallah daga ita har zubaidan bare salma da saddiqa da bama ganinsu ake ba,har ga Allah tausayinta takeji kan fadawa son botsatstsen mutum irin abdallah,wanda koda yana sonki zaki sha wuya da shi bare kuma baiyi da ke a ganinta
hudu ga salla suka fara samun sararawar baqin duk da ana cikin dai hidimar sallah da shagulgulanta
da la’asar ne babu dadewa da gama salla wayarta ta fara ringing,tana kan cinyarta din haka ba jinkiri ta daga,muryar jabir ta tsinta yana mata sallama,ta amsa masa kana suka gaisa amutunce
”mai yayi zafi haka ido zaici wuta maryam,a qalla dai ai ko barka da salla a kirani ayimin”
ta dan saki murmushi
”kayi haquri,na ahiga sabgogi ne da yawa,ayyuka sun kacame min kusan yaune ma kadai na dan samu kaina”
”gaskiya ne,ai manya dama sai da uziri”dariyar zolayan da yayi mata tayi,kafin tace komai ya dora da fadin
”ko zan iya ganinki,maryam?”tavdan fiddo ido waje kamar yana ganinta
”yanzu?”
”eh idan da zan samu yau din da nace miki na gode,amma da zakimin alfarma da sai mace miki mu hadu gobe”
tunaninta daya ina zata ce mishi su hadun?,sam bata da sha’awar kawoshi nan gidan kamar yadda ko kusa ba zata yarda su hadu gidansu ba
ajiyar zuciya ta saki
”babu damuwa,muna iya haduwa gobe kamar hudu na yamma a gidan zoo ko?”
”kin ko san a itin kwanakin nan cika yake,anya zamuyi magana anutse kuwa?”
”eh nafison gurin jama’a din ai,kuma akwai bangaren da zamu iya zama da babu cikowar”
”shikenan babu damuwa na gode,amma baki tambayeni,mai yasa nake da buqatar mu hadun ba”
murmushin ta kuma yi
”a tun sani na da kai da alkhairi,na sanka,don haka yanzu bazan canza in maka zaton sharri ba,kaga kenan ina tsammatar jin alkhairi ne daga bakinka”sosai yaji dadin irin shaidar da tayi masa,har yau bai fasa yaba kyawawan halayen maryamu ba,kowa tana masa kallon mutumin krki ne kamarta,hakanan tana kowa kallin mai kyakkyawar zuciya kamar yadda ita din take
????????????????????????
Qarfe hudu suka fita daga gidan zuwa gidan zoo din ita da hindatu,dukkaninsu cikin kwalliyar atamfa suke riga da skert,sunyi kyau kam masha Allah
a can suka taddashi har yana zolayarsu sai yaci tararsu sun mishi african time,yayi kyau abinshi cikin dinkin kufta ya dswo jabir dinshi na ainihi,kyakkyawan matashin saurayin nan mai yawan ado da fara’a jabiru
gurine kebantacce dake can cikin ainihin gidan ajiyar namun dajin na garin kano,tamkar lambune ska yishi na musamman kudin shigarshi ma daban yske kusan ba kowa ne ma yasan da gurin ba,kujera ce irin ta siminti suka zauna a dayan shima ya zauna a dayan,sabuwar gaisuwa suka sake,maryam ta dubi jindatu tace dan bamu guri kadan to tace kana ta miqe,jabir din yace
”ai da kin qyaleta ma don maganan ya shafeta”ta yi gaba amma ta jiyo abinda yace din sai gabanta ya fadi hakanan
”maryam,haqiqanin gaskiya na yaba da kyakkyawar tarbiyyar da kuka samu,sannan nayi baqinciki qwarai da gaske da rasa ki da nayi duk da nasan cewa komai qaddara ce daga ubangiji,saidai ina kwadayin hada iri da ku maryam,ina neman wata alfarma guda daya,Allah yasa wannan karon bazanyi failing ba”
cikin tattara dukkan hankalinta a kanshi tace
”babu wata alfarma da bazan iya maka ba indai ina da iko kima bata keta haddin shari’a”
”be keta ba maryam”ya fada yana murmushi wanda ya qara masa kyau da kamala
”so nake ku bani hindatu”
idanu ta zazzaro tamkar taga wani abun tsoro idanunta kan jabir din
”jabir……..shin ka manta alaqar dake tsakanin hindtu da jamila ne?,ya da qanwa ne fa?”
”koda na taba sanin jamila a matsayin diya mace hindatu bata haramta gareni ba tunda igiyar saki ta raba tsakaninmu balle babu abinda ya taba shiga tsakanina da ita na auratayya,yadda aka kaimin ita haka na dawo musu da ita,so kika babu maganar janamin auren hindatu kenan”