ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

mama kam rasa mai zata fada tayi,babu shakka duk yadda kaga Allah yayi da rayuwarka baiyi don zalunci a gareka ba,yayi ne saboda shi ne mafi sani ga abinda ya dace ga bawansa
raliya har da hawayen farinciki
”damuwarki tazo qarshe diyana,Allah ya yanke miki,maqiya kuma sai su kashe kansu don baqinciki”abinda ta dinga fadi kenan fuskarta qunshe da murmushi
hindatu kam buri ya cika,don tace ko iya haka Allah ya barsu sun gode masa,Allah ya nuna isa da buwayarshi,itama tata visa din umarar na nan jabir ya tanadar mata bayan sun angwance da wata daya

????????????????????????

qarfe biyu na azahar jirgin ethopian airline zai debe su zuwa ethopia inda anan zasu fara yada zango kafin su isa qasar sin,cikin masu rakiyar tasu harda jabir da hindatunshi,abdulrahim sai zubaida,raliya da yaronta fadil,

ranan ne abdulrahim suka fara haduwa da jabir,tuni ya dade da sanin waye jabir din da kuma matsayin da yake kai a yanzu a gun maryam din,don haka gaisuwar mutunci sukayi tamkar sun jima da sanin juna,kusan dukkansu sama sama suka gaisa da abdallah yaja gefe yana faman cin magani tamkar wanda aka yiwa dolen tafiyar,ita kuwa zubaidan bata damu da ta qyaleshi ba ganin yadda yake faman fuskewa ba tana liqe da shi tana zuba rawar kai yayin da shi kuma yayi mata dif ko kanzil yaqi tanka mata da ita cikin hirarta
cike da bege da qaunar juna suka yi sallama lokacin da aka soma neman matafiyan

maryam ce qarshe saboda tsayawan da sukayi da abdulrahim
”abun mamaki banga irin sallmar nan da masoua kanyi ba yayin rabuwa da juna abdulrahim meke faruwa?”
murmushi ya saki yace
”me kika gani maryam?,kina tuhumata ne kan rashin damuwa da tafiyar da zakigi ki barni?”
”dole in tuhumeka mana abdulrahim,ba sau daya ba basau biyu nasha kamaka da laifin qin sakin jikinka idan muna tare matuqar abdallah na agun,wai shin tsoronshi kake ne ko meye?,aure fa zamuyi nan da sati uku kowa yasan da zamanka,ko wata barazana yake maka aboue wadda mu bamu san da ita ba”
sai taga ya tuntsire da dariyar har yana dan duqawa
”babu tsoro balle barazana tsakanina da shi,ke kika dai fuskanci hakan,hasalima abinda kike zaton ba haka bane,Allah shine mafi sani ga abinda yake cikin zukatan bayinshi,Allah ya kaimun ke lpy ya dawo min da me lpy,ki kula min da kanki matuqa,ki yiwa kanki addu’a mai yawa maryam,kada ki kashe wayarki da wuri zan kiraki kafin ku tashi”sallamar da sukayi kenan

koda ta shiga gurin tayi tsammanin ya dade da wucewa tunda sun rigata shigowa da wajen minti goma sha biyar,sai gashi tana gaba gun screening shi kuma yana tsaye a bayanta,gaba daya sai ta takura,tana ji a jikinta tamkar yana qare mata kallo ne kawai,gashi doguwar riga ta saka sai rolling da tayi wanda iyakacinsa kafada,hill shoes ta saka wanda sanadiyyar hakan yasa ta kusa kama abdallan a tsawon

ko cikin jirgi ma number din sit din nasu daga shi sai ita,mami na a sit din bayansu,tamkar ta zura a guje ta bar sit din haka ta dinga ji,tunda take basu taba zaman kusanci na tsawon lokacin da zasuyi yanzu ba,ta njtsu tsaf tamkar ace ket!ta zura aguje
wayarta tayi tsuwwa ta duba saiga kiran abdur rahim,tamkar ance mata ta kalli gefanshi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wani irin kallo yake mata da ta kasa fassara ma’anarsa,shi ba harara ba ba kuma normal kallo ba,ya kafeta da mayun idanunshi masu cike da kwarjini,sai ta tainci kanta da kasa dagawa har wayar ta tsinke,gani tayi ya ciro tashi wayar ya fara danne danne hakan ne yasa tayi saurin jan tata wayar ta soma dubutawa abdulrahim din saqon karta kwana kan bazata iya amsa waya ba a yanzun cikin yi masa sallama da bankwana,saida kamfanin layin sadarwa suka tabbatar mata da yake sanna ta sauke idanunta daga kan wayar,ta sauke siririyar ajiyar zuciya daidai kokacin da taji shi kuma anasan bangaren yaja tsaki qasa qasa ya furta
”fool”
dayar wayarshi data fara ringin taga ya janyo ya zura earpiece
”hello baby……muna jirgi yanzu zamu tashi…..ok…ok bye take care,i will missed you too”ya kashe wayar gaba daya ya ajjiyeta guri daya

”janye cat eyes dinkin nan daga kaina,yanzun zansa a canza miki gurin zama indai kika ci gaba kallona,bansin kallo kin gane?”
ji tayi kanar ta hukunta idon nata da har yayi kuskuren kallonshi
”me zan kalla wanda babu shi jikin abdul dina?”ta fada cikin dakiya kamar ma bada shi take ba,kanta na kallon wani sashin
”there ar many,ko skin dina kawai batayi kama data baqin mijinki ba mai zubin ta ‘yan garuwa,after all ma kinsan da hakan kike qarewa mijin wata kallo,kinsan kina so tun farko bakiyi magana a taimakeki ko a qwarqwara kixo,yanzun kam its too late qwalelanki”

maganan ta mata baqi da yawa,tayi qoqarin control din bacin ranta don ta samu maida masa amsa yadda ya kamata
”shi dan garuwan ai Allah ne ya halicceshi……”
”eh mana,da ke kika halicceshi”ya katsi numfashinta ba tare data idar ba
da sauri ta dora don kada yaci da rabonta ba tare data samu ta rama ba
”ba kyau ko kudi nakeso ba mutunci nake bida da daraja,kai din kuma ai inama kallon mace ne ‘yar uwata kaga babu yadda za’ayi ince inason jinsina,abdul dina yafimin kowanne namiji cikin jinsin maza,ko a mai min shara bazan iya daukarka ba da dai mai wankin toile……”

”qarya kike wlh ya fada cikin fushi da dan daga sautinshi,ita kanta ta dan tsorata don qasa qasa suke maganar lokaci daya ya daga muryarshi,idanunshi data kalla kawai suka sake sata a zulumi,sai a lokacin ta tuna waye fa,abdallah ne,ta runtse ido tana jin zafin matsar da ya yiwa yatsunta kamar zai karya su ya kuma qi saki
”meye ne abdallah”mami ta fada tana dan leqo da kanta
”babu komai”yace
”ko baka jin dadi ne?”
mami ta tambayeshi cikin yar damuwa jin sautin muryarshi ya canza lokaci guda
”am fyn”ya fada a taqaice
”ok,to ku kashe wayoyinku”tace mishi bayan ta koma ta zauna daidai ksn sit dinta

sai da ya fara hucewa da kanshi sannan ya sakar mata hannu,zuwa lokacin tuni ta fara share qwalla don azaba,jin hannun take kamar ba’a jikinta ba sanadiyyar taruwar jinin da taji ya mata,tuni har jirgin ya daidata a sama,da qyar ta janye hannun tana yarfar da shi tare da fatan jin ya sake daga daurewa da zugin da yaje mata,ko da aka tamvayesu abinda zasu ci cikin jirgin kasa ma mafa na tayi,tanaji yasa aka kawo baqin coffe aka ajjiye musu,itakam ko kallo ma bai isheta ba

a hankali suke sauka daga jirgin daya bayan daya,gaba daya qafafunta sun mata tsami ga hannunta na damunta,itace a gaba abdallah a bayanta mami a bayanshi,rashin qwarin jiki ya sanya qafarta hardewa ta tafi luu zara gangara daga matattakalar
a tsorace mami tace
”subhanallahi,abdallah tarota”
tuni ya tallafota ta dawo jikinsa
”kin zame mana kaya wallahi,dama so kike a rungumeki din an miki hankalinki ya kwanta,amma net tine kika qara sai nayi maganinki”ya fadi yana tureta daga jikinsa
”sannu” mami ke ta mata har suka sauka,duk da yanayin rashin dadin jikinta baihanata ganin qawatuwar garin ba

gida ne mai hawa ashirin cikin unguwar,gini ne qawatacce mai kyawu matuqa da gaske,cikin hawa na takwas nasu gidan yake,gida ne mallakinsu abdallan da suka siya da kudinsu,da fari falone madaidaici sai corridor daga damanka wanda idan ka shiga zaka tadda kitchen wani corridor dinne yake kallan kitchen din shi kuma dakunan bacci ne guda uku kowanne dactoilet cikinsa,sai valcony ‘yar qarana mai kyau daga fuskar kowanne hawa na gidan wanda ta nan kana iya gano ainihin cikin unguwar da layinku da kuke an qawatashi da kyawawan kujeru guda hudu da yan shuke shuke

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button