ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

daki daidai kowa ya dauka,tunda ta shiga dakin tayi wanka tayi akwala tayi sallah ta nade a gado sai bacci,tun la’asar dinsu sai da aka kusa idar da sallar magariba sannan mami ta tadata tayi sallah,tuni sunyi order din abinci an kawo musu har gida don haka shi kowa yaci,ba damar girki an dai siyo dan abinda zasu buqata kafin su gama kwanakinsu kamar ruwan roba qwai suger da sauran abinda zasu iya buqata,tana shirin basu guri don taji sun fara lissafe lissafen siyayyarsu mami ta tsaidata.
”maryam gaya min dame dame kike so,don gobe insha Allahu zamu fita bana son mu wuce kwana hudu,muje muyi kwana goma ko sha biyu a makka mu wuce gida lokaci na qurewa”
a kunyace tace
”bani da zabi mami,duk abinda kika zabarmin yayi”
bata ce mata komai ba ta miqa mata takarda da biro tace taje tayi mata list din duka abinda takeso nan da goma ko sha daya tazo ta kawo mata,hannu biyu tasa ta amsa ta koma daki

sai ta rasa ma me zata rubuta,bata da layin qasar balle ta kiraliya ko hindatu suyi shawara,wani tunani tayi ta koma falon,nan ta samesu yadda ta barsu,saidai wannna karo sunyi kace kace cikin takardu,rubutu kawai kowannansu ya duqufa yana yi
”hmmm,gaskiya ne,ai dole ayi bikin da babu kamarsa,da daya tilo”maryam tace cikin zuciyarta
”ya akayi maryama,har kin gama?”mami ta tambayeta bayan ta dago kanta ta maida kan rubutun da takeyi
”ummm…mami cewa nayi don Allah ko zaki aramin wayarki in dan kira gida?”
”ayya nima kuwa bani da layin qasar nan duk sanda muka zo sabo nake siya wancan faduwa yake,sai gobe idan Allah ya kaimu zan siyi wani”

har ta juya zata koma dakin mamin ta sake kiranta
”maryama zo….abdallah naga kai har ka hada naka layin ara mata tayi wayan”
yayi wani kicin kicin da rai ya saci idon mamin ya harareta kana ya ciro wayar daga aljihun trouser dinashi ya miqo mata
ta miqo hannu zata karba
”idan kinsan wannna baqin basamuden zaki kira da wayata ma gwara kiyi tafiyarki ki barmun abata,don wlh kika sake kika cinyemin credit sai na zara asalary dinki,don shi na fuskanci baya da arziqin da zai iya biya na”ya fada qasa qasa yana kallon paper din hannunshi da yayi rubutu,sai ka rantse ba da ita yake ba,murguda mishi baki tayi bayan itama ta harareshi kana ta karba duk da cewa bai ganinta,shi baisan yadda ta tsaneshi bane,idan banda lalra babu abinda zai hadata da wayarshi ma.

Ta loda numbers din raliyan ta kirata,sosai taji dadin shawarar data samu na abinda ya dace ta siya dim,ta kira hindatu ta zabi abinda itama takeso sai ta rage nata ta hada da na hindatun,kasa jurewa tayi don haka ta saka numbers din abdulrahim ta kirashi,sun taba hira sanna ta kashe,tana shirin ajjiyewa wani kiran ya shigo
my suger ta gani a rubuce,ta zubawa numbers din ido tana kallo,sai ta tabe baki sanna tayi rejecting.

ci gaba akayi da kira ita kam bazqta taahi ba sai ta gama rubuta duka abinda zata rubuta din ta fita gaba daya,kiran yaci gaba da shigowa ba qaqqautawa,tsaki ta ja ta janyo wayar ta daga kana ta kara akunnenta
”kada a cika mana kunne mai wayar bayi kusa”dum akayi kana taji ance
”ok”can qasa qasa

wayarta mata kyau ta dan juyata a hannunta,garin cire lock ta taba gurin pictures,daya bayan daya ta dinga bin folders din tana kalla,abinda ya daure mata kai ganin hounan abdallah da yammata kala kala,tana kalla tana tabe baki,wannnan guy din dan garari ne,waishin ma a ina yake haduwa da yammata haka zuqa zuqa yadda yake nuna he was always busy,ta shafe aqalla awa guda har taso shagala,duka hotunan babu na yarwa ya iya wanka kam babu ja a wannna tana iya bashi maki hundred parcent cif

larm din da agogon dakin yayi na qarfe goman dare ya tunasar da ita,garin sauro ta manta bata sauka daga folder din pics din ba ta kashi takardar ta fita falon,shi kadaine yanzun sai gun da mamin ta zauna,da alama yanzu ta tashi kuma ba dadewa zata yi ba,jin fitowarta bai sanyaahi daga kanshi ba,wayar ta miqa masa kana cikin cool voice dinta tace
”na gode”ya amshi wayar baiko dubeta ba,sai da ya bude screen din yaga inda ta shiga sanna yace
”awa ukun da kika kwashe wayar na gurinki hoton mitum daya dama kika tsaya kalla?”ya tambayeta idonsa cikin nata

ta dan zaro ido tana duban wayar,sai lokacin takula hotonshi ne a kai,yayi kyau cikin shigar suit yana murmushi,da alama ba’a qasar aka dauki hoton ba,bata kai ga cewa komai ba mami ta shigo falon
”kin gama maryamu”
”eh mami”ta fada tana miqa mata takardar,ta karba tana dubawa kuma tana qoqarin zama kan kujerar
”an gaisheki maryam,duk tsawon awoyin man iya ka kadai wadan nan abubuwan kika rubuta?,sunyi kadan”tace tana sake qarewa takardar kallo tana girgiza kai”
kararki tayi yawa dama nasan ba iyawa zakiyi ba,jeki kawai,zanyi amfani da wannan din da kuma wadanda na rubuta”
tana murmushi ta juya ya shige dakin ta barsu nan suna ci gaba da lissafe lissafensu

????????????????????????

ta riga su tashi kamar yadda ta rigasu kwanciya su sai yanzu suke nasu baccin gajiyar,kafin su farka harta kammala breakfast taci nata,sai tayi zaune a parlour tana kallo abinta cikin riga da wando na pakistan orange da baqi,ya mata kyau kuwa sosai

takun da taji shi ya ja hankallinta abdallah ne ke fitowa sanye da riga armless da wando three quater,fuskar an ahade kirtif ya qarasa gaban freezer ha ciro fresh milk da ta hada sanyi ya balle robar ya soma sha,baifi rabi ba ya ajiye saman freezer din ya nufi kitchen sai gashi da plate da cup,mamaki tayi yau da kanshi ya zuba baiko nemi ta zuba masa ba lallai da alamu tunwa ce ta koroshi ma,zaya zo yana wani ciccin magani kamar wanda wani ya zageshi

can gefe guda ya samu ya zauna kan ya fara break din,duk sai taji kamar ya cika falon,zaman ya daina mata dadi,neman dalilin da zaisa ta tabar falon kawai takeyi,don bata buqatar ko qanqani zama inuwa daya ya dinga hadata da shi ko naminti dayane idan ba lalura ba
”ke”taji yace sai tayi banza da shi kamar bata jishi ba,ta fuskanci wani jan bala’i gake nema da ita tunda suka taho,ita kuwa kodan daraja da kunyar mami bazata bari su raba abun fada ba

”bakiji kashein da na miki jiya ba kenan sai da kika kira wani da phone dina ko,to ki gayawa rubabben saurayinkin kada ya kuma kiran numberta don ba sa’anshi bane ni”ya miqe yana dauke cup din tea tare da bari plate din a gun,bai kai ga shiga corridor din ba sukayi kacibus da mami tana fitowa da hijabi jikinta qafarta sanye da silifas
”mami ina zaki?”
”zan sauka ne floor na qasa mu gaisa da maman farida,jiya kaga ban samu na ahiga ba saboda gajiya”
”pls mami ki taimakeni kada ki cewa zeenah tare muke,wallahi kika bari ta sani tofa na banu kafin mubar qasar nan nacinta sai yasa na rame,ango kuma da rama ami ai babu kanta kada ta koro miki ni tace na mata rama da yawa”
dariya ma ya bata gani irin marairaicewar da yayi
”ka maida ni kakarka Allah abdallah,kakannin naka ma ka shafa musu lpy a kaina abun yake qarewa,ni dai Allah ya kusa rabani da alaqaqai gwara kayi auren ko kunnuwa da idanuna zasu huta da ganin yammata,ka shirya kafin na dawo mu fita da wuri so nake a yau a gama siyayyar baki daya”

tayi gaba suka gaisa da maryam ta fita,tayi zaton ya shige dakinsa tana zuwa sukayi kacibus bakib qofa,tana mura handle din dakin da qoqarin shigewa ciki taji yace
”kika sake mami ta miki tayin fita kika ce zaki bimu wata siyayya sai na qarasa targaden da na miki jiya”wuf ta shig dakin ta saka maqulli tadan daga murya
”to baaba na” sanna taja tsaki,gado ta fada cikin jin haushinsa,dama ita bata sha’awar zuwan ma sam,dadai ba da si din zasu je ba shine,amma indai da shine zamanta a gida ya fiye mata dadi,qofar ya tsaya yana kallo,dan qaramin murmushi irin na gefan baki ya subuce masa ya cije lebansa na qasa kadan kana ya tura qofar nashi dakin ya shige ya cire kayan jikinshi ya fada wanka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button