ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”idan da ni mai wadata ne meramu ai nine mai baki ma a matsayin gudun mawa,ke yarinya ce ta gari merama,babu komai tsakaninmu dake saidai muyi miki sai fatan alkhairi”
sai ya kuma karya maya zuciya
”indai ka daukeni ‘ya baaba ka karbi kudin nan,ayi min addu’a”da qyar ta shawo kansa ya karba yana sa mata albarka,sukayi bankwana ta shige gidan ta juya don shiga gidan,tun daga qofar gidan ta fara ganin canji,yasha fenti radau ruwan madara tun daga waje har cikin gidan

mutanene da suka kusa dosan ashirin a tsakar gidan,hira ce kawai ke tashi cike da farinciki,dangin mamanta ne da na babanta na nesa,na garin gaya da sauran garuruwa,sallamarta ya sanya su saka guda atare kowa na fadin albarkacin bakinsa ganin yadda tayi kyau ta canza tamkar ba maryam din ba ,kunya ta kamata ta qarasa gurinsu suka gaggaisa,maryam mai alkahiri,ce duk da yanayin gidansun hakan bai hanata idan ta dauki albashinta ta duba mabuqata sosai cikin dangin nasu ta taimaka musu da dan abinda ba’a rasa ba iya abinda zata iya

daga nan dakin mamanta ta wuce,nan din ma da mutane dakin yayi kaca kaca da kayyaki samiru da kayan robobi wadana aketa kwashewa za’a tafi jere,suka gagggaisa ta shige dakin gadon mama,ita da hindatu ne a dakin kayan sawa ne zube saman gadon sunata aiki,gefan gadon ta samu ta zauna ta soma gaida maman,dafe bakinta hindatu tayi
”la la la adda maryam,tabdijan irin wannan canzawa haka gaskiya mami ta iya kiwo,za’a gigita ya abdur rahim kenan”alamu tayi mata da ido tayi shiru don Allah

”qaraso maryamu ki fidda kayan da kike so za’a bada na bayarwa”
”um um mama kawai a bawa wadanda za’a bawa dim babu komai”hindatu ta janyo jakar bakko gaban maryam din tana fadin
”duba kayan nan adda maryam dinkunanki ne jiya adda raliya aiko idris direba ya kawosu gobe zata amso miki sauran”
da daidaya ta dinga daga kayan,ba qaramin burgeta dinkunan sukayi ba duk ciki babu na kushewa
”Allah ya saka mata da alkhairi”ta fada bayan ta kammala dubawar

A bakin fanfo ta fito yin sallar la’asar ta tadda jamila ta fito ita kuma daga bandaki,gaba dqya ta fige ta lalace kamar mai cutar qanjamau,wani banzan kallo ta yiwa maryam din tare da jan tsaki,bata kulata ba ta bude fanfon ta kunnashi ta fara alwala,bata kai ga gamawa ba taji an bangajeta tayi taga taga kamar zata fadi sauran qiris ta qume goshinta Allah ya taqaita mata ta dafe kan fanfon,miqewa tayi tana duban bayanta,binta ce a tsaye cike da tsabar rashin kunay tana girgiza,ta arkade jikinta da ya debi qura kana ta kalleta
”baki gani ne binta kika bugeni?”
”ina gani mana sai me?,dama jiran dawowarki nake cikin gidan nan,tsofaffin munafukai maciya amana masu aure mijin yar uwarsu”
duk da kalamanta sun mata ciwo amma sai da ta bata dariya,tsayawa tayi kallonta kawai,cikin yaran gidan susu goma sha bakwai binta ita ce qanwarta ta tara,aqalla ta bata ahekaru kusan goma,sai taga ada ma ba ni ta kanta take ba sai ayanzu,ranar tqrihi a rayuwarsu,kada kai tayi tana sake yin murmushi ta juya don ci gaba da alwalarta kafin tace
”duk wadanda kika kira da wadan nan sunayen ai aun riga da sunsan kansu,kinga kenan bada ni kike ba”
”dake nake mana,kuma idan kin isa ki tanka kiga yadda ake ruwan bala’i cikin gidan nan”
ta zubar da ruwan dake bakinta ta gyara daurin dankwalinta kana ta dafa kafadar bintan
”mai abun fada baya fada,harkar girma muke da mutunci bata bala’i da masifa,ina da damar da zan miki dukan tsiya binta hakan ba gagarata zaiyi ba,amma bazanyi hakan ba abinda kuka shuka kuke girba ma kadai ya isheku duka mai taba qololuwar zuciya”ta sake mata kafada tayi dakinsu

”ki dakeni mana kinji ko karuwa kawai”
”ke kuwa tunda bata kulaki ba ai sai ki shafa mata lafiya”inji kulu dake diban ruwan wanka
”babu ruwanki munafukai,dama tun jiya naga kunatavrawar kai ke da uwarki a kansu”kulu ba haquri kamar yadda bintan keji da kanga,take suka hau dambatawa,ragowar dangin babansu da basu je jere ba ne suka rabasu

Dawowar yan jere suka hau hirar gidanjan su maryam din yadda Allah ya musu baiwar samun mazauni mai kyau da qayatarwa ta,maganar ta qara hasala hadiza da yaranta wadanda suka zame mata qawaye,suke kuma tayata haukan da take ta faman yi,don tuni jikin huwaila yayi sanyi,saidai atafau hindatu ta hanata shiga jikinsu,tace sam baza’a maimaita abinda ya faru shekarar bara ba,an dai fidda kayan sawa jakanku na da takalma cikin kayan maryam din an bawa yaranta kuku lubabatu da batulu,da murnarsu kuwa suka arba koba komai sun samu na fitar biki,wannan karbar ma da sukayi saida ya zama bala’i,hadiza da yayanta suka fito suna zubda ruwan rashin mutunci cikin dangin ubansu,hali kam sun saidashi,wanda baisan halisu ma ba ada ayanzun ya sani,kowa ya budi baki tir yake da halayensu

????????????????????????

Tara ga wata ya kama ranar talata ranar sukayi kamu,washegari laraba sukayi budan kai duk shigar da sukayi iri daya ne komai da komai ita da hindatu hatta da yari,alhamis aka musu wani wani dan reception na fulani wanda shiga ce ta fulani kowa da kowa yayi,ba qaramin qayatarwa tsarin nasu yayi ba,komai a tsare cikin nutsuwa da kwanciyar hankali

Ranar juma’a ya kama daurin aure,a gaya aka tsara za’a daura auren wannan karon,dalili da yasa kenan gidan ya zamto sai mata kawai mazan duka sun tafi gaya

Da yammacin gidan maman zahra suke zaune maqotansu,tana tsakiyar qawaye da ‘yan uwa,tayi kyau cikin shadda ‘yar ubansu lemon green da akayiwa adon light blue,rigace da zani dinkin ba qaramin mata kyau yayi ba,tamkar wata fure haka ta koma,raliya na gefanta tana zuba mata abinci cikin plate kana ta miqa mata
”maryam,karbi kici,tunda aka fara sabgogin nan baki ci abincin kirki ba fa”
ya mutsa fuska
”banajin dadin bakina raliya,faduwar gaba nake fama da ita tun da safe”
murmushi tayi
”fargabar shiga sabuwar rayuwa ce,kowacce mace najin hakan har da bacin rai ranar daurin aurenta,wasu ma har kuka suke kafin suji sanyi cikin zuciyarau,kiyita ambaton Allah”

kafin tace komai waurta ta fara kuwwa,a kasalance ta ciro mami ke kiranta,mirmushi tayi sanan tace
”Allah sarki mami na”
”tun da safe naso kiranki maryam,nasan tuni an daura tun safe ko diyata girma ya hau kanta an zama manya”murmushi ta sake yi tace
”na yamma ne mami,suna can dai”
”to Allah yasa ayi a sa’a a gaida maman kice ina mata Allah ya sanya alkhairi”
”ameen mami,na gode”

batulu tayi sallama falon sanye da daya daga cikin kayan da maryam ta bata an gyara mata daidai ita,sun mata kyau kuwa don duka yaran gidan nasu babu laifi akwai kyau irin na fulanin usuli
”adda maryam kizo kinyi baqi suna falon mama”cike da mamaki ta kalleta,gau ta zama adda,sunan da koda wasa bata taba jin wani daga cikin uaran gidan ya kirata da shi ba idan ka dauke hindatu,hatta da isyaku autan gidan
”kice ina zuwa”ta bata amsa tana janyo mayafonta ta lullube jikinta,ta dubi suwaiba dake zaune gefe tace tazo ta rakata
da qyar ta samu ta kutsa ta ahiga gidan nasu saboda yawan jama’a musamman da masu kidan qwarya suka baje hajarsu cikin qwarewa don daga cikin gidan sarki aka daukosu

qannenta shamsiyya,azara,balaraba da yasira na zaune daga gu guda an samu abinci suda yaransu anata kwasa,sannu tayi,musu kafin ta shigesu,yasira da shamsiyya suka danyi qus qus kana suka tabe baki
”an samu duniya”inji azara
tayi sallama falon,maman ma zaune tayi kyau cikin dinkin atamfarya,sai ta koma kamar yarinya mai qananan shekaru,Allah ne kadai yasan farincikin da take ciki,babu shakka komai yayi farko zaiyi qarshe,aure kuwa lokaci ne idan yazo ko ba’a shirya ba sai anyi shi,fata dai kada gaggawar anason ayi auren tasa aje ayi zaben tumun dare
abokan aikinta na na gurin haj atika,taji dadin zuwansu kuwa qwarai da gaske

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button