ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????

????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

     ▶3⃣8⃣

JIRGINSO ZAYA TASHI KE DAI AKE JIRA …’YAR GATA DUNIYAR SO…. KECE DA SARAUTA????????

na dawo gunki nazo baqo da sallama….kai kawo nayi qarshe…a qauna na tsunduma….kin jawo nayi roqo nazo ki ban zuma….na sawo dubi tufata mai kyau da karrama….ke naiwa kwalliyata shiga ta alfarma…..????????
soyayya gaskiya ce ya zanyi in raina….wanda yake aac cikintaaa nima don na zauna…….nayi dare ban masauki gidanki in kwana….zo ka shige har abinci zan maka kwadon rama…..????????

riqe sirri sai mai sirriiii….da fari a cikin taurariiiiii….

wannan waqar na sadaukarwa da readers don jin dadinsu kana iya sauraronta bayan kammala karanta wagga shafi
????????????????

Matsowa kusa da ita ya sakeyi tattausan murmu kwance bisa kyakkyawan fuskarshi,duka hannayenshi ya ware da nufin ta iso gareshi,take jikinta ya soma bari,qwaqwalwarta so take ta tsaya cik da aiki saidai ta ware qwanjinta wajen hana hakan faruwa,bata da buqatar tsayawar tunaninta a yanzu,tama fi buqatarshi fiye da ko yaushe,ya sake matsowa gareta yana nufin janyo ta jikinshi

wata hadaddiyar tsawa ta sakar masa bayan ta dira daga kan gadon jikinta na qyarma,tuni zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa fuskarta,dukkan tunaninta sun gama vata fyade abdallah yazo yi mata,tunda ba wannan ne karo na farko data taba ganinshi kebe da diya mace ba,amma wanne irin tsoro abdur rahim kewa abdallah da ua bashi irin wannan damar?,ko wani abu yayiwa abdur rahim din nsta har ya kai ga shigowa dakinta shi daya ba tare da wani qwaqqwaran motsi ko hayaniya ba.

Abdallan ya sake motsawa don biyota qasan,cikin daga sauti hargagi fushi bacin rai da tashin hankali ta dakatar da shi
”dakata marar tsoron Allah,me kake nema da ni?,me ya shigo da kai dakina?,kana shirin tozarta sunnar ma’aiki?,kana shirin cin mutuncin matar da bata yi maka komai ba?,to Allah ya fika”
jikinta na rawa ra fara daddan na wayar dake hannuna tun dazun da aka kawota lubabatu ta danqa mata a hannunta

Numbers din abdur rahim ne guda uku,saidai duka wadda ta kira sai taji ringin dinta cikin aljihun abdallah,cike da wani tsoron ta dago ta dubeshi,hawaye ne kawai ke kwaranya da sintiri kan fuskarta
”abdallah!,ina abdur rahim?,me kayi mishi?me ka yiwa mijina!?”ta qarasa maganar cikin qaaraaji

baisan sanda yayi alkafura ya diro daga gadon ba,gadan gadan ya nufeta don ya riqeta ganin yadda take kuka tuquru tana dafe bango,saidai kafin ya kai ga riqeta ta goce
”kada ka tabani,kaji tsoron Alkah kasan cewa ni matar wani ce”cikin cool voice dinsa mai cike da jarumta da mazantaka wadda a yau rauni ya cikata ya saje maidata sassanya yace
”pls cool down mana,ki natsu in miki bayani kinji,ki saurareni”

”bazan nutsu ba,in nutsu ka cucu ne,me kake nufi abdallah,me nayi maka,ka shigo dakin aure na,banga mijina ba,na kira wayoyinshi suna jikinka,ka gaya min me ka masa!!me kayi masa!!!”
duk yadda yaso tayi shiru ta saurareshi abun ya faskara,idanunta sun rufe bisa dukkan zatonta ko abdallah ya kashe abdur rahim ne
”ki zauna ki fahimceni…”’
”bazan fahimceka ba…..ina mijina…..ina ka kaimin mijina abdu……..”

”maryam!ni ne nan mijinki,ni ne mijinki ba abdur rahim ba,ni abdallah da ni aka daura miki aure!”ya fada yana nuna kanshi shima cikin daga murya har jijiyar wuyanshi na tashi
sai kukan nata ya tsaya cak,ta tsaya tana kallonshi tamkar doluwa ko sakarya,jin maganar tayi tamkar cikin mafarki,da saufi ta kama hanunta ta mintsina sai ta tabbatar cewa gaske ne,girgizq kantq ta shiga yi tana fadin
”ba kaine mijina ba,bakai ka aureni ba ni zaka yaudara?”

”bari in baki shaida don ki tabbatar”ciro wayarsa yayi ya kira wasu nimbers,ga mamakinta sai ga muryar abdur rahim radau
”kai,bakasan ganganci bane kiran ango daidai wannan lokacin ba?,ko baka shiga dakin marya bane?”yake tambaya cikin sigar zolaya
”hmmm,abdul maryam zata amince nine mijinta kuwa?”
dariya yayi
”a’ah,mai zai hana,idan ma taqi ta amince ka dauketa kuje gidansu tunda su sun sani kaine ka aureta din,ko ni inzo gobe sai in dauko gimbiya muzo in mata bayani”

baiga qarasowarta ba sai waftar wayar da tayi,cikin rawar jiki ta kara wayar a kunnenta
”abdur rahim,ka cemin kaine mijina ba abdallah ba,ka gaya masa don Allah”
”kiyi haquri maryam bani na bada sadakinki ba bani ke neman aurenki ba,duniya bani ta shaida a matsayin mijinki ba duka wannan abdallah ne,nine abdurrahim a fili a boye kuma abdallah,nike neman aurenki a gaban idonki a bayan idonki abdallah ne,banyi hakan ba don komai sai don DACE DA JUNA da kukayi ke da shi,babu wadda ta dace ta zauna da abdallah saike……”

bata bari kunnuwanta sun qarasa ji mata kalmomin da ta yiwa laqabi da munanan kalmomi ba ta saki wayar ta tarwatse agun,taji daga baki mai tushe to shin kuma wa take jira?me take jira da zai tabbatar mata fiye da abinda taji yanzun?babu,babu shi,take taji garkuwar jikinta na raguwa,qarfinta yana yin qasa,sai ta soma sulalewa agun

da gudu abdallah ya isa gareta ya tallafota,tabbas da tana da isashen qarfi bazata yarda ta sauka ajikinshi ba,rungumeta yayi yana jijjigata,numfashinta na fita hakanan idanunta akansa suke hawaye na bin gefan kunnenta saidai numfashin na gware ne gurin fita,rungumeta yayi tsam cikin jikinsa cikin wani tashin hankalin,daukarta yayi tsam tamkqr wata ‘yar tsana ya komar da ita kan gadon ya shimfideta.

mahaukacin bugu yaji ana yiwa qofar bangaren nasa ,sai ya sake diriricewa,cikin qanqanin lokaci kuma ya gayyatowa kansa dakiya da jarumta yana tafiya yana waiwayen maryam din tamkar wanda aka ce masa kafin yaje ya dawo zata bace ya sauko ziwa bakin qofar ya saka key din ya bude

jikinsa ta fado tamkar wadda aka hankado,cikin hanzari yasa hannunsa daya ya cireta daga jikinsa yayi gefe da ita saidai ita qoqarin dawowa take zuwa jikin nasa tana gunjin kuka duk ta wani burkice kamar mahaukaciya
”wai meye haka zubaidq!bana son hauka fa!”ya fada cikin hargagi
”bazan iya ba abdallah,wallahi bazan iya jure rashinka ba,ka tausaya min abdallah,ta yaya muna cikin gida daya zaka kwana da wata abdallah?”
ya tabbata idan yace ma zaya tsaya bata baki ne wahal da kansq kawai zaiyi don ba zata taba fahimtarsa ba,kai infact ma a yanzu bai da time baijin yana da time din wani a yanzu a duniya koma bayan maryam,ya tabbata idan yayi sake kwabarsa zatayi ruwa ne tsululu kuwa,a nashi zaton da hasashen abun bazai kai bacn haka ba,yayi zaton cewa duk randa maryam din ta samu labarin shine miji a gareta zatayi farin ciki ne fiye da kowa kodon,dimbin dukiya da Allah ya mallaka masa

ganin yadda take faman ahigewa jikinsa kamar hauka yasa yq cira hannu hankadata baya tayi taga taga kamar zata fadi
”ki shiga hqnkalinki zubaida,bana cike da iskanci da hauka kina jina ko,bace min da gani”
maimakon tayi kamar yadda yace din sai ta qara tasowa kansa,cikin zafin nama yaja qofqr ya rufe ya maida muqullin,ta kuwa fada jikin qofar ta saki wani kukan tana bubbugawa iya qarfinta
”ka bude min don Allah abdallah,wallahi na kasa barci,na kasa cin abinci,na gaza jurewa,ka bude min abdallah”haka ta dinga fada tqnq bubbuga qofar,yana jinta hqr ya haura sama ya barta anan
ruwan roba mai azabar sanyi yq ciro ya hado da cup ya koma dakin,yadda ya barya haka ua sameta sai qaruwa da ruwan hawayen fuskarta sukayi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button