ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ajjiye cup din yayi a side drower ya haura gadon,ya zame mayafin dake jikinta ya wulla shi gefe,ya janyo cup din ya tsiyaya ruwan yana tsoma hannunshi cikin ruwan yana shafa mata a fuskarta zuwa wuyanta,duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi kin laushi da santsin fatarta ba,duk lokacin da hannunshi ya taba fuskarta ji take tamkar yana dora mata wuta ne a jikinta,zuciyarta,cike fal da tsanarshi,sannu a hankali numfashinta ya soma daidaita,qwarin jikinta ya soma dawowa,da sauri tasa hannunta tayi wurgi da hannunshi dake ci gaba da shafa mata ruwan,ta miqe dqga kan gadon tana shirin sauka,da sauri ya tareta
”ina zaki maryam?”
”ina ruwanka da inda zani?,ka rabu da ni!”tayi maganar cikin tsawa,ganin da gasken fita zatayi yasa ya tareta ya riqe dukkan kafadunta,ta soma zile zille da qoqarin qwacewa tana fadin ya rabu da ita ya saketa,ci gaba yayi da qoqarin tsaidata

”ina buqatar hankalinki maryam,ina buqatar nutsuwarki,ki zauna ki bani dama muyi magana,ki nutsu ki fahimceni,me kike so ne maryam,me kike buqata”
sak ta sakeyi tama kallonshi
”sai yanzu kake da buqatar hankali na?,sai yanzu kake d buqatar nutsuwata?me kake son gaya min,ka aureni ba da sani na ba kuma kace nutsuwata kake buqata?wacce nutsuwa kake sa ran samu daga gareni?,haka ake aure?,ok saboda kana tsammani kana da dukiyar da zata iya kawo maka duk macen da kake so kamar yadda naji kana alfahari kana gayawa abokanka?,koda dukiya zata iya kawo maka kowacce mace da kake miradi yes na yarda zata iya amma banda ni maryamu aciki,koda ina da muradin dukiyarka ina cewa saida izini na zaka aure ni?,after all ma bana aonka abdallah bana qaunarka,bani da burin auren ire irenka ma,abu guda nake da buqata daga gareka shine ka rubuta min sakina guda uku a yanzu ka bani,ni kuma na maka alqawarin bazan kwana maka cikin gida ba,ka sakeni abdallah ka sakeni!”
ta qare maganar cikin hargowa

hannayensa ya harde aqirji yana kallonta,ba qaramin duka kalamanta sukayi masa ba,tunda ya tashi mace bata taba kallon qwayar idanunshi tace bata sonshi ba,akoda yaushe kalmomin so yake samu da karba daga garesu,kalmomin da bai taba samin suna da dataja ba sai yanzun akan maryamun,ya fuskanci ba qaramin fita tayi daga controll dinta ba,kome zaya fada bai da tasiri yanzun cikin kunne da ziciyarta don hakq ya dan jada baya,ya zame rigar jikinshi ya rage daga shi sai farar vest da dogon wandon shaddarsa,ya nufo inda take gadan gadan sai ta juya zata sa gudu caraf ya kamota,duk iya yada taso qwacewa abu ya faskara,qyaleta yayi taci gaba da qoqarin qwatar kan nata har jikinta yayi tubus qarfinta ya qare

”haka kurum zaki bata mana farin darenmu kan dalilin ki wanda kika qi tsayawa kiji nawa dalilin,dare ya tsala lokqcin da ya kamata mu samu hutu amma kin hana mana”ya fada yana mirginata tare da zuge mata zif din rigarta,ganin yana qoqarin cire mata rigar jikinta ya sanya ta sake sakin wani kukan cikin dausashshiyar muryarta da kuka ya dasheta tana ci gaba da qoqarin ture hannauenshi wanda saboda tsabar rashin qwarin jikinta ko motsi hannun nashi baiyi ba
”ka qyaleni abdallah,wallahi idan ka taba mutuncina zan maka Allah ya isa kuma bazan taba yafe maka ba”
duk da yana cikin rashin nutsuwa sai da ta bashi dariya
”kome zan miki ma ai nawa ne,dukkaninki halas dina ce,so ko kin min Allah ya isan ma ba bina zata yi ba”ya qarasa sabule rigar tata,hannayenta tasa ta fara kare qirjinta tana cewa
”ka zalunci rayuwata abdallah,zamu tsaya fa hisabi gaban Allah”
hannu daya yasa ya kawar da hannayen nata wanda ita iya ganinta duka qarfinta tasa gun kare su,ya balle bra din ya zameta daga jikinta,take numfashinsa ya dauke da sauri ya lumshe idanunsa kana ya squka agadon ya isa bakin wardove dinsu ya zabo rigar bacci mai adon fari da pink mai sulbi da taushi ,saidai kafin ya qaraso har ta isa bakin qofa cak ya sake daukota kamar wani kara ya maidota kan gadon ya danneta da rabin jikinsa ya sanya mata kayan baccin

fillow guda ya ajjiye musu bayan ya duba lokaci qarfe biyu da rabi na dare,cikin jikinsa ya jata ya matseta gam suka kwanta ba tare da ya damu da sauya nasa kayan ba,yana jinta tana wutsil wutsil dinta da dan ragowar qarfinta hade da hawaye don tuni muryarta ta gama dakushewa koda tayi maganar ma ba fita take ba,gashinta mai sulbi da taushi kawai yake shafawa yana jin digar hawayen nata tamkar na dalma kan tsokar zuciyarsa.

a hankali ya zagaya da kansa kan kunnenta ya rada mata
”kiyi haquri,na yarda na cutar da ke amma relax pls mu barwa gobe,kome kikeso zan maki,kiyi bacci zuciyarki tayi sanyi”
”ka sakeni bazqn kwana daki daya da kai ba bare jikinka,ka sakeni abdallah”abinda take ta fadi kenan saidai ina muryarta bata fita bare yaji abinda take fada,gaba daya ma taga ya maia abun kamar wani wasa saboda tsabar qarfin hali irin na abdallahn…….

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶3⃣9⃣

????????????????

alqawari ki riqeeee..komai wuya karmu rabu kinji…
m sharif song for dis page
????????

A hankali ta dinga bude idonta da taji ya mata nauyi sakamakon kumburar da sukayi,tana gama budesu tarwai komai ya dawo kanta,abu na farko hawaye ne ya fara bin idanunta kamar yadda ya ta kwanta da shi,jin alamun motsi daga qasa ya sanyata wurga idanunta can,abdallah ne zaune kan sallaya,ta dubi agogon dakin qarfe bakwai saura na safe,da sauri ta miqe cikin zuciuarta tana istigfarin rashin yin sallar asubahi akan kari,jiki babu qwari ta zuro qafafunta qasa motsin wannan ne ya juyo da hankalin abdallah kanta

sai ta kasa tashi don batasan ina toilet yake ba,da suka hada idanu kuma sai ta dauke kanta gefe guda
”ga toilet din can”ya fada yana kada yatsunsa tare da yi mata nuni,ta jishi sarai saidai ba zata oya tashi ba saboda rigar baccin jikinta gajeriya ce,gashi ta wuwwurga idanunta ko ina bata hango kayanta ba,zanin gadon ta yayaye kawai gaba daya duk da girmansa ta lullube jikinta da shi kana ta samu sukunin shigewa bandakin

kuka ta zauna yi riris kan daddumar,tana ji har cikin zuciyarta abdur rahim ya zalunce ta abdallah ya cuceta,don ko kadan bata da plan din airen abdallah akundin rayiwarta,sai gashi dare daya wata qatotiwar qaddara mai wuyar afassara ta fada mata,abdallah mai girmankai,mai izgili mai taqama da dukiyarsho,mai titiya da kyawun surar da Allah ya bashi,abdallah mai tarin ‘yammata,ko baya ga haka ma sama ai ta yiwa yaro nisa,ina zata kai abdallahn,batajin cikin yarin masoyansa ita din karanta ya kai tsaikon da zata daga hannu,me take da shi da zata nunawa duniya amatsayin matar abdallah abdulkarem mai nasara?,yaro dan gata gaba da baya da daya tilo tamkar taoka daya cikin miya,mai tarin kyau asali dukiya da arziqin ma baki daya,ta ina tarayyarsa da maryam diya ga malam amadu zatqyi daidai,masu nema da qyar suci da kansu da qyar,diyar da ta taso cikin qunci hantara da takurar rayuwa?,rufin asiri take nema da girma ba bankada da tonon sililin asirinta va,ta iya talaucinta haka zalika ta iya tsayawa iya matsayinta,to akan me yanzu zata yadda ta sarayar da dulka wadan nan abubuwa?,ko ta zuba ido abdallan ua sarayar mata da au lokaci guda

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button