ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

tasha ji daga bakunan wasu matan yadda auren mai dukiya quruciya da kyau yake zamewa mace qarfan qafa alaqaqai,don me zata zira kanta rijiya mai gaba dubu?bata taba sha’awar auren mai tarin dukiya irin abdallah ba,balle shi din da tasha jin kalmomin nuna ko ahi waye da matsayin da yake ji ua taka daga bakinsa,idanuwanta sunsha nuna mata kal kalan ‘yammata dake hauka akanshi,tana cikin wanna tunanin ta tsinci tafin hannunshi dafe da saman qafafunta,da sauri ta janyesu ba tare data daga kai ta dubeshi ba
”maryam”ya kirata asanyaye
”ko baki fada ba kuka kike”
”kuka na ya zama dole,auren dole qiriqiri?,irin auren dolen da ko a fina finai ban taba cin karo da ahi ba sai gashi yau ya faru a kaina?,ka fada min wanne mataki ka dauka game da zaman mu,zaman mu ba mai yiwu bane”
”ki bani dama mafyam ni zan mai da ahi mai yiwuwa,indai matsalar taki ta zuciya ce,zuciyarki bata san abdallah,ta bawa abdallah dama na kwana talatin cif na rantse miki sai taso abdallah fiye da yadda take son kanta”
”ka taba ganin inda ruwa da wuta suka cakudu suka zauna guri guda lafiya lau?”
ya fuskanci mai take nufi da maganarta don haka bata buqatar amsa
kusan mintina goma ahiru ya ratsa tsakaninsu,ta qagauta ya janye jiminahi daga inda take,ganin babu niuya tasa ta bude bakinta murya can qasa
”ka matsa daga kusa da mi,kuma ka cika min alqawarin da ka dauka min daren jiya yanzu ba sai anjima ba”
gayara zamanshi ya kuma tamkar ma basa ahi take maganarta ba
”naji,zan sakeki…..amma bisa wani sharadi guda”
tunda suka fara maganar bata dago ta kalleshi ba sai a yanzu
”ba buqatar wani sharado daga gareka ko wanne iei ne saki nake so,kuma dole ka sakeni”
ya sanya fitinannun qwayoyin idanunshi cikin nata kana ya tabe baki
”babu dole fa maryam,abdallah ne mijin ba wai maryam ba,idan kin amince zan gaya miki sharadina daya ne zuwa biyu da zarar kin cika sharadina ba tare da bata lokaci ba agobe ma kina iya tafiya da takardarki”idanunta ta lumshe saboda yadda ya nutsa qwayoyin idanunshi cikin nata yake mata magana haka kanshi tsaye kamar ba mai laifi ba
shiru tayi,cikin dan taqaitaccen nazari zuciyarta ta bata shawarar sauraranshi kanta kawai ta gyada masa,ya sake sanyaya murya tamkar mai jin bacci tare da sake matsowa kusa da ita,tayi yinqurin matsawa da sauri yace
”babu buqatar ki kuma matsawa baya,kin manta sirri zamuyi,ko kina nayita daga sauti na bayan jiya kinsa maqogarona nata zafi har yau?”tilas ta zauna a hakan qamshin turaren da tun jiya ya fesa shi amma har yanzu yana tashi a jikinshi
”tambayoyi ne zan miki su da farlo wadanda nake buqatar amsarsu daga yau zuwa gobe da safe kafin ki bar gidan nan,kada kiyi tsammanin samun takardar sakinki daga gareni matuqar kika gaza amsa min tambayoyina cikin gamsashshiyar amsa,na farko mai yasa kika damu da abdallah da yawa,kika gaza barinshi yaci guba da aka zuba cikin abincinshi har sau biyu?”da hanzari ta dago cikin mamaki da tsoro ta dubeshi,yaushe abdallah yasan da maganar gubar data hanashi ci?
gira ya daga mata yana mata killing smile dinshi
”hey,meye na tsorata haka,bayan tambayoyin basu qare ba,daya cikin wadanda zasu biyo baya fa”
sai ta duqar da kanta zuciyarta na dukan uku uku
”me yasa kika damu da sanin irin gubar da ake ahirin kasheni da ita sai da kika dangana da asibiti a washegari aka tabbatar miki da irin qarfi da illarta ga duk mutumin da yaci?,me yasa kika gaza barin gidansu abdallah duk da irin takura raini da abdalla ke miki?,me yake saki rudewa harda kuka duk lokacin da kika ganni kebe da wata cikin tsakiyar dare?suke nan tambayoyina”
gaza daurewa tayi a wannan karon ma sai data dago ta dubeshi cikin mamaki shin abdallah yasan akwai masu farautarsa ua qyale ya zuba musu ido?,tamkar yaji abinda take zantawa cikin zuciyarta yace
”kada kiyi tsammanin abdallah wawa ne bansana ana farauar rayiwanshi cikin gidan ubanshi ba,i know kuma zuwa gobe zaki ga abinda zaya faru,naki kawai answer din question dina…..gaba ta gaba,are you ready madam?”
kai ta sake gyada masa kamar qadangaruwa
”ok,mami is unaware game da wadda na aura,nayi haka ne saboda ina son inyi suorising dinta,ta bani komai a rayuwa bansan me zan bata ba,na sani baya ga ni kece ta biyu cikin diyoyin da take so,bata san diyarta na dawo mata da ita ba,na tabbata zatayi matuqar farinciki da mamaki da ganinki…saidai kinsan me?,farincikinta da mamakinta zai dore ne matuqar taji cewa auren so da qauna ne tsakaninmu,kinsan abun duba?duk wani motion da act namu zai zama irin na masoya a gabanta daga wunin yau zuwa goben tafiyarki babu musu tsakaninmu,yi nayi bari na bari wannan shine abubuwan da zasu sana miki takardar rabuwa da ni thats all”
gaba daya ji tayi ya daurera da duka jijiyoyin jikinta,wadan nan tsauraran sharuda har ina?,har gwara ya samu bulala ya bugeta yadda yakeso kana ya sallameta yafi nata sauqi,ina zata sami tulin amsoshin tambayoyinsa wadanda bata tab tunanin ma a kansu ba?me yake nufi yace da ita?,ama ture ta wannan baki daya,ya zata iya tanqwara zuciyarta ta nuna alamu na soyayya ga mutumin da babu so ko qwauar zarra tasa cikin zuciyarta…..
”idan kuma baki iya tsallake wadan nan abubuwa…..fine….sai ki shimfida ta barma da daura damarar zama da abdallah kiga idan bazai saceki gaba dayanki ma ba zuciyarki ba cikin kwanaki talatin kacal,hakan kuwa kinga bazaya miki dadi ba tunda kince wai baki sonshi bayan tsayin daka da kikayi wajen kare mishi ranshi da lafiyarshi don kina da buqatar ra……”
”naji….naji na amince”ta fada da sauri don katse soki burutsun da tace yana shirin yi mata
”good job,shikenan Allah ya bada sa’a”ya miqe daga inda yake,har yayi taku biyu ya kalleta still tana duqe
”kada ki manta da answer din tambayoyi na,don sune bqngare na farko na yarjejiniyar mu”
Sakaliyar la’asar ce data gama hada hadari wanda ya tilastawa garin lumshewa,sannu a hankali suke taku wanda idan ka gansu sai ka rantse shaqiqan masoya ne guda biyu hannayensu sarqafe cikin na juna,sanye suke da kaya kala daya saidai bambancin sunan yadikan,nata material ne na mata yayin da nashi ya kasance na maza,dukkansu sea green colour ne,abu daya zai saka duhu yadda fuskanshi ke qunshe da wani irin haske da annuri,yayin da nata fuskar ke duqunqune cunkushe da bacin rai duk da hakan bai hanata yin kyawu ba,maryam ne da abdalla kan hanyarsu ta zuwa gaida mami bayan ya tabbata da jama’ar gidan kowa ya koma inda ya fito
sunfi minti talatin cikin bangarensa yana nuna mata salon kallo magana da ladabin da yakeso tayi masa gaban mamin wanda hakan shi ya kusan janyo rikici
ya sake waiwaya ya dubeta suna gab da ahiga bangaren mamin kana ya dakatar da tafoyar tasu,tsatstsareta yayi da kallo,ta kauda kanta tana qoqarin sabule hannayenta dddaga cikin nashi
”malam bamuyi da kai zaka dinga min akallon mayi ba ko,idan kuwa kaci gaba daidai nake da na koma inda na foto na hada ya nawa ya nawa na koma inda nafi wayo”
”kya sha tsinuwar Allah data mala’iku,runda ko banza miji nake agareki koda qarshen duniya zaki gudu,nike ma da magana dake,kinfara karya wasu dokokin tun yanzu,wanda hakan na nufin tangal tangal da muradinki ne,haka koka ga fuskar amarya na kasancewa washegarin ranar da aka kanta,look at ur self don Allah,jiya kin kwana kuka idanunki sun koma kamar kumburarren qullin qosai,an samu da qyar sun daidaita kafin yamma,sanna kina son ki sake wargaza mana shiri,to wlh u hv to make sure idan kika bari mami ta dago wani abu babu ke ba samun takardar sallama”