ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

yanzun ma baqinciki ne ya hanata motsi da kuma umarnin maman,don tana zaune ne tana karatun waec da fitilar qwai a gabanta,sallamar ta kawai hindun ta amsa ta dora da cewa
”yanzu fisabilillahi yaya maryam haka zaki ci gaba da zama ana miki cin mutunci ba zaki kare kanki ba?”
”kinci gidanku nace hindatu,nace kinci gidanku,da baban nata zatayi sa’insa ko da matan ubanta?,ke maryamu,ina kika samo kayan jikinki?”
kai ita kam dai ta shiga uku,wato ko ina cikin tuhuma take
”mama tsarabar da raliya ta bani ce,na tayata aiki tace bazan taho ba sai nayi wanka,shine aciki na cire nasa wannan”
”madalla,amma daga yau kada ki sake ki sake kaiwa magariba a waje kina jina ko?”
”to mama”

dakinsu ta shige ta ajjiye jakarta saman katifarta,qoqari take ta shanye dukkan wani bacin rai,batason ta barshi yayi tasiri a ranta,tunda idan da sabo ai yaci ace ta saba,sau nawa ake ruwa qasa tana shanyewa,ta zare rolling din kanta ta dawo tsakar gida ta daura alwala,sai da tayi nafila raka’a biyu ta kaiwa Allah kukanta,ta dade saman carfet tana jan,hasbunallahu wa ni’imal wakeel sannu a hankali taki sauqi na zuwar ma zuciyarta

kira ne ya shigo wayarta data duba agogo sai ta tabbatar jabir ne don bata da alaqa da wani da zai kirata a irin wannan lokacin,shi dinne kuwa,awanni kusan biyu sukayi akan wayar har ta soma gajiya don bata saba doguwar hira irin haka waya ba,cikin awanni tayi amanna da kyawawan halayen jabir,bayan ta,jada da wanda raliya ta gaya mata,a yanzun mafita kawai take nema,koda wanda bai kai jabir din ba zata iya aurenshi matuqar zaya riqeta da daraja

sunayin sallama hindatu ta shigo dakin da tarin litattafanta ta watsasu tata katifar,kasancewar dakinsu daya don maryamu bata da sha’awar raba daki da ‘yar uwar tata,doguwar hamma ta ja,maryam ta dubeta tana dariya ”boko wahala”
”mtsw,ke dai bari yaya maryam,yanzu a haka kukayi degree?”
”me kayi da maza inji karya,idan banda abun hindu ke,da sai yanzu ma zaki bar secondry din”
”gaskiya ne kuma fa”ta fada tana fadawa kan katifar tabayan ta ture liattatafan da ta watsa gefe

”yauwaaa”maryayam ta gada tana janyo jakarta ta ciro kudin da jabir ya bata dazu
”ungo irga kiga nawa ne”
”an biya ku salary ne ya maryam?”tace lokacin tame lissafa kudin
”a’ah jabir ne ya bani”
”ya maryam Allah ya tsaida jabir din nan mu sha budiri”murmushi itadai kawai tayi
”ten thousand ne”
”ok…to ko riqesu,zan cika miki kudin rigistration din exam dinku”
”na gode ya maryam,na gode”
”don mind,ni dake duka daya ne,kawai ki tayani addu’a hindu”
”ai babu fashi wannan ya maryam”

????????????????????????

cikin sati,guda kacal sabo ya shiga tsakaninsu da jabir,yana da sauqin kai,fara’a da haba haba da jama’a,yan sonta ji da ita da tattalinta,cikar satin ta isar masa da saqon baban,murna da farinciki tamkar zai goya ta,washegari kuwa magabatansa suka iso,a take aka tsaida magana harda sa rana,farincikin mama bazai misaltu ba duk da tana boye wa,yayin da huwaila da hadiza sukejin kamar an musu transfer zuwa jahannama

????????????????????????

shiye shirye tuni suka fara kankama domin sati biyu kacal ya rage,cikin yammacin gab da sallar magariba jabir yazo gurinta kawo mata invitations kasancewar akan hanya yake yasa bai shiga daga cikin gidan ba,suna tsaye jikin motarsa taga kamar an wulgasu,ta dago kanta don ganin me wucewar,maraqisiyya ce har ta gota su taga ta dawo,da baya,qare musu kallo tayi sannan ta gyada kai ta shige cikin gidan fuuu da uban akwatinta dake rinjayarta

wani faduwa taji gabanta yayi wanda yasanya har sai da ta rufe idonta,duk lokacin da maraqisiyya tazo gida to babu alkhairi a zuwanta,don bata taba komawa inda ta fito sai ta assasa wani bala’in cikin gidan
”lafiya?”jabir ya tambayeta cikin kulawa
murmushi tayi wanda yafi kama da na yaqe ta girgiza kai”babu komai”

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

      ▶5⃣

Babu sallama sam bisa tsarin maraqisiyya,don kaf gidan tafi kowa lalacewa,jamila ke rufa mata baya,a tsakar gida ta iske uwarta hadiza da ‘yar kanzaginta huwaila,basu ga shigowarta ba sai yif kawai sukaji na warbar da akwatinta da tayi da zamanta jabar kusa da su

inna hadiza ce ta dafe qirjinta”na shiga uku ni dije,kada dai kice min yauma korokin yayi?”
fuska ta yatsine
”yau ba shi ya kore ni ba ni na taho,don na gaji da zama da matsiyaci direban babbar mota kuma mashayi”
”oh ni ‘yar nan,auwalu matsiya cine”
”lamba daya”maraqisiyyan ta qarashe mata
huwaila tace
”aini na ma kasa magana,yara duka aure ya zama na tafashi kada,babu daya qwaqqwara?”
matsowa maraqisiyya tayi sosai kusa da su ta ma manta da tata matsalar”wai hadiza ni fa ban gane ba(haka suke kiran iyayen kansu tsaye)idanuna kamar wancan mujiyar nake gani da wani jikin wata qatuwar mota,ko gixo take min”

caraf huwaila ta kama”itace mana ‘yar nan,kinga babarku babu yadda banyi da ita ba mu tashi tsaye ko malaman da mata ke shiga muma wannan karon mu fada amma tace bata da kudi,dame zata ji,da matsalolinku ko da kisan kudinta da take nema da qyar?kawai mu qyaleta tunda wancan karon hakanan taqi auruwa to wannan karon ma hakance zata faru”
”hadiza ai ranar biyan buqata rai ba a bakin komai yake ba,ku yanzu ko kunya bakwaji,ai abun kunya ne a tattarw da ku maryama ta auri irin mijin dai da na ganta tare da shi,wlh dukkanin alamu sun nuna mai akwai ne,yaranku suna zaune?,wadanda ma aka aurar din gamu cikin wahala?,kuma ita tahaye?,si wallahi inaaaa,zaman gida bai qarewa maryam ba,ku matso kuji”

shewa sukayi bayan sun tafa kamar wasu,sa’anni wanda yayi daidai da shigowar maryam din
”sannunku,maraqisiyya ya hanya?”babu amsa sai uban tsaki da taja kamar zata cire harshenta

????????????????????????

washegari ta shirya tsaf don zuwa karbo dinkunanta da kuma yin sallama da uwar dakinta wadda take aiki a qarqashin katafaren kamfaninta nayin girke girke da shirya guraren biki,tayi sallama da maman ta,fito tsakar gidan

saiji tayi maraqisiyya na dura ashar,cikin takaici ta,juya don ganin da wa take,ita da hindatu ne ta,sirka ruwanta ta wanke kanta rabi zatayi wanka maraqisiyyar ta,sheqar mata ta,tara wsni don shiga nata wankan
”wannan banzar yayar taki ma bata isheni ba bare ke karan kada miya”
hindatu dama dake qullace da su tace
”dalla gafara can malama,banza a banza kawai,wadda ta kasa zsmsn gidan aurenta,yayar tawa kuma da,kike maganarta kuwa wallahi tako ina ta sha gabanki,aure kuwa nasan bazati irin naku ba auren jeka nayi ka,wanda dashi gwara babu”tofa baki yasan abinda zai fada baisan me za’a mayar masa ba

kamar ta zubawa maraqisiyya ruwan zafi ta,lsilayo wani uban ashar din”wlh zaki san kinyi da huwaila ‘yar hadiza,auren da kike taqama ayishi mu gani”
”Allah ya fiki ya fi wanda ya fiki ma”hindatu ta fada wadda maryam ta tura daki tana mata gargadin kada ta sake cewa komai,sai kuma abu ya dawo kanta bata kula kowa ba ta fice inda ta nufa cikin zuciyarta cike fal da tsanar halayensu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button