ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ga mamakinsu saiga mamin itama ta sauko gabansu,hawaye ne bisa fuskarta wani na nin wani,a rude abdallah yasa hanninshi yana shate mata hawayen
”idan na bata miki mami kiyi haquri,hawayenki bala’i ne mami a gurina”
sai ta kasa cewa komai,jikinta ta janyosu gaba daya ta rungumesu
”barni abdallah na nayi kuka,kuka ne na tsantsar farin ciki ba baqinciki ba,tabbas addu’a bata faduwa qasa banza,na jima ina addu’ar Allah ya baka mace ta gari,lokacin da maryam ta shigo rayuwarmu na fuskanci dukkan halayenta na gari sai maji ina maka sha’awarta,domin hasken alkhairai da nake iya hangowa qunshe da ita,ganin hankulanku bai gamu guri guda ba yasa na fidda burin daga daina na dungumi yi muku addu’a gaba dayanku,kai har wayewar garin yau maryam ce a raina da ita na tashi har ka cimmani a kitchen tunanin maryam nake”

ta janye daga jikinsu bayan ta dauke qwallar idonta,kama hannun abdallah tayi da na maryam ta hade guri guda bayan ta dora nata a saman nasu
”na godewa Allah da irin wannan zabi da ya mana baki daya,naji dadi matuqa da kasancewarki maryam cikin zuri’ata,maryam,ga abdallah nan amana ce na baki ita har bayan raina,na baki amanar abdallah har abada,bani da kowa sai shi,ki zauna da abdallah cikin amana da aminci,abdallah kaima na baka amanar maryam,matuqar ka cuceta bayan zamowarka miji a gareta ban yafe maka ba,ku kula da junaku”abinda ta fada kenan tana jijjiga hannunsu

Duk yadda yaso ya daure sai da ya kasa,qaunar shi da maryam qarara yake ganowa cikin idanun mamin,baiso maryam din taga kasawarshi saboda haka ya kifa kanahi saman hannun mamin ya sumbata cikin dabara ya goge qwallar idonshi
”nikam na dauka mami,na dauka,Allah ya tayani riqo”
”kefa maryamu na?”ta fada tana kalllob maryam wanda kanta ke duqe take cure guri guda,abune goma da shirin suka cunkushe a qwaqwalwarta,zuciyarta na gaya mata wayo kawai abdallah yayi mata,mai yasa bata bar gidan salin alin ba tare da mami ma tasan wadda abdallah ya aura ba bare ta mata wanna kandagrakin mai daddaure jijiyoyin jiki?,zata iya watsawa mami mai dimbin alkhairai da karamck qasa a ido koko zata yarda ta zauna da abdallan ta sarayar da dukkan wani haqqi da ‘yancinta da ya take,ya aureta ta sigar ‘yar burum burum,zata barshi yaci nasara a kanta ya sameta a bulus ya sameta ta sigar qarfa qarfa da banga banga?,wani sashen na zuciyarta ke mata qarfafa ata gwiwar alqawari ya daukar mata,kuma ta riga da ta cika masa gabar farko na yarjejeniyarsu,bata jin kuma zai karya alqawarin

daga qasa kuma hannunta yaketa yamutsa mata cikin wani irib salo da yake sa taigar jikinta tashi saboda nata hannun na kife ne cikin nashi tafin hannun,dob samun hanyqr tsira do son cire hannunta daga nashi tayi saurin cewa
”na karba mami,insha Allahu”cikin zuciyarta tana sauya qudirin ma’anar na karba in don kada Allah ya tuhumeta

Mami dake sauri ta koma gun mutane sai gata ta rashe a cikinsu,hira sabuwa ta barke duk da maryam na rakube gefe guda,ga zaton mami surukuta ce da kunya irin wadda tasan maryam din ko da can baya da ita bare yanzun,saidai ga maryam kuwa takura ce data sanyawa zuciyarta na nemo amsoshin tambayoyin abdallah,sai ta hada amsar sai taji duka sun wargaje,idan ta kamo nan ta qulla da can sai ya tsinke,ita kanta ta rasa dalilin da ya sanyata kasa barin gidan a lokacin da ta fahimci abunda ke faruwa,dik da tana ta bawa kanta amsar cewa girma da darajar mami ne saidai ita a karan kanta take jin amsar ba gamsashshiya bace bare ta doshi abdallah da ita

”ina zuqa,bari naje kitchen indauko wayat na kira mr stephien,dinner nakeso a shirya mib sabuwa daga nan zuwa takwas na dare a compound din gidan nan”mamin ta fada ikin zumudi da farinciki tana fita daga dakin

bayan fitarta shiru ne ya biyo baya,abdalla nata qate mata kallo ba tare data sani ba don kanta na duqe ne
”sai faman duqar da kai kike kamar wata mai gajeran wuya,amma dai ba haka mukayi da ke ba ko?,sauran qiris ki wargaza wannan matakin da kika kusa kammalashi,ki tashi ki dauko drink cikin fridge ki zuba kin,ki kuma zauna agaba na har sai maki tazo ta ganmu a haka dn mu sake wanke zuciyarta”

batasan lokacin da ta dago ba ta kalleshi da oily eyes dinta ba ta balla masa harara,idanu ya lumshe yana jin wani abu na tsirga masa,ko banza buqatarsa ta biya,burinshin dama ya kalli oily and brown ayes nata wanda tun jiya rabonshi da su
”ka isa ma?”
”haka kika ce?”
”eh”ta bashi amsa kanta tsaye tana kawar da kanta daa kanshi,gyada kansa yayi cike da mamakin tsiwarta
”za kuwa kiga kalar tawa isad,ki bar gani na kodaki gaban mami na baki muhimmanci,ina iya qin sakin naki naga wanda ya isa ya sani in sake ki”

bata san lokacin da kuka ya qwace mata ba
”tabbas abdallah ya gama raina mata hankali,a daki mutum a hanashi kuka haka ake,ita da ya kamata a lallaba ita ake raina ma wayo
dauke kanshi yayi gefe guda tamkar bsi damu bs,saidai shi kadai yasan zugin fitar hawayenta da yakeji,hakan ya sashi gaggawar fadin
”Allah ya baki sa’a kici gaba sa kukan har mami tazo ta ruskeki a haka,idan tabi ba’asi kuma na warware mata zare da abawa kinga daga haka ta daina ganin girma da mutuncin mu baki daya,ni kuma naqi sakinki tunda igiyar na hannu na,qarshe kiyi biyu babu”

Jin hakan ya sanyata miqewa da hanzari kuma cikun nutsuwa ta durfafi fridge din,binta tayi da kallo a sace sakamakon yadda rigar tabi jikinta ta fidda surarta,ta ciro lemon ta dauki glass cup saman fridge,gabanshi tazo ta tsaya ta tsiyaya mishi ta miqa masa,qi karba yayi sai harara ma da ya gallamata
”kina tsammani idan mami ta shigo ta taddaki a haka kina bani abu ba zata zargi komai ba?kin min tsaye a ka kamar zamu shiga filin yaqi”
cikin qufula da hasala tace da shi wasu hawayen sabbi na bullowa
”ya isheni ya isheni fa,don me zaka dinga juya ni kamar wata waina,wannan wanne irin abu ne?”

sake dauke kanshi yayi
”har yanzu ke din a matsayin matata kike,ko babu yarjejiya tsakaninmu dole kiyimin dukka abinda nace tunda ban sakekin ba,ruwanki ne ki rusuna ki bani ruwanki ne ki bar leminki nima na riqe aure na”
ba maganar da taqi jinin ya fadeta kamar wannan,tilas ta rusuna ta miqa masa,sai da ya wani sha qamshi kafin ya karba,bayan zuciyarshi cike take fal da tausayi da qaunarta,daga shi sai Allah sukasan abinda yake ji cikin zuciyarsa

Ai kam a hakan mamin ta samesu
”a’ah me ya sameki maryam?”caraf ya karbe
”don nace ta miqon drink”girgiza kanta mami tayi tana miqar da ita tsaye
”a’sh banson sharri,bansan maryamu da qiwa ko ganda ba bare kan mijinta,halan bata da lafiya tafiyanne batasonyi ko?”ta fada tana kallon maryam,sam ita bata fahimci ma’anarta ba rashin sanin me zata ce yasanyata saurin gyada kai don shine kadai mafita
”ayya sannu,hau gado ki kwanta bari in lalubo miki magani,kai kuma banason takura ka qyaleta ta huta har ta warke,ko kuma na riqeta anan idan bakayi wasa tayi sati”

Wayyo Allah,ai duka sai a lokacin suka fahimci inda ta dosa,a tare suka hada ido ita da abdallah,wata iriyan kunyanshi da bata taba jin irinta ba ta saukar mata,da sauri taja idonta ta qulke gam,shi din na da sauri yaja qafafunshi ya fice a dakin don bazai iya hada ido da mamin ba tunda kallon da take masa kenan,ita kam ko a jikinta,cikin gurin da take ajiyar magungunanta ta duba ta fito da pain killer da paracetamol ta hado da ruwa ta kwowa maryam din
”tashi kisha kinjk marya,kada ki biyewa abdallah ya cutar da ke ba tare da kin warke ba,idan kinga ma da takura kimin magana zan maganinsh don nasan halinshi da rawar kai sarai,idan kinki jikin bai miki daidai ba ki sanar min sai a haqura da dinner din”ita dai kamar qasa ta tsage ta shige haka ta dinga ji,wannan abun kunya har ina,sai da taga ta sha ta kwanta taja mata bargo sannan ta fice a dakin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button