ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

cikin wani irin salo mai qayatarwa dinner din ta dinga gudana,kowa ranshi fari tas cikin burgewa,tana zaune a muhallinta suka mutane suka dinga zuwa suna gaisawa da taya su murna,saidai babu daya cikin yammatan da suke son Abdallah data gani a gun,da alamu kuwa hansu zuwa gun akayi,kodai iyaye ko yan uwansu,qarfe aha daya aka taahi kai tsaye mami tace su quce bangarensu maryam taje ta kwanta ta huta.
Yana iya hangota cikin dan qaramin hasken fitilar barci takure saman gadon yayin da shi kuma ke kwance saman sofa din dake cikin bedroom din,a haka sai kayi tsammanin bacci suke saidai ko kadan kowannansu da duniyar daya shiga ita nata tunanin har yau kan amsar tambayoyinne da takeson bada su a gobe batasan ta samu failure,ya miqe ya ciro paper cikin ma’ajiyar da yake ajjiye takardu yar qarama dake can qasan gadon wanda sai ka danna wani abu take iya bullowa ya hada da biro ya dawo yayi kwanciyar rigin gine ya soma rubutu ajiki.
a qalla mintina goma ya samu kyawawa yana ruutun,a hankali yaji jikinsa ya soma masa nauyi tamkar an dora masa dutsen dala,ya sake yunqurawa da nufin daga hannun nashi a karo na biyar saidai ko alamar motsawa baiyi ba,wasa wasa sai magana ta zama babba,ya bude bakinsa da niyyar yin magan amma sai yaji kamar super glue aka saka aka manne fatar lebansa ta sama da qasa saidai.
Cikin mintina da basu gaza ashirin ba komai nasa ya daina motsi face idanunshi da kunnuwansa dake iya jin abinda ke motsi da qara baya ga haka babu wani abu dake moruwa,tuni takarda da biron hannunshi suka sulale suka fadi qasa,hannayen suka zube gefe guda,gasu a jikinsa amma ji yake kamar an cire masa su su da qafafunsa.
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶4⃣1⃣
????????????????????????????????
shin ka/kina da labarin mutune guda bakwai da zasu shiga inuwar al’arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai tasa?,ranar da rana zata matso daf da kawunun al’umma ta dinga tafasa qwaqwalwansu?,to ku matso kuji daga bakin da baya qarya
An karbo hadisi daga abu hurairah R A yace:Manzan Allah S A W yace: mutane guda bakwai Allah zai saka su cikin inuwarshi,ranar da babu wata inuwa sai tasa
1⃣ shugaba adali
2⃣ da saurayi matashi ko matashiya da suka rayu cikin bautawa Allah mai girma da daukaka
3⃣ da mutumin da zuciyarsa ke rataye da masallaci,ma’ana wanda ko yaushe jira yake yaji anyi kira zuwa sallah ya tafi masallaci
4⃣ da mutane guda biyu da suka so junansu saboda Allah,don Allah suka hadu kuma suka rabu donshi ma’ana badon wani harkar banza ba ko duniya
5⃣ da mutumin da mace ma’abociyar kyawun sura tayi kiransa zuwa yin zina ko aikata wani fasiqanci yaqi yace mata ni ina tsoron Allah
6⃣ da mutumin da yayi sadaka ya boye yin sadakar da yayi har hannun hagunsa baisan me damansa ta ciyad kota bayar ba
7⃣ da mutumin da ya tunq girma Allah a kebe shi kadai idanunsa suka zubda hawaye saboda tsananin girma da tsoro Allahn
Duk yadda abdallah ya kai ga son motsa sassan jikin nasa bun ya faskara,ya yarda ya kima saddaqar da cewa wani mummunan abu ya gama faruwa da shi,tamkar wanda dannu ya danneshi haka yake ji
babu tsumi babu dabara sai Allah haka yake ta faman ambata
sam bata san halin da ake ciki ba,saidai gaba daya ta nemi bacci a idonta ta rasa wanda ta alaqanta hakan da damuwar dake cunkushe cikin ranta,tayi juyi kan gadon yafi a qirga,ba zata iya tantance lokacin da bacci yayi gaba da ita ba
????????????????????????
qarfe biyar da rabi na asuba ta farka daidai lokacin da wasu masallatan suka kai tsakiya a sallarasu,da ddu’ar tashi a bacci ta farka a bakinta kamar yadda ta saba sannan ta lalubi wayarta don jaska dakin da babu wadatar haske a ckinsa sakamakon kashe qawayen da akayi,sai data lalubi makunnin ta kunna sanna ta sauko daga gadon,a hankali idanunta suka sauka kan abdallah wanda zuwa lokacin ya rufe idanunsa gam zuciyarshi kawai ke aiki,ya gama amanna cewa tashi ce ta zo qarshe abinda yake jira kadai shine fitar ruhinsa daga gangar jikinsa,kamar ta wuceshi sai kuma taga bai kamata ba tunda dole dai ya tashi yayi sallah.
ta tsaya saitin kanahi cikin muryar dake nuna alamun yanzu aka tashi daga barci tace
”ka tashi kayi sallah lokacin sallah yayi,anyi asuba”jin ahiru ya sanya tayi zaton ko bai farka bane,amma wannan wace idiyar kwanciya ce haka yayi ya yada hannun?,sai ta dan duqa tana bubbugar filon da ya dora kanshi tana sake fadin
”anyi sallar asuba an kusa idarwa”
jin muryarta ya sanyashi bude idabun nashi a hankali tamkar mai tsoron ganin wani abun,sai ta dan zuba masa ido ganin yadda qwayar idanun tayi jazur,a sanyaye ta juya ta ahige toilet ta daura alwala ta fito ta tada sallah,ganin har ta idar bai tashi ba ya sanyata tayi zatob ko komawa ya sakeyi ne
kanshin ta kuma komawa ga mamakinta sai taga idanuwanshi biyu
”lokacin ta zaya fita alfijir na ahirin ketowa”
”bazan iya taahi ba maryam duk yadda naso hakan,ji nake kamar an daddaureni,ki taimakamin in tashi”abinda yake aon fada kenan saidai ina bakin yayi nauyi,ci gaba kawai yayi da kallonta,saita tsinci kanta itama da kallon nashi,lokaci guda kuma taji jikinta ya mutu murus,komawa tayi bakin gadon ta zauna ta inda take iya fuskantarsa suna ci gaba da kallon juna
kusan mintina talatin suna a haka har shida da rabi
”rana fa ta fito ba zakayi sallar bane?”sai taga ya maida idanun nashi ya lumshe,hakanan gabanta taji yayi wata mummunan faduwa,sai ta kasa zaman ta qarasa inda yake,abu na farko data fara lura da shi shine hannunshi da ya zamo qasa tunda ya farka bata ga ya gyara kwanciyarshi,ta sanya hannunta tadaga hannun taga ko zai gyara saidai tan sakinshi ya biyo ta,ta sake gwadawa har sau biyu babu banbanci
batasan lokacin data furta
”abdallah lafiya kuwa kake!”cikin tsorata da rudani
idanun nasa dai taga ya kuma zuba mata tamkar zai hadiyeta,sai ta shiga kiran sunansa a jejjere saidai ko guda bai amsa mata da shi ba
Lokacin da zuciyarta tayi mata hasashen abinda ya samu abdallahn jiri ne ya debeta ta zube a nan tana fadin
”me ya sameka?,me ya sameka don Allah abdalkah,ka bude baki ka gaya min”
inda zai iya da ya mata maganar amma babu iko
sai kuma ta zabura ta miqe da gudu ta fice a sashen nasu tayi bangaren mami
da sauri nene ta toshe bakin zahariyya da ta dan saki ihun farinciki ganin shigewae maryam bangaren mamin a hargitse
”nene Allah yasa ya sambade lahira”
”ko bai mutu ba to yana kan hanyarshi ta mutuwar”ta fada tana duban zahariyya
”don da ya kammla wucewar da ihun kururuwatsu kadai ta ishemu albishir”
saman mamin ta haura kai tsaye ta fara bubbuga qofar dakin nata ba qaqqautawa,tunda taji bugun ta tabbatar ba lafiya ba,ga zatonta ma abdallah dinne,tunda ta tashi dama takejin jikinta ba normal ba yadda ta saba jinsa,da hanzarinta ta murza muqullin ta bude qofan,kama hannun maryam tayi wadda taga tsagwaron rashin hankali kwance kan fuskarta
”lafiya maryam ne ya faru?”
fara jan mamin tayi
”mami zo kiga abdalkah,zo ki ganshi mami…”ta qarashe cikin rushewa da kuka