ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

tamkar gini haka maryam ta koma,mafarki ne koko gaske,almara ce ko tatsuniya ce,ji tayi wasu hawaye masu dumi na sauko mata,batasan sanda ta tsinci bakinta na furta
”ya Allah kada ka jarrabemu da wata jarabtar ta daban bayan wadda muke ciki,ubangiji idan ka saka mana wannan cikin sabuwar karrabar da zaka mana ba zamu iya jurewa ba nida abdallah,ya Allah sassaucinka muke nema”bibbiyu ta dinga gani a haka ta bar bangaren zuwa nasu,tafi qarfin minti talatin zaune afalonsu tana rasgar kuka
wanna wace iriyar jarrabar rayuwa ce da suka wayi gari da ita da safen nan,anya ma kuwa da mami tayi magana?,mamin abdallah fa,mai tattali da qaunarshi akoda yaushe,mai son ganin farinciki da walwalarsa,mamin da tasha bata amanar abdallah,tasha gaya mata bata da kowa sai shi ta kula mata da shi bata so ta rasashi yadda ta rasa mahaifinsa
cike da tantamar ba mamin bace ta dauki wayarta ta kira number dinta don ta tabbatar,saidai dagawar farko ta kuma cin karo da muryarta tana fadin
”wai nikam sa’arki ce maryam?,lallai na sakar miki da yawa kinga gadon barcina,sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki kamar yadda nene tace”jin sunan nene kawai data ambata ya sata dauke wayar daga kunnenta tana kiran sunan Allah,tabbas akwai wani abu na daban dakeaon kunmo kai
”Allah na roqekakoma meye ka kawoshi da sauqi ya arhamar rahimeen”ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka
kiran sallar la’asar ya fargar da ita abdallah data bari,da sauri ta miqe a rude ta tura qofar dakin ta shiga,yanayin fuskarsa kawai ta kalla ya tabbatar mata ya gaji da kwanciyar,sai tausayinsa ya kamata,da sauri ta qarasa kan hadon cikin rawar murya
”kayi haquri don Allah,mun barka kai kadai wallahi ma…..”
maganr tata ta katse saboda yadda taga ya zubawa fuskarta ido,tamkar mai son tambayarta abinda ya sanyata kuka,sai a lokacin ta tuna da hawayen fuskarta,kawar da kanta tayi gefe tana qoqarin boye damuwarta,kusan minti biyar kafin ta dawo da kallonshi saiai har yanzu ita din yake kallo,data fuskanci tambaya ce yake mata sai ta girgiza kai
”ba kuka bane abu ne ya fada min io kuma daga nan sai ma dauro alwala da yaqi fita….bari na kawo maa abincinka”ta fada tana miqrwa da saudi ta fice adakin yayin da ya bita da kallo zuciyarshi cike da wani abu dake masa yawo ko ina cikin jininshi
Da qyar ta iya jingina ahi da fuskar hadon ta tattare si da filota zauna dab da shi har cinyarta na gogar tasa,ya lumshe ido cikin zuciyarshi data zame masa abokiyar tadi yake fadin
”so bala’ne,duk cikin yanayin da kake baya barinka ka huta?”
”bismillah karbi”yaji tana fada saitin kunnenshi,tsigar jikinsa ta tashi,a hankali ya bude idonshi ya sake zubasu a kanta,yana hango bacin rai da tashin hankali qarara kan fuskarta,da yana da baki zaiso ya tambayeta yaji me ya sameta?,bai taba tunanin zata ci gaba da zama da ahi a yadda yake ba,yayizaton a washegarin randa lalurar ta sameshi zata hada yanata yanata ta qara gaba ko babu takardar saki,kwatankwcin yadda yaji wasu matan nayi ga mazajensu idan lalura ta samesu,wasun su kun hayayyafa ma tare amma basu iya zama da kai da,bare su da kwana bihu kacal sukayi a matsayin ma’aurata.
kallon taga yayi yawa
”ka karbi abincin”a maimakon taga ya karba sai ya juyar da kanshi yana duban bakin qofa,hakan ya nuna mata mami yake son gani,hakan sai ya sake karyar mata da zuciya,ta sani mawuyaci ne ya karbi abinci idan bai ga mamin ba,saboda haka ta ajjiye cokali ta kuma daukar wayarta cike da fatan ta samu sauyawar yanayin mamin
”mami ya farka yaqi ya karbi abincin keyake jira”
”ke!ke fita daga idona,wai shin komayyar ce ke da gaske?,to wallahi zan ci iki mutunci fiye da zatonki,ko rayuwarku wajibi na ce,kuje kuji da kanku kada ki kuma kira na na gaya miki”daga haka ta katse wayar,hada idanu sukayi da abdallan da alamu yaji wani abu cikin abina mamin ta fada,mutum ne mai kaifin ji,hadiye kukan da yake taso mata tayi ta kuma diban abincin a cokali ta miqa masa tana fadin
”kayi haquri ka karba,anjima mamin zata zo kaji”
????????????????????
wasa wasa abun sai ya zama gaake,tun ranar data yi shigowar qarshe mami bata sake waiwayarsu ba,sam ta mance da su ma baki daya,gaba daya an canza mata alqiblar rayuwa,kusan gidan ma baki daya ya koma hannun nene sai abinda ta shimfida wa jama’ar gidan ciki harda mamin,a hankali a hankali suka dinga karbar takardun lamfanoni filaye gidaje da duk wata plaza na abdallahn daga hannun mamin,ba tare da musu ba haka zata dauka ta damqa musu
hisham baisan halin da ake ciki ba,bai an kara ba sai da yake duba kamfanin yin flower na abdallahn ya tadda adnan dare dare kan kujerarshi kamar wanda ya gada daga gurin ubanshi,da ya sami mamin ya mata maanar ranar ya ga bala’in da bai taba gani ba gurinta,har da ja mishi kunnen matiqar bai dauke idonhi daga lamuransu ba zata sa ahanaahi shigowa gidan kamar yadda tasa aka hana duk wani dan uwanta ko na maryam zuwa gidan,tilas ya ka bakinshi on ya san daina zuwanshi gidan ba qaramin tagayyra zai haifarwa abdallah da maryam ba,ya dai cika da mamakin canzawar mamin lokaci guda,tsana nin biyayya da bi sau da qafa da takewa nene
????????????????????
Sau biyu tana leqowa taga ko bacci ya daukeshi?wanka take son tayi ta sauya kayan bacci ta kwanta,a karo na uku ta tadda idanunshi ruf alamun ya samu bacci kenan,ta jima tsaye akansa tana qare masa kallo,a hankali ta sanya hannunta cikin tattausan sumarshi,yana buqatar a rage masa ita saidai bazai iya magana ba,cikin ranta ta qudirci gayawa hisham gobe ko zai iya masa yana da clipper tunda ita bata iya ba,jin ya motsa ya sanyata saurin janye hannunta tsoronta kada ya farka,sai da taga ya bar motsin kana ta tofa masa fatiha da yatul kursiyyun da take yawan tofa mishi akai akai ta juya ta isa bakin cupboard dinsu ta soma cire doguwan rigan jikinta
a hankali ya bude idanunshi ya zuba mata ido duka batasan me akeyi ba,ta janyo towel ta daura tayi banaki,ya lumshe idona wani dan murmushi ya subuce masa,maryam maryam bai san maryam ba sai yanzun,yanzun ne yasan maryam,cikin tunaninshi yaji tana qoqarin itowa ya maza ya maida idanunshi ya lumshe,yana iua hagota tana shiryawa tsigar jikinhi na tashi,ji yake ina ma yana da lafiyar da zai nuna mata irin soyayyarta dake danqare ciki zuciyarshi,har ta kammala ta zura rigar baccinta ta dora dan hijabinta a kai
Bata taba yarda ta kwanta kan gadon matuqar idonshi biyu,sai bacci ya daukeshi take lallabowa ta kwanta ga tsammaninta duk bai sani ba,saidai data kwanta din ko cikin bacci yake zai farka saboda wani dumi na musamman yake ji daga garta,yau din ma lallabowa tayi ta kwanta gefanshi bayan ta gama qare masa kllo kamar yadda ta saba,a hankali gajiya ta mamayeta,bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,a irin wannan lokacinne shima yake samun damar qare mata nashi kallon,yakan tsinci kansh ciki wani irin nishadi a lokacin
ya daga hannunshi da niyyar janyota cikin jikinshi ya kusa sau goma amma ya kasa,ya saki nannuyan ajiuyar zuciya yanajin radadin hakan cikin ranshi.
cikin sa’a tayi wani juyi tashin farko sai gata cikin jikinshi,murmushi yayi yana godewa Allah tare da dora kanshi saman kanta,duk da hijabin jikinta hakan bai hanashi jin dumi da qamshinta ba
sannu a hankali sai kuma ya dinga jin motsi kamar ana hawowa saman da suke,yaci gaba da kallon bakin qofar don ya tabbatar yau maryam tayi mantuwa bata rufe qofofin ba,idanunshi fes kan qofar yaji an turo an shigo,tashin farko aka dallare dakin da fitila mai tsananin haske kai tsaye hasken ya iso har inda suke
”wal masakinu bakayi bacci ba?”yaji an fada kana aka kunna duka qwayayen dakin,fuskar adnan ta bayyana
”gwara ma da bakayi baccin ba ai kaga ka gani da idonka tunda gani ya kori ji ko?,yau zan cika burina,zan kwanta da matarka agabanka,zan cusa maka baqinciki abdallah irin wanda na dade ina sha akanka,ka fini kyau,ka fini matsayi ka fini kudi ka fini nasaba hakanqn ka fini farinjini,yau zan kuma nakastaka kafin lokain da muka diba maka na mutuwarka ya cika,kabi bayan tsohonka ku hade acan kafin tsohuwarka ta biyoku”