ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

itakam zahariyya ma kasa cewa komai tayi
”amma fa nene,naga hannun abdallah ya dawo aiki”ya fada yana kallon nene,da sauri zahariyya ta tashi zaune daga kashingidar da adazu tayi tana kallon fuskar nenen tana zazzare idanu
wani murmushin ta kuma saki tana girgiza qafa
”ko duka jikin abdallah ne ya dawo aiki wanna karon naci alwashin abdallah bazai qara sati guda araye ba,don nima……”
tilas suka katse maganar kowa ya watse sakamakon shigowar zubaida dakin
nenen ta bita da kallon mamaki don tayi zaton ciwon ABDALLAH zai sata a wani hali sai ta lura ma sam tunda ya fara cutar ko hanyar part din bata yi,hankalinta kwance kamar bata da wata damuwa da shi,hakan ba qaramin dadi ya yiwa nenen ba

????????????????????????

Su uku ne cikin bedroom din,hisham da abdallah sai maryam dake zaune kan ressing chair data janyota bakin gadon inda abdallah da hisham ke kai hisham na bawa abdallan kunun gyada bayan masa wanka da canza kaya da aka masa ckkin baqin t shirt da trouser da suka sake haska shi

farinciki ne fal zicjyar hisham sakamakon ci gaban motsa hannun da abdallah ke iyayi yanzun,yana bashi kunun suna hirar da maryam duk da nata bai wuce eh ko a’a,ba gwanar magana bace ama sanann bugu da qari kallon da abdallan keta tsareta da shi ke dada takura ta,wani kallo ya koya daga wayewar gari zuwa yanzun,duk wani motsinta na kan idanunshi,lafiyarta yakeson ji amma babu bakin tambaya
”kai man,irin wannan kallo haka ko na baku guri ne?”inji hisham yace da abdallah cikin zolaya,kallonshi kawai abdallan yayi ya saki murmushi,duk sai suka zuba masa ido don tunda ya fara ciwon wannna ne karon farko da suka ga murmushi kan fuskarshi

cikin dariya hisham yace
”kai mutumina,anya daren jiya ba soyayya aka sha ba kuwa?”kunya ta kama maryam ta duqar da kanta ,yayin da abdallah ya sake wani murmushin yana duban fiskar hisham bisa dukkan alamu akwai abinda yake son fada wanda ya kasa fada
”Allah ya baka lafiya abdallah”inji hisham yana dafa kafadanshi,ya dubi maryam
”me kikace dazu yana buqata?”
kanta na sunkuye tace
”shaving za’a masa,naga kanshi yayi suma da yawa”
ya dan duba agogonshi ”eh gaskiya ya kamata,bari na masa na kai ke sqi kiyi masa na fuskanshi”
”ai ban iya ba”
”eh,ya kamata ki koya madam,zan nuna miki,akwai meeting da zamu shigavda ma’aikatan kamfanin suger na abdallah,don ina tsammanin gwara kawai a rufe kamfanin har zuwa lokacin da zai samu alfiya,saboda barnar da ake cikin kamfanin tayi yawa”

”Allah ya taimaka” ta ce bayan ta miqevta dauko masa kayan askin,ya kammala kana ya nuna mata yadda zata masa na fuskar ya musu sallama ya wuce ta bishi da godiya

gefanshi ta dawo ta zauna ta fara matso cream din,a hankali take shafa masa a gefe da gefan fuskarshi,idanunahi qyar cikin nata,nauyi takeji da kunyarsa duk lokacin da ya zuba mata idanunshi,a hankali ta janye qwayar idonta tana ci gaba da shafa masa din,ta kammala ta dauko shever ta fara masa askin,ajiyar zuciyan da ya saki ya sata saurin kallonshi cikin tsoro,cikin sassanyar muryarta tace
”ko na yanke ka?”murmushi ya mata ba tare da ya nuna alamun a’a ba,kusan sakanni uku sannan taci gaba,a hankali taji ya riqe hannun nata da take shaving di dashi,ta sake waiwayo ta kalleshi shima din ita yake kallo
ta langabe kai
”da zafi ko?,dama na ce masa ban iya ba…..”bata qarasa ba taji ta kan qirjinsa sakamkon janyota da yayi ya rungumeta tsam

dukan uku uku qirjinta ya shiga yi,tayi yunqurin tashi taji ya sake maidata,idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake,dukkansu suna jin bugun zuciyar junansu da ta qara gudu fiyeda yada take bugawa,sannu a hankali taji kasala na kashe mata duk wata gaba ta jikinta,jikinta ta saki batasan yadda akayi bacci yayi awon gaba da ita kan qirjin nasa ba,shi din ma yanayin ya masa,ji yake amar ya tsaida lokaci don su dawwama a haka,tun yana jin saukar numfashinta har shima baccin yayi gaba da shi

????????????????????

kusan lokaci daya suka farka,da hanzarita ta miqe daga jikinsa don tunawa da cream da ta bar masa a fuska,idanunshi a lumshe yake kallonta,sai taga ya kai hannunshi gefan kunnenta ya ciro wani abu ya nuna mata,cream dinne da sauri ta dauki madubin dake hade set da shaver din ta haska,ai kuwa gashi nan ta kwaaheshi ya bata mata fuska ta dubeshi suka hada ido sai suka saki murmushi tare,dan towel din askin a janyo ta goge fuskarta ta matsa ta dauki shaver zata ci gaba da askin,dora hannunshi yayi saman nata hannun da sauri ta janye hannun nata saboda tsigar jikinta da taji ta tashi,ya karbe abun askin ta fuskanci me yake nufi don haka ta dinga haska masa yana askin da kansa,idan ya gaji ya tsaida hannun nashi ya huta tunda har yanzun ba wani qwari ne da shi ba
towel tasa mai mai kyau ta goge masa fuskan bayan ya gama,tana shirin miqewa taji ya riqo hannun nata ya sanya tafin hannunshi cikin natan ya matsa su sannna ya gyada kai ta fuskanci godiya yake mata,murmushi kawai ta saki ta sunkuyar da kanta kana ta zame hannun nata ta sauka daga kan gadon tana tattara kayayyakin da sukayi amfanin da su har yanzu idonshi a kanta yake,yanayinta kadai burgeshi yake,kominta anutse cike da tsafta tausayi da kulawa,ya maida idonsa ya lumshe bayan yaga fitarsa yana addu’ar Allah ya bashi damar da zai nuna mata nashi kalan halaccin koda bata sonshi

da uammain mubarak ya kawo wheelchair da hisham yace ya kamata a fara dora abdalla atleast zai dinga jin dadi idan an fita dashi daga bedroom zuwa parlour zuwa balcony din saman tunda ba zata iya saukowa da shi ba falon qasa,yaji dadi kuwa don alamu sun nuna afuskarshi,yawanci idan la’asar tayi aka dorashi zata yita shawagai da ahi daga parlou zuwa kitchen zuwa balcony din wani sa’ilin ma ya mata alaman su zauna cikin kitchen musamman idan tana girki,ganin zaman shiru suke yi yasa tana girkin tana bashi labaraimasu debe kewa,hakan kuwa na matuqar sa farinciki a zuciyarshi,don zata ga fuskarsa ta fadada sosai da murmushi alamun yana jin dadi

saidai kallon qurillar da abdallah ya koya tilas yasa take zama da hijabi,don ba qaramin kunya yake bata ba,ko ina yaso kalla kallonsa yake kanshi tsaye,da sun hada ido kuma ya wani lumshe ido ya basar kamar bashi ba,wani lokacin murmushi take cikin zuciyarta tace
”hali zanen dutse,babu abinda ke saiyawa dan adam halinshi,har yau halin abdallah na basarwa da waskewa na nan cikin jininshi”

mrs muhammad ce

????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

     ▶4⃣3⃣

An karbo daga nana Aisha Allah ya qara yarda a gareta tace:naji manzan Allah S A W yana cewa ”ya Ubangiji duk wanda aka dora mishi wani shugabancin na al’umata,ya tsananta musu Allah ka tsananta masa shima,wanda aka dora mishi wani shugabanci na al’ummata ya tausasa ya sassauta musu Alla ka tausasa masa ka sassauta masa shima

Qarfe biyar da rabi ne na yammaci mai cike da ni’ima da dadi kasancewar ko kusa garin babu rana sai lullumin hadari da ya lullube sama,su biyu ne zaune cikin falon yana kan wheel chair tana kan kan kujera saidai suna facing juna ne
novel ne a hannunta take karanta mishi sannu sannu cikin daddadar muryarta,tunda ta kifa fuskarta alittafin data kare fuskarta da shi bata dago ba saboda nauyin da kunyar kallon da abdallahn yake mata,gashi hakanan yaqi yarda yau a saka mashi kaya complete,duk wanda hisham ya ciro sai ya wurgar shi daminshi suke,wando three quater ne ajikinshi da riga armless duk wata qirar jikinsa ta bayyana

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button