ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali yasa hannunshi ya riqe littafin yayi qasa da shi tavdago kanta suka hada idanu,ido daya ya kashe mata yana murmushi don ya fuskanci abinda ya sata qin sakewar,littafin ta sakar mishi ta dora fuskarta saman cinyarta cike da jin kunya,taba kanta taki yayi sai taqi dagowa,ya daga littafin ya dan buga mata kadana akanta tare da cusa mata shi.
A hankali ta dago da zummar dauke littafin taci gaba da kare fuskarta,rubutu ne baro baro a bangon littafin I LOVE U,wani feeling ta dinga ji tana sake maimaita rubutun tamkar yau ta fara ganin kalmar,a dan sace ta rage tsawon littafin idanunta suka fito,karaf suka hada idanu da abdallahn daya zubawa cover littafin ido,tayi azamar maida littafin saidai tuni ha riqe da hannunshi daya yana ci gaba da kallonta,ji tayi bazata iya hada qwayar idanunsu ba saita sauke qwayar idanun nata kan cinyarta tana kallon yatsun hannayenta.
Qarar bugun da akayiwa qofar dukkansu sai data basu tsoro,kusan a tare suka kalli qofan,mami ce ke shigowa a burkice idanunta a kansu, qaraso gabansu ta ja burki
”sannunku qananun ‘yan ta’adda,wato har kisa kuka so yimin cikin gida na ko?,to wallahi baku isa ba matuqar kuka ci gaba da yunqurin taba lafiyar wani cikin gidan nan zan iya tattarku kubar min gida tunda dai ba naku bane,kada ku kiskura ku sake aikata wani abu mai kama da haka don ba gidan ‘yan ta’adda bane nan”duk maganar da take kan maruam na duqe a qasa,yayin da abdallah ya zuba mata ido cikin qunar zuciya da tashin hankali,me ya sami maminshi haka?me ya canza masa mami?,mamin da bata qaunar taa ko sauyawa fuskarshi tayi,mami mai tattali da qaunar farincikinsa,mami dake qauqnr maryam ta dauketa tamkar diyarta ta cikinta
ta kalli maryam”kuma ki gaggauta zuwa ki nemi yafiyar nene da danan idan ba haka ba wallahi sai na wulaqantaki,idan banda ma ke butu ce shegiya mara mutunci daga zuwa ya duba lafiyar mijinki sai ki masa irin wann mummunar sakayyar,na baki nan da minti talatin kije ki basu haquri”ta juya zata fota suka hada ido da abdallqh,hara ra ta wurga masa saboda jin wani abu na son taba zuciyarta,sai kuma wani abu daga can daban ya taso ya danneshi
shiru ne ya ratsa falon bayan fitarta,dukkansu kansu na sunkuye zuciyoyinsu na saqa musu abubuwa mabanbanta,ganin ya kusa gota mibti talatin din da mami ta bata ya sanyata miqewa da sauri,hannunta taji an damqo,ta waiwayo sai taga abdallah ne,a hankali ya dao idonsa suka hada ido,da sauri ta kawar da kanta saboda tashin hankalin da ta gani cikin qwayar idanunshi basu musaltuwa,fararen qwayar idanunshi sun juye sun koma ja baya ga jijiyar kanshi da ke tashi,kai ya girgiza mata alamar ba zata je ba,itama kan ta girgiza kana ta dawo gabanshi ta durqusa tace
”kayi haquri ka bari inje din,umarnin mami nake qoqarin cikawa ba donsu zani ba,kada ka manta har yau mami na matsayin uwa ne a garemu kaga ya zama dole mu bi umarninta don gamawa da duniya lafiya indai ba ya sabawa addini ba”
shiru yayi ma wasu ‘yan daqiqu kana ya daga mata yatsunshi guda biyar alamun minti biyar ya bata,guada kanta tayi sanan ra miqe ya bita da kallo har da fice
tana gab da shiga waitin falo inda anan qofofin bangaren nau yake ta hango adnan,muta ne uku ne zabga zabga baqaqe,cikin baqin kaya masu qirar samudawa biye da shi,kallo daya zaka musu ka tabbatar cewa babu masaukin imani cikin zuciyarsu,mamaki ya cikata duk da tasan cewa lokaci lokaci zaka ganahi da ire iren mutanen a matsayin abokanshi,sai ta kasa wucewa ta rakube har suka wuce,tazarar minti biyar ta bada tasan zywa lokacin sun shiga koma ina zasu ahiga sannn tabi bayansu,a qofar waiting parlour din suka kusa karo da mami wadda ke sanye da kayan aiki da alama asibiti zata fita taja da baya ta bata hanya,harara ta watsa mata mamin kana ta fice,girgiza kanta tayi kawai tabi ta da kallo,kallo daya zaka mata ga wanda ya santa yasan cewa ta canza,tsaftarta har yanzu tana nan saidai duka gayun nan babu shi,bata mantawa shekaran kiya doctor safara’u abokiyar aikin mamin ta kira maryam take tambayarta me yake damin mamin ne,kullum tazo office bata da aiki sai kuka,tambayar duniya kuma ba zara gaya maka abinda ke damunta ba,magana daya zata gaya maka shine babu komai
Ganin babu kowa cikin falon qasan ya sanyata nufar sama,tana atep din qarahe na matattakalar ta soma jiyo maganganu,tamkar an dasata agun ta kasa gaba ta kasa baya
”yace saidai mu mu qarasa aikinmu,dalili kenan da yasa nace ka nemo min su mugu,wanna karon zamuyi aikin qarshe kan abdullahi,jibi da daddare nake so ku kashemin abdullahi,kafin ranar zansan duk abinda zanyi na kori yarinyar daga gidan nan,idan kuma tayi taurin kan qin tafiya na baku dama ku hada harda ita….”
”haba nene haba nene,ya zaki ce a kasheta bayan kinsan qudirina akanta…”adnan ya katseta
”dakata min adnan,wanna karon bana son matsala kowacce iri ce,mata gasunan bila haddin,koda an kasheta da zarar ka samu ‘ya’yan banki kana iya samun dubunta ka huta da su ko ka auresu,mubar wannan maganar”
bibbiyi ta dinga hada matattakalar benan tana saukowa,badon nutsawa da sukayi kan maganr ba da babu abinda zai sanyasu jin takun saukarta,saidai ina dukkansu hankalin yayi gaba,a inda ta bar abdallah ta tarar da shi,a hankali ya dago kai yana dubanta,gqnin irin birkicewar da tay ya zuba mata ido kamar mai tambayarta,cikin rawar jiki ta tura whewl chair din suka ahige brdroom ta maida muqulli ta rufesu,jikinta na rawa ta dauki wayarta,ta fara qoqarin neman numbers dib hisham saidai bata yi sa’a ba ta samesu a kashe,bakin gadon ta koma ta dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka,tana kallon abdallah na daga mata hannu saidai ta kasa ce masaa komai,tausayinsu su duka biyin ya lullubeta
Misalin goma na dare ta samu wayar tashi ta shiga,da sauri ta fita adakin ta canza daki don bata son abdallah yaji komai,shi,kansa da baisan meke faruwa ba hankalinshi a tashe yake tun dazun fuskarsa ta nuna,bata jira jin komai daga bakinsa ta fara fada masa abinda ke faruwa
innalillahi wa inna ilaihi raji’un kawai yake furtawa,tabbas zarginsa ya zama gaskiya
”ki saka nutsuwa afuskarki maruqm,kada ki sake ki nuna musu kiji wani abu,yanzun haka ina kaduna amma gobe qarfe biyar da rabi na asuba zan taho,insha Allahu duk inda goma na safe yake ko tara na iso kano,na miki alqawarin babu abinda zai sameku,a gobe zan fiddaku daga cikin gidan insha Allahu”
Yadda ta kwana tana sallah haka ya kwana akan whellchair yana kallonta,cikin jikinshi yake jin wani mummunan abu na tunkaro su,yanayin data shiga kadai ya isheshi amsa,sam yaqi yarda ma akwantar dashi,da safe saiga nenwn zahariyya harda danna wai sunzo duba abdallahn,yanayin fuskarta idan ka kalleta dik qwaqwarka ba zaka tsammaci gana cikin mummunan tashin hankali ba,ba qaramar jarumta ta nuna ba,haka suka qaraci kallonau suka fice maryam ta bisu da ido cike da mamakin qarfin hali irin nasu
mubarak ma da yazo sam qin yadda abdallah yaui ayi masa wanka,abincin ma da qyar ta samu yaci,ya fahimci manufarsa yana son jin abinda ke faruwa ne a ganinta kuma bai kamata yaji din yanzu ba
????????????????????????
yana kan wheelchair din yatsunsa soke cikin na juna yana kallon su
tsaf hisham ya gama hada duka wani atm card takardun companies filaye gidan gonaki da na duk wani estate da plaza na abdallan ya sanya cikin wata jaka baqa ua zuge zif din,maryam yasa ta ciro babban bargunan dake ninke gefe daya kan gadon,ya jera dukkan filallukan dake kan gadob ya lullubesu da bargon take suka tashi kamar mutum kana ya qarasa inda abdallah yake da niyyar sauko da shi daga kan wheel chair din