ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

da sauri take gyada kanta ,kana ta bata umarnin ta koma inda ta fito
hawaye ne kawai ke zuba daga idon nene tana sharewa,idan banda darajar mami da take tausayawa babu abinda zai zaunar da ita a gidan,abubuwa marasa dadi da idanunta ke gane mata wanda ke faruwa shine ummul aba’isin zamanta cikin gidan badon wani abu ba

????????????????????

babu wanda ya sake cewa komai har suka qarasa gidan hisham din,gida ne madaidai ci mai kyau wanda ke dauke da makeken falo kitchen dining area sai dakunan bacci guda hudu

A falo suka tadda abdallah kan kujera,gwiwarta a sanyaye ta qarasa gurinshi kanshi na duqe a qasa,a gabanshi ta durqusa ta sanya hannunta cikin nashi tana kallonshi,sam yaqi daga idanunahi ya kalleta,hakan na nuna mata cikin tsananin bacin rai yake,ta leqa fuskanahi idanunahi biyu don tana iya ganin qiftawar idanunshi,sai zuciyarta ta karya ta tura kanta tsakanin cinyoyinsa da fuskarsa sai a sannan suka hada idanu,ya zuba matq idanun naahi da suke har yanzu kalar ja

shigowar hisham falon ya sata miqewa,ya taimaka suka shiga da abdallah daya cikin dakunan dake falon,dakine mayalwaci mai hade da toilet,gado madubi side bed sai cupboard da kujera doguwa qwaya daya da carfet da ya malale qasan dakin da shi a maimakon tiles
”zan fita amma bazan jima ba zan dawo”
ya qarasa gaban abdallah yace
”abokin sai na dawo mintina kadan zan dawo”kai kawai ya gyada masa ya miqa masa hannunshi sukayi musabaha

????????????????????????

Qarfe goma na daren ranar suka fito daga maboyar da nene tayi musu cikin dakunan barcinta,gaba dayansu baqaqen kaya ne ajikinsu hatta da mask din da suka sanya,kowannensu wuqa ce boye a jikinsa

taku daya biyu nene tayi ta tsaya a gabansu,dukkansu sun fita tsawo nesa ba kusa ba,ta dubesu daya bayan daya
”banason a samu kuskure ko sabani cikin aikin nan,shekaru na kwashe masu yawa ina neman wannan damar,saboda haka ku tabbatar komai ya tafi yadda ake so”
dqya daga cikinsu wanda da alama shine oga ya buda hanci ya shaqi iska
”haj,sanin kanki ne munsan aikin mu dalilin da yasa kema kika neme mu kenan”
gyada kai tayi
”haka ne kam”

da daya da daya suka dinga fita har suka isa sashen abdallah,jijjiga qofan suka yi suka jita gam hakan ne ya tabbatar musu a kulle take,don haka kansu tsaye ba tare da wani tsoro ko shayi ba tunda sun san cewa babu security ko daya cikin gidan bare su jisu duka nenen ta bawa kowa aikin da har su gama abinda zasuyin ba zasu riskesu ba,take suka hau lallauya qofan da wani shegen qarfe suka ajjiyeta saahe guda kana suka kutsa ciki

Sau uku yama luma wuqa kan tarin filallukan dake tare a kan gadon ganin qamas babu alamun jini ya sanya su yaye bargon,a mamakance suka kalli juna kana daya daga cikinsu ya ciro waya ya kira nene,da zumudinta ta daga kiran ga tsammaninta sun cika aikinsu
cikin mamaki da fushi take fadin
”wanne irin babu kowa?kada ku gauamin maganar banza mana,yaron da ko motai bai iyayi ina zaije?,kuma tun jiya babu kowa a tare da shi balle ace ya fidda shi?”
cikin ciccijewa ya maida mata amsa
”kinga hajiya duk ke kika san wannan,kizo kawai idonki ya gane miki”
da azama tq fito ita da zahariyya da danan suka bazamo bangaren abdallan,surutai take tayi kamar wadda ta samu matsala a qwaqwalwarta don bata taba sawa cikin lissafinta cewa wannan karon akwai cikas din da zasu samu ba

cirko cirko sukayi cikin dakin bayan kammala duba ko ina na cikin gidan ciki har uwar dakin mami wadda batasan me ake nema ba,ta dai ga nenwn kai tsaye ta ahige mata daki tana dube dube daga bisani ta fito
”taya ya abdallah ya fita daga cikin gidan nan”
”ke za’a tambaya hajiya”cewar ogansu yana maida locker da tasa ya balle ta dakin abdallan wadda basuyi katarin samun komai ba sai rafar din dubu hamsin

”miqo min wadan nan kudaden,yanzu hatta da takardun kadarorinsa ma ace babu su cikin dakin nan,anya wani baisan abinda muka shirya ba kuwa cikin gidan nan,anya banu mai,mana labe da leqen asiri?”ta fada tana zare ido kamar wata zautacciya
kudin ya kalla kana ya dubeta
”ban fajimci me kike fada ba,wannna kidi ai namu ne ladan zaunar damy da kika yi nuka kwana cikin gidanki,ai lissafi zamuyi kawai ki cika mana sauran miliyan dayan da mukayi da ke zaki cika mana”
”idan aiki yayi kyau ba,ana ta kai wa yake ta kaya,kwananku kuma cikin gida na ai ku kuka qaru da ni bani na qaru da ku ba asara ce ma ta hauni goma da goma,tunda har ‘yata na baka ta tayaka kwana ko?baya ga haka ma ni a yanzu bani da miliyan daya bani da dalilinta,da aiki yayi kyau ne ma na tabbata cikin dukiyar da zamu samu ba komai bane cire miliyan daya daga ciki ”ta fada tana matsowa gabansa tare da zazzare idanuwa,don ji take su suka ma ja mata duk wata asara da ta fada matan

Dariya ya sheqe da ita
”haba hajiya,kinci qarya kin kwana da yunwa,muba qananan makasa bane ba irinnu akewa haka ba”ya sake matsowa inda take har tana jin warin wiwinshi na dukan hancinta,yatsunshi ya daga guda uku
”kwana uku kacal na baki ki turo mana ragowar kudinmu,wlh wlh wlh ko ke kikayo naqudata matuqar baki turo da sauran kudin nan ba ke da ‘ya’yanki ki tabbatar kuna cikin masifa,domin duk ranar dana waiwayeku sai kun buraci mutuwarku akan rayuwarku,na baku dama ku gaggauta warware harqallar da kuka qulla dani”

ya juya zai wuce adnan yasha gabansa cike da taurin kai da jin shima karansa ya kai tsaiko yana ciccije lebe cikin son nuna shima jan wuya nebayan shi kansa yasan fanko ne lamba daya,kafin yace komai yasa kan wuqar hannunshi ya daki kanshi saiga adnan din a qasa,ihu nene ta saka tayo kansu,da tsinin wuqar ya juna ta ta koma baya tayi luf sai da suka kammala ficewa ta saka kururuwa ta biyo bayansu ko Allah zaisa taci sa’a wani daga cikin security din sun dawo suyi ram da su,saidai ina,babu wanda ta samu bakin get din kamar yadda ta watsa su don gabatar da aikinta

????????????????????????

ta kai ta kawo tayi hakan ya kusa sau goma sha biyar,ji take kamar zata hau bori ko hauka kafin ta samu guri ta iya tsugunnawa,ta dubi adnan da kanshi yasha dauri da bandeji da zaharkyya wadda ke zaune tana faman hade fuska,babu wanda take ganin laifi sama da nene,don ita kam ta gaji da wanna jeka ka dawo din,ta riga da ta yanke ma kanta hukuncin abinda zata aikata matuqar wannan karon haqarsu bata cimma ruwa ba kamar sauran lokutan baya
”babu shakka cikin hisham da maryam akwai wanda ya fidda abdallah daga cikin gidan nan,ko kuma daya daga cikinsun ya aikata hakan,kuma nafi zargin wanna shaidaniyar ce marya,tabbas kuwa”ta fada tana guada kai hadesake tabbatarwa kanta
”qwarai kuwa nene,nima na zargi haka tunda kinga fitarsu ana gobe za’a gudanar da aikin,cikinsu akwai wanda yake da hannu kan tsirar abdallah”inji zahariyya,shikam adnan ya kasa magana ta kanahi yake,tsanin ciwo yake masa kamar zai tsage gida biyu har
zumbur nene ta miqe tana fadin
”wallahi basu isa ba dukkansu,duk wanda yaci tuwo da ni miya yasha”

????????????????????????

Tana cikin kitchen tana qoqarin hada masu abincin rana ta jiyo hisham na qwalla mata kira,cike da mamaki ta ajjiye abinda take yi din ta fito don bata taba jin ya mata makamancin irin wanna kiran ba
tashin hankali ta gano qarara cikin idanunshi
”dauko duk abinda kika san kina da buqata ki sameni a mota na riga da na kai andallah ciki,babu lokacin bayani na miki shi a hanya”
bata tsaya tambayar ba kuwa,ta koma kitchen din a gurguje ta kashe gas din ta ahiga dakinsu da suka sauka ta dauki iya abinda take jin zata iya buqata ta fito ta taddasu cikin mota

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button