ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Tafiya yayi ta kusan mintina hamsin har suka fara barin ainihin qwaryar birnin kano sanna yayi parking a nutse ya dubeta
”maryam,na samu bayanan sirri daga daya daha cikin security din gidansu abdallah wanda nake biyanshi bayan barinmu yake samin ido kan duk wani motsi da yanayi da gidan ke ciki,don na tsammaci dama lallai wani abu na iya faruwa kan barinmu gidan da abdallah da mukaui,hasashena kuwa ya tabbata ya zama gaske iya,suna na ne ma farko cikin jerin mutanen da nene ke tuhuma,don ta saka amata bincike kan inda nake,yanzu haka mutanen na kan hanyarsu ta zuwa gidana,dalilin barowarmu gidan kenan”
kuka ne ya qwacewa maruam,wannan wace iriyar mace ce nene?me ta dauki rayuwar duniya,baza’a mutu ba?dawwama kowa zaiyi yana abinda yaga dama?,me take nema ne cikin duniyar da dukkanta bata kai qima da darajar fika fikin sauro ba agun Allah,wanne jin dadi ne a ginta ta kashe ran mumini wanda qimatsa tafi ka’aba agun Allah?,tana tsammanin idan ta aikata hakan taci bulus ne ko kuwa,zata taira daga hisabi da zabar Allah ne?dukkan amsar itace a’ah,babu
”a halin da muke ciki maryam kuka babu amfanin da zai mana,ki tsaida kukan mu nemi mafita”
tabbas maganar hisham haka take,ba bata lokaci ta ciro wayarta ta sake kiran mama wadda basu yi awa biyu da yin waya ba,magan sukayi ta kimanin minti talatin da ita kana ta kashe wayar ta dubi hisham kasancewar handsfree ta saka yaji komai
kansa ya gyada
”maganar mama gaskiya ce,kuma tsarin nata yayi,nima da mun isa gobe zan wuce katsina hometown namu”ya fada yana mai gamsuwa da bayanin maman yana kuma sawa motar key,ta juya ta sake kallon abdallah har yanzu idanunshi a lumshe yake,babu baki balle ya bayyana abinda ke cin ransa,ta tabbata ba magana daya ke dawainiya da zuciyar abdallah ba,suna da dama,koda bao jude idonsa ba,koda baiyi,magana ba tana ki a jikinta zuciyar abdallan a quntace take,takan tashi kokawa afili da boye duk da shi din tsananin jarumtarsa bai taba barinta taga hawayensa ba
Da taimakon bayanin da mama ke masu a waya suka kai ga isa qauyen NI’IMA dake cikin qauyen gaya,tun daga shigowarka garin zaka bawa kanka amsa,tabbas qauyen yaci sunanshi ni’ima,qauye ne da Allah ya wadata su da yawaitar korayen shuke shuke qoramu dabbobi da lullumi ma’ana rashin haske da zafin rana
duk da haka sai da sukayi tambaya kafin su kai ga isa ainihin gidan da suke nema,gaya garin kakanninta ne tana zuwa lokaci bayan lokaci saidai qauyen ni’ima din zata iya irga iya adadin zuwanta tunda bata da wani shaqiqin da zata zo gunsa face wannan tsoho qwaya daya da yake qanin kakanta
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[6:27pm, 9/22/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶4⃣5⃣
Mazan Allah S A W yace:ku umarci ‘ya’yanku da yin sallah suna da shekaru bakwai,sannan ku dakesu saboda ita idan suka kai shekaru goma,kuma ku rarraba musu gurin kwanciya(ma’ana ya zama gurin kwanan maza daban gurin kwanan matan daban yayin da suka cika shekaru goma)
Gida ne ginin qasa kamar yadda yake kasancewa ginin gidajen qauyuka,saidai wannan ya dan banbanta da nasu damin uasha shafe da ruwan makuba,hakanan ginin sumul sumul yake sakamakon fulastar kar qasa da aka yi masa da kuma makubar da akabi aka shafe ginin da ita.
Maryam ce ta fara shiga,kamar yadda muka sani yan uwanmu na karkara basa gini quntatacce hakan ce ta kasance ga wannan gida,babban tsakar gida ne mai girma wanda babu sumunti a qasan sa,turbaya ce saidai ta sha shara fes da ita,ga alamun shatin tsintsoya ne,daga can quryar katangar gidan garkene na dabbobi dake a tsaftace shima,sai rijiya daura da shi wanda lema ce duk a bakinta da tukwanen qasa da aka kikkife da alamu wanke wanke aka gama agun babu jimawa.
ta sake yin sallama kin shiru ba’a amsa ba karo na uku,cikin daya daga dakuna hudin dake jere taji muryar matashiya na amsa mata,ta fito sanye da roga da zani na atamfa wadan da suka danyi haske saboda dan jimawar da sukayi a duniya,maryam ta duba itama ta kalleta
”don Allah inna wuro fa?”maryam ta tambaha,sai ta juya ta kalli dakin kana ta kalli maryam
”tana ciki salla take amma yanzu zata….”’
”wake sallama ne mero,a shigo mana”
muryar inna wuro ta katsesu
”inna wuro baqi kikayi”
”kaddai ace su meramu ne har sun iso haka da wuri”ta fada tana yunqurin fitowa,kasancewar ta san zasu zo din mama ta kirata awaya ta mata bayanin zasu zo din ta wayar mustafa jikan gidan.
hannunta dauke da tabarmar kaba sabuwa dal ta fito,dattijuwa ce wadda aqiyasce zata doshi shekaru sittin,tsaf da ita cikin cikin atamfar itama da hijabi ruwan madara,fuskarta ta fadada da fara’ar ganin maryam din
”to kuma ya na ganki ke daya”itama murmushin ne afuskarta
”inna suna qofar gida”
”to yi maza kice musu su shigo daga ciki mana”ta fada yayin da take shimfida tabarmar.
Tare suka shigo hisham na tura abdallah kan wheelchair
”hukumullahu min zalika,Allah mai yadda yaso da bayinshi”inna wuro ta fada tama kallonsu
”sannu dam nan sannu”ta qara fada tana kuma gyarq musu gun zama
matashiyar da inna wuro ta kira da mero dazu ta qaraso dauke da kwanonsha cike da ruwan tulu mai sanyi fari tas ta ajjiye gabansu,kanq ta ja hijabinta daga kan igiya tana fadin
”inna zanje gida,idan na dawo r
yau to,idan kika ga ban dawo ba kuma sai gobe”
”to mero na gode Allah ya huta gajiya,ki gaida su azimin”
Bayan gaishe gaishe shiru,ne ya biyo baya inna tana kallon ikon Allah
”yanzu mairamu tun yaushe lalurar ta sameshi?”a nutse tayi mata bayani,kamq bqki innan tayi
”matsalar ku kenan mitanen binni,boko tasa baku da kulawa sam,ni kam ba wai zato ba amma wanna lalura ta yaron nan batayi kama da komai ba face sihiri,kuma kinsani sarai qanin kakanki masani ne kan irin wannna matsaloli baki tuntiba ba,yanzu ma zuwa kukayi kenan idan qura ta lafa ku koma ba neman magani ya kawoku ba”
hisham ya guara zqma jin hanyar waraka na shirin samuwa
”a’a inna,har maganin ma mun zo mu nemeshi”
shiru tayi ma wasu ‘yan mintina kana tace
”to Allah yasa adace,insha Allahu Allah zai kawo qarshen abun nan kusa”
maryam ta dubi inna wuron
”ina tsoho alhajin ne?”
”kinsan watan tafiya gabas ne,bana Allah ya kirashi yana can qasa mai tsarki,ina tsammanin yau duka kwananahi uku da tafiya,amma muna sa ran nan da sati uku zuwa hudu zasu dawo insha Allahu”
”Allah ya dawo da ahi lafiya”suka hada baki ita da hisham wajen fada
”daya dawo insha Allahu zan masa bayanin komai,idan rabo sai kuga ya warke”
”Allah yasa”inji hisham cike da fata.
In banda sannu babu abinda inna wuro kema abdallah,gaba daya tausayinshi ke damunta,irin wanna lalura mai fama da ita kadai yasan yanayin da yake ciki,da kanta ta bude musu wani daki can bangare daya,ba laifi dakin akwai girma,malale take da leda duk da cewa ba sabuwa bace,akwai labulaye a window da qofar,sai tsohuwar katifa da kujera qwaya daya,a ahare dakin yake fes kasancewar inna wuron bata lamuntar qazanta
hisham ya qarewa dakin kallo kana ya girgiza kai
”rayuwa mai juyi kuyi,Allah mai yadda yaso”ta karanci me yake nufi,tabbas ita kanta ta sani abdallah dan gata dan gayu,young millonier yafi qarcin zama cikin qauye ma baki daya ba dakin ba.



