ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

tuni har mero ta isa dakin ta bude wheel cahir din ta tsaya agaban katifar abdallahn tana kallonshi,shima idonshin na kanta,wani abu maryam taji ya taba ranta sai ta dauke kai ta qaras inda yake,gabanshi ta tsugunna
”inna wuro tace ko zaka fita waje can yafi iska mai dadi?”tana maganar ne idonta na kallon gefe ba inda yake ba,kai ya guada alamun to cikin zuciyarshi yana fadin
”Allah yama inna wuro albarka,ko banza ta samamin hanyar da yau zan wuni ina kallonki,ko ke ba zaki kalleni ba,’yar qauye kawai”.

sau uku tana qoqarin dagashi ta kasa,mero na tsaye ta dameta da maganar kaza zakiyi kinga haka zakiyi,ana hudun ne ta taho da sauri zata tayata kama shi
”me haka ne wai mero?lafiyanki?”madyam ta fada a dan zafafe,ita kanta batasan ta fada din ba sai daga bisani,sai ta waske da aon ci gaba da daga shi din,qarshe inna wuro ce ta taimaka mata suka dorashin ita ta turoshi mero da inna wuron sukayi gaba.

Da ido yake binsu hirar tasu na bashi sha’awa,zaya so ace yana da bakin da zai saka cikin hirar tasu,hakanan yaji jininshi ya hadu da inna wuro,tsohuwa ce mai karamci da dattako kamar maminshi duk da ta fita shekaru,weather din garin yaji yayi masa kamar a qasashen turai ba cikin qasar kano ba,kanon ma cikin wani qauye.

Murmushin da maryam ta ga yana tashi kadan kadan kan fuskarshi ya tabbatar mata yaji dadin zaman gun,hakan neya bawa mero damar matso da kujerarta ‘yar tsuguno daura da abdallah ,ta fara bashi labaran qauyen da waqoqinsu,al’a dunsu da kuma yanayin shagulgulansu inna wuro na sa musu baki jefi jefi,yadda maryam taga ya bada hankalinshi sosai kan meron sai taji baa wai,duk da tana ta qoqarin nutsar da zuciyarta kan meye nata?,Abdallah dama temporary ne jiran samun lafiyarshi kawai take ta kaucema rayuwarsa.

Saidai duk yadda taso nutsar da kanta hakanan taji hakan ya faskara,sai tayi zaton zama shirun da tayi ne saboda gaka ta miqe tana fadin
”inna wuro bani garin tuwon nan mana na tankade miki shi”
”kwano biyar ne fa meramu?ba zaki iya ba”
”ai inna babu abinda nake Allah zan iya ki bani kawai”
hakanna inna wuro ta bata din sai ta tafi can dan nesa da au kadan bakin rijiya ta zauna ta saka kujera ta tsuguno tana son kauda hankalinta daga garesu,duk da tana iya kallosu tana kuma jin abinda suke fada.

A sace yake kallinta,qarara ya karanto damuwa cikin zuciyarta saidai miskilancinta da wani dalilinta can maras tushe ya hanata gano me take ciki?me take so?mene kuma bata so,duk sanda ya fusknci zata dago kai ta kallesu sai ya dauke kanshi ya maida kan mero,ita kam mero farinciki ya cika zuciyarta kamar ta taahi taka rawa,tqu,balaraben nan ne yake ta kallonta,kai gaskiya tafi kowacce mace dake cikin qauyen ni’ima sa’ar zuwa duniya.

har aka kira sallar la’asar yana nan zaune yana sauraron hirar tasu yana kuma tayasu da murmushi,musamman idan akayi abun dariya,tankaden da ya kamata ace ta gamashi cikin qanqanin lokaci sai gashi zuwa lokacin la’asar din ko rabi bata yi ba,hakanan ta miqe ta karkade jikinta,ta maida saura cikin buhu wani kuma cikin fanteka ta rufe ta share gun
”ayiwa bawan Allah alwala ko?”inji inna wuro,mero ce ta miqe tana fadin
”sai nayi masa inna tunda maryamu na tankade”
”a’ah,ina aka taba haka mutum da matarsa ba wai bat nan bane,haramci ne ai,ki karbi tankaden ita tayi masa alwalar….af,tama kammala kinga,to bata butar”

haka nan taji tana jin haushin meron,ko da tazo miqa mata butar karba tayi ba tare da ta kalleta ba,abdallah ma kan whell chair dinshi yana kallinsu,murmushi ya aubuce masa kana ya duqar da kanshi yana jin wani sukuni da farinciki na ratsaahi wanda tunda ya kwanta cutar nan baiji irinshi ba sai yau,ya kuma rasa na meye,a gaggauce ta daura mishi alwala ta fuskantar da shi gabas ta bar gurin taje tayi tata,da suka idar ma hirar taau suka zo suka dora,madafa tayi tafiyarta wata rumface ta bunu dake gefe daya na tsakar gidan,anan din ma tana iya hangosu amma sai ta juya musu baya.

haka ta hana kanta sakat taqi zama gu daya har sai da ta kammala tuwon masarar miyar danyar kubewa,shi kuma abdallah ta dafa miahi couse couse da miyar ganye
anan din ma dai suka zauna don cin abincin dare,qemem yaqi couse couse din,tayi mamaki matuqa da taga yana cin tuwon masarar,shi da ko na semovita bai dameshi ba
”ato,dama ai tuwo shine abinci,a tsari na abincin gidan bahaushe ma ahekari aru aru ahine abincin dare ba wadannan abinciccikan yahudawan ba da basu qara mana komai face cututtuka”inji inna wuro ta fada har sai da tasa abdallah murmushi.

ido ya zuba mata ganin kowa ya kammala cin abincin ta tattara kwanukan ta wanke ta dawo ta zauna ba tare da ta sa komai cikinta ba,ta lura sarai da yadda yake kallonta don haka ta canza ma gin zama inda ba zasu iya hada ido ba
”abdullshi me kake kallo ne?,ko wani abun kake so?”inji mero ta fada
kai ya gyada,bayqn ya kalleta,sai ta sake washe haqora tana fadin
”to me kake so?”ya tsanshi ya nuna saitin maryam,sai ta bi yatsar da kallo har kn maryam
sai ta rage farashin fara’ar fuskarta kana tace
”maryamu magana ye dake ko?”ba tare data dubesu ba tana tsincewa inna wuro qulalai daga cikin audugar da take kadi,cikin salon dakiya da shariya tace
”magana ta me kenan?”
”nima ban sani ba”meramu ta fada tana komawa inda ta taso ta zauna,qarasowar inna wuro gun yasa suka ci gaba da hirarsu,haka ya qarqci kallonta har ya haqura.

inna wuro ce ta lura da yadda ya soma lumshe ido
”bawan Allah bacci ina tsammani yake ji”inji inna wuro
”kaishi daki maza meramu,idan zaki dawo kya dawo”ta fada tana janye daeon audugar daga gabanta,yana sane ya lumahe idon yaji dadi da inna wuro ta masa hanya.

da qyar ta samu dorashi kan katifar,ta janyo masa abun rufa kan ta gama lullubeshi ta tuna da ruwan ganyan magaryarta,taso idanunshi biyu yasha,amma duka da haka ta debo cikin tafukan hannunta ta shafa mishi dukka jikinshi,kana ta masa addu’o’in kwanciya barci ta shafa masa,wani sanyi da nutsuwa yaji suna ratsashi,kamar ta shafa masa ruwan qanqara,ta juya da nufin tashi sai taji an janyota,bata zata ba sabida haka kai tsaye jikinshi ta fada
”ka sake ni”take fada tana mutsu mutsu,saidai ko ajikinshi,bata son me yasa yake yawan son rungumarta ba haka
”haba ka sakeni nace mana,kayita taba jikin mutane haka kawai”
”jiki na ne,halaliyata,lada ma Allah zaya bani”haka yakeson fada amma ya gaza.

duk yada taso zame jikin nata ta gaza,tanaji tana gani har gajiya ta sauko mata bacci ya qwace idanunta,yan jin saukar numfashinta cikin nutsuwa,shi din ma idanun nasa a rufen auke sai kayi tsammani bacci yake,saidai sam ko daya,tunanin maryam dinne cike fal da kwanyarsa,yana tausayinta,yana jin sonta har cikin jini tsoka da bargonsa fiye da da,sai yanzu yake sake tabbatarwa kanshi Alah ne kawai ya bashi maryam din ba mutum dukiya ko qarfin iko ba,maryam din kadarace mai tsada kai tama shallake kadara agunsa,samun mace mai halacci da juriya kan lalura da halayen mijinta abune mai,matuqar wuta a wananan zamanin namu,ya sani sarai bata zaman qauye iyakacinta da ahi ziyara ta kwanaki uku,sai gashi yau ta amince ta yarda ta zauna cikinsa shi da ita cikin zuriyarta har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya ba tare da damuwa raki ko qorafi ba,lokacin da dukkansu shi da ita basu san sanda zaizo ba don babu wanda ya san iya tsahonsa,baya ga dama da take da shi na tafiyarta ta barshi tunda babu zuri’a ko iddarsa akanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button