ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ya dinga tina yininsu shi da ita na yau,murmushi ya subuce masa,fushi da kishi daya dinga ganowa qarara cikin qwayar idanunta,saidai ita sam bata san da su ba,batasan suna bayyanar da kansu bane su duk yadda kakai ga qoqarin boyesu,murmushi ya subuce masa,ya sanya hannunshi ya cire dan hijabin dake maqale a wuyanta,ya sake zare ribbom din kanta ya sa hannunshi yana shafa gashin,santsinsa da qamshinsa na burgeta,yayi imani abinda yake ji game da maryam din wani irin jini a jiki da ba kowa Allah yake bawa ba.

Ta sake zubawa qofar dakin ido a karo na barkatai,mintina kusan goma ta sake janye tagumin da tayi ta saki ajiyar zuciya ta kalli inna wuro da ta duqufa wajen yin kadinta
”kinga inna meramu shiru bata dawo ba”
”eh…..wata qila itama baccin yayi awon gaba da ita ne,ai yau kam ta aikatu itama,meramu babu son jiki,harvta fiki son aiki”innan ta fada cikin halin ko in kula don bata kawo komai cikin ranta ba
”amma inna bacci da wuri haka,qarfe tara da rabi fa,yanzu ma wasu suke fita dandali”
”yo su mutan birni barci da wuri a gunau wani abu ne?,rayuwa suke gida a qulle,daga sallar isha idan suka shige gidajensu suka kulle sai kuma washegari”
”q’nn,bari na tashi nima na tafi”
”da wuri haka?”inna wuro ta fada tana binta da kallo
”eh”ta bata amsa gana zira sudaddun silifas dinta
”to kinga ga abincin nan kokus yake kome ne?,tafi da shi gida kwaci”duk yadda take kwadayin couse couse rin sanda ake dafashi take fata ya shigo farantinta amma a yanzu sai taji duk ya sure mata,a salube ta dauki kwanon tana fadin
”an gode sai da safe”
”Allah ya bamu alkahairi”inji inna wuron
bata haqura ba sai da ta je bakin qofar dakin tace
”abdullahi da meramu sai da safe”sau uku tana maimaitawa taji shiru,abdallah na jinta amma maryam batasan ma me ake ba don ta jima cikin daddadar duniyar barci ta musamman.

inna wuro ta dubeta
”na gaya miki sunyi bacci,kije kwa hadu da safen,ki gaida su hansai”jiki ba qwari ta fice daga gidan
ko a gida tana kallo qannanta na damben cin couse couse couse din amma ta kasa ci sai ido kawai data zuba musu tana kallonsu,sau uku babarta iya hansai na mata tayin taci bakinta cike da shi taqi cewa komai,qarshe ma tashi tayi ta shige dan takurarren dakinta wanda zakayi tsammanin duk ranar da aka samu ruwan sama mai yawa zai iya ruftowa mazauna ciki.

kasa bacci tayi,yau kam ta kai maqura,jin son Abdallan take kamar ta mutu kota haukace,ita kam ko a haka ma zata iya aurenshi,amma idan ta dubeshi ta dubi kanta sai jinta yayi sanyi qalau,tasan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,duk da batasan waye ainihin abdallah ba,amma kallo daya da ta masa ta san cewa ba qaramin mutum bane shi da maryam din ma baki daya
tunanin da ya isheta qarshe kuka ta fashe da shi a haka bacci yayi awon gaba da ita tana Allah Allah gari ya waye ta koma gidan inna wuro.

????????????????????????

Kamar yadda suka amida shi al’adarsu bayan sallar la’asar su zauna hira har salllar magariba wani lokaci har isha’a yanzu ma hakane.

yana zaune kan whell chair wanda yau ita da mustafa suka dorashi don ya dawo daga gona da wuri,ta karbi dan qaramin alqur’anin da ya gama karatu da ahi daga hannunshi ta ajjiyeshi a muhallinsa,ta dauko roban da take ajjiye duwan ganyan magaryar,wanda ta karanta a yoyin dake cikin surutul A’araf aya ta 117 zuwa ta 122
sai ta cikin suratul yunus aya ta 79 zuwa ta 81
sai cikin suratu Daha aya ta 65 zuwa ta 70
ayatul kursiyyu falaq da nasi da iklas duka,tana shirin tsiyayowa taji sallamar mero wadda ta fita dazun tace zata je tayi wanka,idan da savbo maryam ta saba,da safe zata zo da kwalliyarta,idan ta gama wuninta qarfe uku zata koma gida ta sake wanka da kwalliyarsu irin ta mutan qauye.

a cup ta tsiyayo ta miqo masa,sai ya dan bata rai,saboda dandanon magaryar da baiso,itama kicin kicin tayi,musamman da ta jiyo tana tambayar inna wuro ina suke basu fito ba,tasan kadan daga aikinta ta fado musu,taji dadi da inna wuron ta ce mata
”zauna anan ki tsinke zogalen nan kada meramu ta fito ta hau aikin,sonke kwana biyu naga gun hira kika fi kauri,duka kin sakar mata ragamar aikin,kullum ita ke ruwon dare ta barki da lugudar lebe”.

Dariya ta bashi cikin ranshi ganin yadda tayi wani kicin kicin
”lallai ma yarinya,wuyanki ya isa yanka,ni zaki wani budewa ido kamar qaninki,Allah ya bani lafiya zaki gane shayi ruwa ne”hakanan ya karba yayi bismillah cikin ranshi yasha donshi kansa yana jin dadin sa,wani lokacin don ya tsokaneta yake qin karba,don ya lura indai yanason ganin fushi da bacin ranta yaqi karba yasha ya kuma zauna sauraren labaran mero

ta bude wata ‘yar roba mai kama data naseline,saidai ba shi bane ciki,man zaitun ne da na habbatussaudah wanda ta karantawa ayoyin da suka wuce a baya ta qara da ayatushshifa ta tofa aciki ya zama na man shafawarsa ta miqa masa don tana jin kunyar shafa masa,nan ma sai da ya gama shan qamahinsa ya amsa ya shafa ta maidashi inda yake.

komawa tayi ta zauna kamar ba fitar zasuyi ba,ya zuba mata ido yana son ganin iya gudun ruwanta saidai qememe tayi taqi kallonshi ta fara karanta azkar dinta na maraice,ta kammal ata shiga wasu sabgogin abinta,don har cikin ranta bata jin fitar,sai data qara kusan awa guda sannan ta miqe ta iso inda yake,ido suka hada sai taga ya dan harareta,dariya ma yaso bata amma sai ta dake ta tura whellchair din a tausashe suka fito.

tana kan tabarmar kabar da suka saba zama qasan bishiyar dalbejiyar,tasha daobta daidai da irin nasu baki cike da kan ta kile,koriyar atamfa ce jikinta shar wadda hatta da zanan jikinta yanzun da zaka bawa maryam ta zana maka tsab zata zanashi saboda tsabar sawar da meron keyi yau da gobe don bata da kamarta duk cikin kayanta,gaba dayanta qofar dakin take kallo,gyaran zogalen da aka batan ma ko rabi bata yi ba,inna wuro batasan me ke gudana ba don yau tayi riga malam masallaci ta shiga ta hura wutar tuwon da kanta don kada maryam ta karba yadda ta saba su ta barsu da shan inuwar qasan bishiya,sai da ta kalli gidan ko ina tsaf ya sha shara sai qamshin qasa yake kamar kullum kana ta juya abdallah can bayan mero yadda ba zata iya ganin fuskarshi ba saidai idan juyowa zatayi,ai kam kamad an tsikareta ta juyo din tana fadin
”nayi zaton yau ba zaku fito ba ai,har na fidda tsammani Allah”.

kai kawai ya girgiza yana dan qaramin murmushi wanda idan yayi meron kejin duk duniya fa ita an gama biyanta,kallon murmushin take da matuqar qima don bata taba ganin wani cikin samarin garin da idan yayi murmushi yake qawatashi ya masa kyau kwatankwacin haka ba.

yau kam innan ta zaunar da ita cikinsu babu batun zuwa kitchen wato rumfar girki,taqi kallo kosa baki ko sau daya cikin hirarsu,ranta take ji yana mata suya,kamar ta kori mero amma sai taga meye nata a cik,bata da wannan hurumin,ita kanta batasan me yake jefata damuwa mai yawa kan lamadin meron ba da abdallah,ita da ya kamata ta zama ‘yar abi yarima asha kida cikin sabgar.

Dakinsu ta koma ta dora doguwar riga kan dinkin atamfa riga da skert dake jikinta,cikin kitchen ta samu inna wuro
”inna naga kuna kusa da rafo,zan qarasa da abdallah can yaga garin naku”
”to Allah ya kiyaye sai kun dawo”
bata kalli mero ba bare tace mata wani abu ta fara tura whell chair din abdallah,ya waiwayo suka hada ido sai ta dauke idonta
”ina zaki meramu?”mero ta fada tana miqewa da sauri tare da zura takalmanta ta biyo bayanta,inna dake kitchen ce ta amsa mata
”zasu rafin malam dogo na bayanmun nan”
”ai da ni za’a,dama ina son in gaya muku idan kuna son zuwa,girin na da kyau aradu”ta fada tana bin bayan maryam
”um hmmm”kawai tace da ita tana ci gaba da tura abdallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button