ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

sai da ya kammala ya bubbuga qofan bandakin tazo ta fidda shi,tana ta rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta shigo idanunta a qasa taqi yarda su hada idanu,itakam rashin kunyar shi ta fara isarta,daga warkewarsa jiya zuwa yau ya addabeta gaba daya ya hanata sukuni,ina dalili,yana abu kamar su biyu ne kadai cikin gidan.
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[7:29pm, 9/25/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
4⃣8⃣
Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku
mala’iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur’ani a cikinsa
A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar
”kun dawo kenan mer…..”’sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji
”Allah qaadiran ala mai yasha’u,bawan Allah?”ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu.
murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana
”babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min”
kiran sallar magariba ya katse su
”inna muyi sallah tukun”ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci
”gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi”inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta
”haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala”
”to inna”ta fada cikin rawar murya
tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta.
Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi.
Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta
”nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai”mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa.
sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al’qur’ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur’ani ya shafa addu’anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba.
”madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana”ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar.
Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata
”ka sakemin hannu kaga duk ka…..”
”bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hira?”
ta sake kau da kanta kana tace
”to me kake so muce ko ince maka ne?”
”bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya furta kina cutar da zuciyarki hakanan babu gaira babu dalili ba tare da ta yi miki laifin komai ba”
kamar wadda ya doka sai ta soma hawaye,ita kanta batasan me yake saurin karya mata zuciya ba
”subhanallah,kuka…kuka kuma maryam me na miki”babu amsa don haka ya janyota ta fada jikinshi ragowar ruwan ya zube mata ya jiqa mata gaban dan yalolon hijabin jikinta wanda takansa duk dare idan zata kwanta,dama ba wani kauri gareahi ba,yauqi ne da shi da rashin kauri take kuwa ya manne mata a jiki.
”yi shiru ki gayan matsalarki,bazanso saki kuka ba maryam cikin irin wannan lokacin,baki cancanci haka ba”
”ka sakeni ni babu abinda ke damuna,ka qyaleni”
kai ya girgiza hakanan mutum,bazai yita kuka ba komai na da dalili”
ta tabbatar indai abdallah ne bazai saketa din ba don ya mata riqon tsauri ne don haka tace
”kayana,ka jiqamin kayana ka sakeni na canza wasu”
idanunshi ya kai kan gaban jijabin nata cikin hasken torch din wayarshin,wani abu ya tairga mishi har qasan qafarshi,ya kai,hannunshi gaban hijabin yana fadin
”bari na cire miki”
kan tayi qoqarin hanashi har yaje,gaba dayansu wuta ta dauke musu shi da itan gaba daya,sai ta sakar masa wani kikan harda dan sauti
”am so sorry my dear”kawai yake fada ya cire hijabin ya cillar gefe daya ya sake mannata kan qirjinsa,yana kin sautin kukanta bai hana ta ba don yasan koma mene idan tayi kuka sosai zuciyarta zata sassauta,tun sautin na fita kadan kadan har ta koma ajiyar zuciya kana numfashinta ya fara sauka a hankali alamun bacci yayi awon gaba da ita.
murmushi ya saka mai qayatarwa qasa qasa yace bayan ya leqa fuskarta
”rigimammiya,kin hana zuciyarki sakat”yana gyara mata kwanciya,ya fuskanci duk ranar da ta kwanta a qirjinshi bata dadewa bacci ke daukanta wani lokacin ma har taso makara gun tashi,ya saki ajiyar zuciya qasa qasa yace
”u dont know how u make me feel duk sanda kike jikina”ya dora kanshi saman habarta cike da wata iriyar nutsuwa.
????????????????????????
A shirye take cikin riga da wando na pakistan ruwan madara tayi rolling da mayafinsu,zaune take kan kujera ko motsi batayi kanta a duqe tana kallon yatsuntsa,ya sake dubanta tini har ta fara zub da qwallar tata abinda bai son gani
”kina son fita amma kinqi ki gyara ni,nikam yau babu wanda zaimin wanka idan bake ba,see you ko tausayina baki ji,kin gwammace mustafa yayi ta yimin bayan bako ina yake wanke min ba wani gun ni nake da kaina”
maryam cikin muryar kuka ba tare da ta dago ba
”taya zan wuce bandaki ni da kai yi maka wanka inna wuro na kallon mu,haba mana abdal….”
”fine,muyi zamanmu ko baby na ni dake yau cikin daki,babu mai cewa don me ko”qara narkewa tayi tana faman hawaye don tana jiyo muryar inna wuro na jajjabin rashin jin motsin daya daga cikinsu,duk da tasan kara da alkunya bazata bar inna wuron tayi magana ba ko zasu shekara cikin dakin.