ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Narkewa yayi shima cikin filallukan dake kan whellchair dinshi dariya na cinshi,ya sani cewa ba zata taba iyawa ba,ko kaya na shan iska bata yarda ta gani jikinsa kuma duka ua gama karantota,ta daukeshi kamar wani muharraminta
sallama mairo tayi tana daga labulen dakin
”yaya abdullahi muna ta cigiyarku shiru?”ta fada tana kallonashi tana kuma kallon maryam
girarshi ya dage guda daya
”eh,muma muna ta cigiyarku,daman ke nake jira ki taimaka min inyi wanka,yau meramu ta gaji”ya ambaci sunan ta irin salon da yaji suna fada
zuciyar mero qal ta rufe fuskarta da tafukan hannunta,da sauri maryam ta dago babu shiri ta dubi abdallah qirjinta ya buga kamar an dakeshi da guduma,ido daya ya kashe mata kana ya dauke kanshi ya maida kan mero wadda take fadin
”kai yaya abdullahi”cikin salon nuna jin kunya.
kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi hanyar fita da shi,sai data bude idon nata raga dakin wayam har sun fice,jiki ba qwari jtama ta fice a dakin
inna wuro bata a tsakar gidan don haka tayi maza ta tura suka shige bayan gidan
”take it easy mana madam,kada ki fadar da bawan Allah”inji abdallah cike da dariyar mugunta da yake qunsheta
tana tsaye ya soma cire kayanshi ta dauke kanta qirjinta na lugude,saura gajeran wandon daya rage wanda yake bari a jikinsa idan zaiyi wanka,gaba daya ta rude don bata yarda taga jikinshi har kamar haka,hatta da cinyoyinshi dake cike da gargasa sun fito,ganin yana niyyar fidda shi shima yasa ta qarasa rudewar gaba daya,batasan ta dafe hannunshi ba
”ayya mana abdallah ba kyau fa don Allah”ta fada cikin son fashewa da kuka
dariya sosai ta kamshi amma ya hade rai yayi kicin kicin
”to me naki,dazun fa adaki kika gayan babu ruwan wani da wani,kema me ruwanki da ni ko na cire din,ba wanka zaki tayani ba?,kimin wankanki kawai ki maida ni daki,wai haka ma ake jinyar mutum?,oh ni abdallah sam baki iya jinya ba”ba bakin maida amsa girgiza kai tayi yaci gaba da kiciniyarshi,a guje ta kwasa ta fice a bayin dariyar da yake boyewa tilas ta fito,mamaki take bashi tamkar cikin qauyen aka haifeta ko kuma shi din ba mijinta bane,kunyarta ta mata yawa ta maida shi kamar wani dodo,Allah yasa komai na wanka na gabanshi don haka ya qyaleta yayi abunshi tunda hannunshi na kaiwa.
sai da ya kammala ya bubbuga qofan bandakin tazo ta fidda shi,tana ta rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta shigo idanunta a qasa taqi yarda su hada idanu,itakam rashin kunyar shi ta fara isarta,daga warkewarsa jiya zuwa yau ya addabeta gaba daya ya hanata sukuni,ina dalili,yana abu kamar su biyu ne kadai cikin gidan.
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[2:36pm, 9/27/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶4⃣9⃣
GA WASU FA’IDOJI????????
daga bakin mai gaskiya abun gasgatawa assaadiq al masduq Annabi Muhammad S A W yace”abinda yake zama hijabi tsakanin al’aurar dan adam da idon shaidanu fadin wannan addu’ar yayin da zaka cire tufarka BISMILLAHILLAZI LA ILAHA ILLA HUWA”
don samun kariya yayin yin baccinka,bayan ka kammla dukkan addu’ar baccin da annabin rahama ya koyar,ki karanta wadan nan ayoyin suma ki tofa musamman ga ‘yan mata da suke fama da jinnul aashiq wato aljanin dare
1⃣ katamallahu ala qulubihim wa’ala sam’ihim wa ala absaarihim gishawah,ealahum azabun alim
2⃣ waja’alna min bani aydihim saddan wamin khalfihim saddan fa agshaynahum fahum la yubsirun
3⃣ wa’iza qara’atal qur’ana ja’alna bainaka wa bainal lazina la yu’u minuna bil aakhirati hijaban mastura,wa iza zakarta rabbuka bil qur’ani wahdahu wallau ala adbarihim nufura
Hira suke kamar kowanne dare zaune warqashin rumfar qofar dakin inna wuro,dukkansu sauraron inna wuron suke su ukun tana basu labarin yanayin zaman aure a shekarun baya can da suka shude
ita kam maryam fadi take taga ta kanta,ta sani sarai da biyu inna wuro ta tsiro da wannan tarihin,tana ankare da abdallah yana satar kallonta,da sun hada ido kuma ya dauke kai sai ka rantse ba kallonta yake ba.
wata yarinyarce tayi sallama ta shigo gidan,inna wuro ta kalli yarinyar lokacin da ta duqa tana gaidata
”lpy qalau indo,ya mutan gidan”
”suna nan lpy suna gaisheku”ta juya ta kalli abdallah da maryam ta gaidasu kana ta kalli mero dake qoqarin miqewa tana fadin
”amma indo yaushe kuka dawo daga kanon,gaskiya birni ta karbeki kinga yadda kika canza kika zama ‘yar gayu kuwa?”.
Abdallah da maryam suka dubeta dukkansu dariya ce taso kamasu ita marysm cikin zuciyar ta ne,ina wani gayu anan,amma ita mero ganin wayewarta take a haka,abdallah kuwa sai da murmushi ya bayyana a fuskarshi yana duban yarinyar da ake batun wai ta canza din ta waye,idanun maryam yakai kansa,sai taji wani abu ya tokareta,ga zatonta su meron yakewa murmushi,ta janye idanunta a hankali tana gargadin zuciyarta.
Kama hannun indo mero tayi tana fadin ”muje waje indo”
”dan dalin fa?labaran yace tunda na tafi bai sake ganinki a dandali ba,yanzu ma shi ya aikoni na kai masa ke”bata amsa mata ba sai figar hannun indon da tayi suka fice,ci gaba sukayi da hurar wadda kusan inna wuro da abdallah ne jigon.
Kwanukan maryam ta kwashe ta kai cikin tukunyar tuwon da aka cikata da ruwa don inna wuro tuni ta hanata wanke wanken dare
ta tattare gun ta nufi soron inda suke ajjiye abun shararsu don ta zubar,soron babu haske don wearing din solar da kayi banda nan don haka bata iya ganinsu sosai,saidai tana ganin tsaiwatsu daga can qofar ficewa a gidan baki daya,muryar indo ta fara ji
”yanzu ke mero idan banda tsaurin ido inake ina wannan balaraben tsabar daukowa kai masifa da kuma jan abinda yafi qarfinka,ins laifin ma ki tsayawa labaran dinki,tunfa kina mitsitsiyarki yake sonki kuma an bashi ke,rashin kudin kayan daki ne ya hana auranku amma da tuni yanzu ai kina da yara”
”babu jan masifa,wallahi indo kada ki dauka wasa nake,da gaske sonsa nake wallahi tun ranar da na fara ganinsa,inason abdullahi sosai wallahi”
”tab,to kuwa kin debo da zafi,daidai ruwa fa daidai qurji,wai shin wannan ‘yar indiyar ta gefensa ba matarsa bace,idan kuwa hakane to inake ina hada kai da ita,aradu baki fice irin aikinsu da ake kai musubirni ba,ta gurin gashi ne kawai zaku goga da ita amma ta wuceki mero,kiyi haquri kada ki wahal da kanki”.
tsaki mero ta ja
”bafulata ce kamar ni shima haka,yo to ni ina ruwana da matarsama indai shi yana sona ai shikenan,kuma ni ban taba ganin ma ta,nuna,wani abu ba sai rashin fara’a da take da ita kuma wannan halinta ne,ke koma mebe ita ta jiyo,nidai ina son abdullahi kuma bazan fasa……”
jin taku ya sanya mero yin shiru suka waiwaya da sauri,sai sukayo tairu tauru,maryam ce ke takowa inda suke ta qarasa gaban sharar tayo bismillah ta zuba kana ta juya ba tare da tace musu komai ba,zucoyarta ke mata wani irin suya,duk da qoqarin kwantarwa da kanta hankali da take kan ba son abdallah take ba don me to zata ji zafi don wata tace tana sonshi.