ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

bin maryam suka yi da ido har ta shige cikin gidan,suka dawo da idonsu kan junansu suka kalli juna,indo yace cikin zare ido
”kinga irinta ko?yanzu gashi ta ji”cikin son nuna dakiya mero tace
”to baki ga babu abinda ta yi ba,na gaya miki ita fa babu ruwanta”harararta indo tayi
”ashe dai baki da kai mero har yanzu,wace ce zata ce bata kishin mijinta,kina kallon yadda kullum sai anje gudan mai gari rabon fadan kishiyoyi kamar zasu hallaka junansu,bakisan halin irin wadannan matan birnin bane,qila wallahi qyaleki tayi ranar da ta tashi saka ki a maqata babu mai fitar dake,ko kin manta yadda akayi da jummai ita da lantana kan mijinta?”tuno abinda ya faru din ya ruda mero tace
”wallahi hakane fa,ni ai na manta”kama hannun indon tayi qam qam tana kallon cikin gidan
”wallahi bazan koma ba ma cikin gidan,zo mu tafi”ta figeta suka fice gabanta na faduwa saboda tsoron abinda ya faru da lantana kada ya faru da ita,don a yanzun tana nan tana fama da ido daya wanda jummai ta tsiyayar mata.
????????????????????????
Tunda nene ta yiwa malam na hayi maganar su gizago yace ta kwantar da hankalinta,ta riga ai da ta sani fada da aljani babu dadi,cikin kwana daya ya masa ‘yan surkullensa ya rufe bakinsa bai kuwa sake dawo musu.
dukkansu suka qarewa dakin qwaya daya kallo mai azabar girma wanda aka ginashi da laka da ciyawa irin ginin qauye sosai,dukka suka dubi malam na hayi dake tsaye burgijaja cikin babbar riga da ta wadatu da maqale maqale na kayan sihiri,fuskarnam cike da suma ha hana qarya wanda yayi fiqi fiqi kamar yana barazanar tsone idon daya daga cikinsu,turo baki zahariyya tayi
”gaskiya malam nidai wanan abu yayi min tsauri,ina laifin ma asama min gida mai dan kyau ba wanann kwangon ba cikin wadancan kucakan mutanen da ake kira da mata,daga su har yaransu ni basa min,maraba da dabbobi don wallahi gwara na zauna da karnuka,da in zauna da su”ta qare maganar tana jan tsaki.
malam na hayi ya qara farashin muzuran da yake yi
”su mata na ne ke kuwa ba matata bace,matar aljani zulan anfaini ce,saboda haka babu ruwanki da wani cikin gidan nan,shi kuwa aljani ina ruwansa da wani kyawun giri,kwata kwata ke din ma ba zaki wuce wata biyu ba zakiyi naki gu,idan kuma zaman din din din kike so kuyi to sai a gaya masa,ya dauko miki gida daga dubai yazo ya ajjiye miki cikin gidan nan ki zabi wanda kike so ya maida sauran,ko kuma ya mayar da ke can bangon duniya kuyi zamanku daga ke sai shi”ido ta zaro tana ja da baya
”a’ah,ni bance ba malam kada ka jawomin salalan tsiya”
”ato,shine nima na gani ai”ya fada yana murza hana qaruarsa cikin zuciyarsa cike fal da sha’awarta,musamman idan ya dubi shigar da tayi sai yaji kamar ya janyota ya fara sha’aninsa a lokacin,zuciyarsa ke kwabarsa yabi a hankali,kada kwabarsa tayi ruwa tunda dai nan da jibi komai zai qare.
Cikin sigar lallashi nene tace
”yo banda abun zahariyya ma kwana nawa anyi an gama,ai dama bayan wuya sai dadi”
caraf adnan ya karbe zancen yana yarfa hannuwa
”ehenn,shine fa,to ni Allah na tuba ko kuttu aka ce na shiga na zauna ba shiga zanyi ba,daga fa ‘ya’yan bankin sunzo fa sai yadda kaga damar yi”,hara ra zahariyya ta balla masa
”kaga idan ana zance fa ka daina sako kanka,gwara ma macen da kai”har zai hayyaqo,mata nene ta dakatar da shi don dukkansu biyayya suke mata yanzun lallaba ta suke.
????????????????????????
kwana uku tsakani nenen da adnan suka rako zahariyyan gidan malam na hayi a matsayin amaryar aljani zul anfaini,babu abinda aka saka dakin face leda da katifa sai wasu qattin labulaye masu azabar nauyi da kauri wanda malam din ne ya saku su suma a dakin suka tadda shi,wai na aljani zul anfaini ne tanan zai dinga zywa gareta,buta ce kawai sai botikin wanka sai kayan sawarta akwati biyu.
sanda zasu koma ji ta dinga yi kamar ta bisu musamman da ta rakasu qofar gidan taga motarsu ta tashi bayan malam na hayi ya danqa muau ‘yan dubu dubu sababbi qar na naira dubu dari uku kudin sadakin zahariyyar inji aljani zul’ainaini,ta dinga binsu da kallo suna keta duhin masara har suka bace mata,ajiyar zuciya ta saki tana jin ba dadi amma data tuna nan da wata biyi komai ya daidaita ta zama wata abar kwatance cikin alumma sai taji hankalinta ya kwanta ta juya cike da qwarin gwiwa ta koma cikin gidan.
gida ne tafkeke mai azabar girma kada ma tsakar gidan nasu yaji labari,ko ina ahimfide yake da jar qasa jazur da ita kuwa,gefe fuda bandakinsu yake mai gajeriyar katanga wadda idan kayi wani wawan tsallen ana iya hangoka,babu mamaki don ita kanta katangar gidan ma tsaf wani dogon mutum din zai kamata ya tsallaketa ba tare da ya taka komai ba,gidan tsakiyar gonaki yake,babu wani gida nan kusa da su su kadaine a gun sai dan gaba kadan bukkar da malam na hayi yake dab da wani rafi hakn ne ma yasa ake ce masa malam na hayi don sai ka hau kwale kwale sanna zaka tsallaka dan qaramin qauyen dake maqotansu inda nan din akwai mutane babu laifi.
dakuna ne rututu a jejjere kuma durqusasau kusan babu dakin,ma da ya kai nata kyua cikinsu sai qwaya daya na malam din dake can gefe guda wanda idan ka kalli dakin shi kadai sai ka dauka ba cikin gidan yake ba,gini ne sosai na zamani don hatta da bangon dakin da yar qaramar baranda da aka yi masa duka tiles ne manne da shi,alatu sosai aka zuba ciki duk da bata ganin ainijin cikin dakin amma kallo daya zaka masa daga waje ka gane hakan.
qofar bandakinsu kaca kaca da qasa da dagwalo sauran kadan ta aheqa amai tayi saurin dauke kanta,yara ne guyin guyin da mata gami da yammata gasunan ko ina tsakar gidan tamkar gidan marayu,kallo suke ta binta da shi kamar mayu manyansu da qana nanau,gefe guda kuwa yara ne zaune cincirondo guda dukakkansu babu mai tufar arziqi dan kamfai ne kawai a jikinsu daidaiku ne masu riga ‘yar shar hanci kaca kaca da majina sun zuba mata idanu suna kallonta,daya daga cikin yaran ya taso daga cikin cabalbalin da suke wasa ya sheqo a guje yana mata dariya ya kama gefan rigar material din dake jikinta ruwanmadara take kuwa shatin hannunshi suka fito taya taya,batayi wata wata ba ta tsinkeshi da mari sai ga yaron a qasa warwas ya zube,da gudu wata mace cikin matan dake kallonta ta taho,hannu tasa ta dauke yaran ta janye shi gefe ba tare da tace komai ba,tayi tsammanin jin ihun kuka daga gin yaron saidai ga mamakinta ko uhm baice ba saima miqewa da yayi ya koma gun wasansa,kanta tsaye ta shige dakinta cikin bacin ran kayan da ya bata mata.
tun magariba malam na hayi ya shogo ya gaya mata dokokin zaman aure da aljani zul anfaini,dole dakinta ya dinga kasancewa cikin duhu ana yin sallar magariba har garin Allah ya waye,hakanan duk abinda zata gani kada ta sake tace zatq yi magana ko tambaya a kai idan ba haka ba matsala zata biyo baya da haka ya mata sallama yace ya tafi gun iyalinshi.
wajejan sha daya na dare tana kwance cike da,azabar zafi dq sauro,ga matsanancin duhun da ya mamaye dakin,taja tsaki yafi cikin carbi,addu’a take cikin zuciyarta na bacci yazo ya dauketa kota huta,ta saba kwana cikin hasken qwai da sanyin raba kan tattausan gadonta ta lulluba cikin lafiyayuen bargo,yau sai gata cikin wani irin qadagirin daki,ko qauyensu mahaifinta basu taba marmarin zuwa ba sabida sam bata hada hanya ma da maras shi sai gata yau zata kwana cikin wani daji tsakiyar gonaki”kai neman kudi da wuya yake”ta fada cikin zuciyarta,cikin sa’a kuwa baccin yazo yayi awan gaba da ita.



