ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Saidai ko cikakkiyar awa bata yi da fara baccin ba taji wani irin wari mai gigitarwa na ahirin tsaida fitar numfashinta,a rude ta farka daga baccin saidai nata iya ganin koda tafin hannunta saboda tsananin duhun dakin,tayi yunqurin tashi ta kasa saboda wani uban nauyi da taji samanta tare da wani irin nishi da gurnani,ta riga ta saddaqad aljani,zul anfaini ne ya iso saboda haka bata da wani saufan qarfi na qwatar kanta,haka ta koma ta kwanta daidai.

Tasha azabar da bata taba zaton shan irinta,duk da ba budurci gareta ba amma ko ranar da ta bada budurcinta wa saurayinta bata ji kalar wannnan azabar ba,tun tana ganewa har ta fita hayyacinta,bata farka ba saida hayaniya da haaken rana suka cika idonta
a hankali ta dinga bude idonta,haihuwar uwarta haka ta tsinci kanta,da qyar ta samu ta jawo rigarta ta zura,tun a yau ta fara dana sanin auren aljani zul anfaini,ta jima zaune tana tunanin me ya kamata ma tayi,idanunta suka sauka kan wata baqar leda,maiqon da taga tana yi ya sanyar janyota,kaza ce gasashahiya ciki,ture ledar tayi don bata ko burgeta ba,ganin babu sarki sai Allah donko dan tsakin gidan bata ga ya leqota ba ya sanyata miqewa din ta nemi,bandaki,don hatta da jikinta irin doyin jiya da daddare taji yana yi.

Ta fita kanta tsaye tana dingisawa,tun daga nesa ta hango dogon layi babu babba babu uaro kowa yabi,qofar bandakin suke fuskanta kowannansu da botiki wasu da qwarya wasu da kwatanniya cike da ruwa,bata damu ba ta durfafi qofar bandakin tana da niyyar shigewa,ji tayi an fincikota baya cikin wata iriyar dakakkiyar murya
”ina zakije?”waiwayowa tayi don ganin wanda ya mata wannan cin kashin,mace ce saidai idan baka lura da kyau ba zaka iya kiranta da namiji,a murde take,hakanna a tsaye take qyam,idan banda qirjinta da qudundunanniyar sumar kanta babu abinda zai nuna maka cewa ita maca ce,ba shiri ta hadiye tsiwarta da ta qunso ta sanyaya muryarta don ta fuskanci a banza matar zata dakata
”bandaki zan shiga”wata iriyar ashar da duk duniyancin zahariyya bata taba jin irinsa ba matar ta qundumo kana ta dora
”dan uwarku duka wadan nan da kika gani a gun ba mutane bane,duba har da yaran da,basu wuce shekara biyar ba kowa sai yabi layi,saike wata gundumemiyarki da ke zaki wani taho gandan gandan wai ke zaki shiga bandaki,to sai ki shiga mu gani”inji matar tana muzurai.

Ran zahariyya ya baci,tana ganin kamar ita za’a yiwa haka,tsaki ta ja kana ta juya karo na biyu da niyyar shiga bandakin,bata kai qa ida nufinta ba taji an fincikota an watsar take ta samu masauki cikin tabo da dagwalin dake kwance gaban bandakin,cikin tashin hankali ta dago don ganin wanda ya mata wanann danyan aikin
wata figigiyar matashiyace wadda gaba daya jikinta idan banda fata da jijiya babu komai,sai uban qashi a fuska,kallo daya zaka mata ka tabbatar cewa yunwa ta samu gindin zama a jikinta,tsoro da kunya suka hanata cewa komai haka ta miqe tsamo tsamo ta koma dakinta,dariya taji sun rude da ita muryoyi daban daban babu dadin ji yaransu da manyansu,wani baqinciki da bacin rai take ji ya shaqe,duk yadda takeji da rashin arziqi amma wai har yau za’a samu mai taka ta?,malam kawai take jira ta sauje masa kwanson tsiya,sam bazaiyiwu ta zauna cikin irin wannan qasqancin ba,ai neman kudi ba hauka bane,kuma ita ba matarsa bace bare ta shiga sahun irin rayuwarsu.

????????????????????????

Kamar kowanne maraice da suke qare shi gaban qoramar bayan gari yauma haka ne,saidai yau kam akwai banbanci domin,kwanaki uku kenan suke wasan buya da mero,koda wasa taqi haduwa da maryam saboda tsoro da kunyarta,sau daya da safe maryam ta fito ta tadda meron zaune bakin rijiya ta zubawa qofar dakin su ido suka hada udo,kallon da maryam ta yi mata yasa ta miqewa cikib hanzari da kame kame ta hau yin wanke wanken da dama shi zatayi ta zauna zaman kallon dakin,idan ta zo da safe ta yiwa inna wuro aikace aikacenta a gurguje take barin gidan duk da yadda har yanzu zuciyarta taqi yadda ta rabu da abdallah,batajin zata iya ci gaba da rashin ganinshin.

Material ne ajikinta mai santsi milk ne da adon manyan fulawoyi ash colour,dinkin bubane da ya saukar mata har qasa tayi rolling har zuwa kafadarta da mayafi cotting ruwan madara,yadine tissue a jikin abdallah light blue dinkin boda gajeriyae riga iya gwiwa,ba qaramin kyau yayi ba cikin yammacin,wani lokacin maryam kanyi mamakin yadda fatar abdallahn ke qara kyau tamkar ba cikin qauye yake ba,ta alaqanta hakan da yadda weather din garin ke da kyau da ni’imtarwa.

Kamar kowanne lokaci garin a lullume yake,a wadace da korayen tsirrai,a hankali suke tafiya,jinta take kamar wadda kasala zata lullube,shiru suke tafiya hakanan a hankali,abdallah na sake nazarin qauyan,shiru hanyar tasu take yau fiye da kullum,babu gilmawar mutane kamar ragowar kwanakin,duk dama ba hanya ce ta jama’a ba.

”haqiqa Allah mai hikima ne baiwa da kuma cikakken iko,babu shakka Allah ne kadai masanin sirruka da boyayyun al’amura,wannan garin ya amshi sunansu babu ko makawa,a koda yaushe na wayi gari,cikin qauyen nan nakanyi duba izuwa tarin ni’imomi da baiwa da Allah ya musu,hakan yake sake sakani,cikin sakankancewa da iko da isa ta ubangiji,nake sake nisa da nutsuwa gun miqa qoqon bara ta agareshi,tabbas na yadda babu makawa Allah na ji kuma akwai lokacin da zaya bude min gaba daya qofofin ni’imarshi”shiru maryam tayi na saurarensa
sassanyar ajiyar zuciya ya saki shima yana kin kasalar na saukar masa.

”maryam”ya kira sunanta cikin wani irinsalo da ya qarasa kashe mata jikinta gaba daya,hakanan taji bakinta ya mata nauyi ta gaza amsawa
”maryam…..sai yausge zaki bawa zuciyarki dama ta bayyaba abinda yake cikinta?,sai yaushe zaki bata dama yaushe zaki bata ‘yancinta?”
gaba daya sai ya qarasa qulle mata duk wasu qofofin qwaqwalwarta ta shiga kai kawon nazarin maganarsa,bilhaqqi da gaskiya ya sake tubudata cikin wani duhun ne,meke cikin zuciyar tata da yake tambayarta ta bata ‘yancinta a kansa?,bata kai ga warware qullin ba ya sake jefo mata wata tambayar.

”maryam,sona ne maqare cikin zuciyarki,so na ne yake hanaki sukuni duk lokacin da na kadaice da mero,so na ke saka ki cikin yanayi na kasala da mutuwar jiki,me yasa zaki takureshi a muhalli guda ki hana shi fitowa inda ya dace?”ya waiwayo yana dubanta tare da qoqarin kallon qwayar idanunta
bugun zuciyar ta ya sake yawa,tayi gaggaqar cire qwayar idonta daga cikin tasa ta maidata gefe wani abu na taba zuciyarta,me yasa abdallah ke mata haka ne,ko yaushe rauninta yake son gani kuma bata jin zata barshi ya gani din
zuciyarta ke qarfafarta ta qaryata batun abdallah,cikin muryar da ka mata dogon nazaei qwaya tal zaka gano akwai wani abu mai qarfi cikinta tace
”kada ka soma bari zuciyarka ta dora ka akan keken bera,don ko digo babu wani abu mai kama da so cikin zuciyata game da kai,ko ka manta abdur rahim ta so shi kuma ta aura a zatonta?,saboda haka babu so tsakanina da kai kaima ka sani”.

dan guntun murmushi ya saki sannan yace
”irin wanna karsashi da jurumtar na maryamu na dade ina ganinshi cikin idonta tun tana a matsayin kukun abdallah a gidan mami,saidai wani abu guda da bata sani ba,ta dade da makarowa,tun ranar farko da taga abdallah ta fada tarkon sonsa,duk da jarumtar boyewar da take amm is too late don abdallah ba a iya boyemiahi ire iren wanann abubuwan,don ya saba ganinshi cikin idanun ‘yan mata daban daban,amma fa wani abu daya da maryam bata sani ba,abdallah shima ya fara sonta ne tun lokacin da ta fara sonshi,sunso juna a rana guda lokaci guda a guri guda a kuma sakanni guda”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button