ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba daya ilahirin jikinta ya kama rawa har ta gaza ci gaba da rura wheelchair din,wanne tonin silili abdallah ke son yi mata,saidai sam na zata bashi dama ya riga zare mata duk wata laka da qwarin gwiwa dake jikinta ba yadda yaga dama,don haka ta ttara sauran dukkan wani karsashi nata
”idanunka da zuciyarka sun maka qarya abdallah,ban taba sonka ban taba sha’awar na qaunaceka ba ko ka manta da bakinka kasha fadan ba kowacce mace ta dace da kaiba?bako wacce mace ta cancanci ka sota ba,nasan naso abdur rahim amma ba kai ba kuma bana sonka,bana sonka bana……”
idanunshi a rufe suke yana jin saukar maganarta,sukan zuciyarshi take da wani abu mai kaifi ba tare data sani ba,duk da zuciyarshi na qaryata duk wata magana dake fitowa daga bakinta saidai bai son jin furucin sam,sannu kuma kishin abdur rahim mai qarfi ya fara shigarsa,sanadiyyan katsewar maganarta shine fincikota da yayi ta dire a gabanshi,rashin qwarin jikinta ya sanyata zubewa a gaban nashi.
Murmushi ne kan fuskarsa wanda ko yaushe ke fidda sigar kyawunshi
”banyarda baki son abdallah ba sabida na jima da ci miki alwashin sai kin soni,alhmdlh ban zama looser ba ni nayi nasara,but now ina mai qara tabbatar miki sai son abdallah ya ninku cikin zuciyarki fiye da da,i promise”ya fada yana miqa mata qaramin yatsanshi alamar su qulla,ba tare da jinkiri ba ta miqa masa suka qulle kamar yadda yara keyi,shi ya dagata da kanshi ya kade mata jikinta kana suka ci gaba da tafiya.
suna tafe yana murmushi,raguwar kuzarin jikinta kawai ya isheshi amsar tambayarsa,sai da suka qara mintinan da suke yi akan nada kafin su isa ta ajjiyeshi inda ta saba,qur’aninsa ya ciro gaban aljihunsa don kwana biyu da suke tahowa su kadai da alqur’ani yake tahowa,yana yin tilawa kuwa mai yawa kafin su koma,wucewa tayi gurin da ta saba zama kamar ko yaushe ta zauna.
ta daga idonta take ta hango shanun su baffa da kwana biyu bata ganinsu,murmushi ta saki don sun kwana biyin basu gaisa ba,ciro qafafunta tayi ta karkade jikinta bayan ta miqe ta maida takalmanta ta fara tafiya,daga idonshi yayi a hankali ya bita da kallo,yana lura da yadda ko yaushe idan sunzo idonta na tsallaken rafin bai san meke burgeta ba a gun.
kamar ko wanne lokaci daga baya ta tsaya bata shiga cikin shanun ba sai baffa ne ya isketa,tamkar wadanda suka ahekara tare haka suka dinga hirarsu,ta tambaya kwana biyu bata ganin fitowarsu yace eh mai gida ke fidda zaka cikin dabbobin nasa to sai jiya ya kammala shi yasa sai yau suka fito
ba tare dafa tambaya ba ya ciro wani mazubi mai kyau ya fara tatsar mata madara
”mai gida yace duk sanda ka zo a baka,yana ta tambayarka ma”tayi murmushi tana fadin
”Allah sarki na gode kuwa baffa”ta miqa hannu ta karbi mazubin tayi bismillah ta fara sha
”kisha ahankali idan bai isa ba ma sai a qara miki”taji muryar daga gefanta na gada,ta daga kanta ahankali,mahmud ne yauma cikin shigar kufta,murmushi ta danyi kana ta ja baya tana fadin
”ina wuni”ya amsa mata da ”lafiya lau,tun rannan kuma sai kika bace abunki ban sake ganinki ba”
‘?eh wlh ta amsa masa a taqaice tana rufe mazubin ta miqawa baffa
”baffa gashi na gode ni zan wuce”
”a’ah,jeki da shi meramu,duk lokacib da kike so kizo da shi sai a dinga zuba miki ciki”godiya ta masa don abun ya mata kyau,dan mazubi ne maikyau irin na fulani
”zaki gudu kenan kam irin na rannan?”ya tambayeta yana dan dada sauri don su jera tare
”a’ah,bani kadaice bace na fada maka,da yayana kuma mijina muke tare”ta fada cikin rashin sakin jiki
dariya ya saka
”wai ni zaki yiwa wayo,don kin fuskanci na yaba ko?”
kai ta girgiza idanunta a qasa
”da gaake ni matar aure ce”
”nima mijin aure ne”ya maida mata amsa cikin maida maganar wasa wasa,ganin da gaske yaqi yarda din ya sata tsayawa da tafiyar da takeyi don sun,kusa da inda abdallah yake bayan ta rage fara’ar fuskarta sosai
”idan baka amince ba muje ka ganshi da idonka,amma ka fara yin gaba tukun yana nan zaune akan kujera idan yaso sai na biyo bayanka”.
kafada ya daga kana yace
”is ok,bari nayi gaban,amma da sharadin idan qarya kike zaki amshi soyayyata”
kada kai tayi kawai ba tare da tace komai ba idanunta suka sauka kan abdallah zaune kan kujerarsa a gabansu,mamakin yadda ya iya kawo kanshi tayi,sai ta dubi kujerar wasu abubuwa guda biyu ta gani gefe da gefe bata taba kula da su ba wanda bisa alamu da su ya tuqa kanshi.
Kallo daya ta yiwa idonshi bata sake marmarun kuma kallonsu ba,ya kalleta ya kalki mahmud sai taga ya danna wani abu,rivearse kujerar tayi da kanta kana ta saita hanya ya soma tafiya sannu a hankali
”ko baki fada ba nasan shine mijinkin,kiyi haquri don Allah,wlh harga Allah ban dauka da gaske kike ba”mahmud ya fada cike da damuwa
a gagguce ta gyada kai bata samu cewa komai ba ta biyo bayan abdallah.
mrs muhammd ce????
????????????✍????✍????✍????
[2:00pm, 9/29/2017] Huguma????: [11:46am, 9/29/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
5⃣0⃣
????????????????????????????????
shin ka/kina lura kuwa ‘yar uwa?,kin fuskanci kuwa yadda kwanaki keta zura gudu abinsu?,kinsan me hakan yake nufi a gareka/ki?,tamkar gaya miki suke kifa shirya kina kusantar kabari ne,ki shirya kina kisantar ajalinki,ki shirya kwanakin ki na duniya da aka diba miki na qarewa
daure ki aikata mai kyau don ki tarar da me kyau,babu yadda za’ayi ki shuka qaya kice inibi kikeson cira,duk fitar numfashinki daya daidai yake da kusantowar ajalinki,yadda idan second guda ta kubuce miki har abda bazata dawo ba haka ajalinki idan yazo daidai da qiftawar ido Allah bazai barki cikin duniya ba,to don me zaki batawa kanki lokaci kan cutar da wani?,don me zaki damu kanki da ababan duniya,duniyar da take wulaqantacciya?,duniyar da Allah yace bata kai qima da darajar da girma daidai da na fukafukin sauro a gurinsa ba,saboda me zaki shagala kin manta ki daina tuna mutuwa,bayan kina da yaqinin tabbas/lallai/babu makawa sai kin muyu kamar yadda kika ga wasu sun mace kema wataran haka ne,komai qararre ne banda zatin Allah,ya ubangijin kowa da komai ya mai rahama da tausayin bayinsa kasa muyi kyakkyawan qarshe,mu mutu muna kan tafarkinka na gaskiya
ALHAMDULILLAHI ALA NI’IMATUL ISLAM
kafin na fara shafin nan ya zama dole na gaisar na kuma miqa godiya ta ga masu aiko da saqonninsu gareni,saqonninku sun ishemin,ina muku fatan alkhairi naji dadi qwarai da addu’o’inku,abinda kuketa roqamin na alkhairi ina fatan Allah ya sanyaku ciki kuma
ummi jos
mrs tafida
haulat m badamasi
Aisha kanyah
ummu zainab
sis rabi’a
jammy jammy zbi group
zahra hari zbi group
na gode Allah ya bar zumunci da qauna????????
Cikin kwana goma sha hudu da zahariyya tayi cikin gidan ba qaramar dandana kudarta tayi ba,sauqinta daya malam na hayi ya tsawatarwa iyalin nasa bayan bore da tayi ta samu sauqin abubuwa,saidai babu mai kulata ci kanki babu mai ce mata,ita din ma bata damu ba domin ta dade da raina ajawalinsu,tana ganin babu wadda tayi isar da zqtq rabe ta balle mu’amala ta hadasu,banda neman biyan buqata daya tilasta ta zama cikinsu ba su isa ta zauna da su ba har wata guda,ba don suna waya da nene ba tana tausarta ta tabbatar da tuni ta jima da cika bujenta da iska,wuyar ta isheta,kullum dare kwana ake ana abu daya ita da aljani zul anfaini,ga masifaffen wari da take ji jikin aljanin wanda kullum yake sata tashi da amai da ciwon kai