ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Dadin bakin neme da lussafin da tayi na saura sati biyu ta bar wanann zaman shahadar,saura sati biyu ta zama mai arziqi irin aezuqin nan na kwatance na gayawa sa’a yasa ta danne taci gaba da lissafin
Misalin sha biyu ne na rana wanda ko ba’a fada maka ba kasan lokaci ne da rana ke kan ganiyar zafinta,bare rana irin ta qauye da take budewa sosai saboda wadatar fili da suke da shi,tana cikin dakin amma ji take kamar tayi hauka,ta riga da ta saba zama cikin a.c ko yaushe,rufin dakin na langa langa kawai ya taimaka wajan qaro dumamar zafin ranar zuwa cikin dakin
tsaki ta ja tana goge gumi
”kai,Allah ka tsinewa talauci,me za’ayi da talauci don Allah,Allah ka nuna cikar sati biyun nan nayi na gama wannan aikin na san inda dare ya yimin,ai wlh ko a hanya bazan bari mu hadu da talauci ba,zamana nan gidan kawai ya qara fito min da illarsa qarara wadda a baya ban sani ba,haba wannan azaba dole ne ma fa kasona cikin dukiyar abdallah tafi yawa idan mun karbe wallahi”ita kadai take sumbatu cikin dakin,vest,ce kawaia a jikinta doguwa har zuwa gwiwa amma ji take kamar tayi tsirara
kallo daya zaka mata kaga yadda fatarta tayo baqi ta kuma rame a hakan ma wai aljanin mujinta na dauke mata abinci irin wanda ta saba ci yake kawo mata,ta kuma jan tsaki ta gyara kwanciyarta kan katifar ta don dama ikin kenan,idan ta kwanta irin haka ko sallah saidai ta yi maja ta hadeta baki daya
Karo na farko taji ana qoqarin dago jibgegen labulen dakin da ya qara sawa dakin duhu,kanta ta dago don ganin waye,domin bata taba ganin wani ya rqbo bakin qofar dakin nata ba idan ka dauke malam na hayi
siriryar macace wadda a kallon farko zaka gane sanda duniya na damawa da ita fara ce,wuya da yunwa suka maidata baqa baqa duk da akwai sauran haskenta,tsugunnawa tayi gefan zahariyya da ta zuba mata ido tana kallonta bayab tayi kicin kicin da rai,murmushi matar ta saki wanda ya bayyana jerarrun haqoranta da suka dafe
”sannu amarya,dama zuwa nayi na gaya miki ki fito yau zaki amshi girki”
Ba shiri ta miqe zaune daga kwanciyar da take a dazu,ckkin sake hade girar dama data qasa tace
”ke malama,bana son hauka,wa ya gaya miki ni matar gidan nan ce?,akwai abunda ya kawo ni zama nan kuma nan da sati biyi zan bar muku wanann dajin naku”
murmushi ta gani matar ta yi har da dan darawa kadan
”Allah sarki,ina zaton azal din data hau kaina kema ita ta hau kanki”cikin raahin fahimta take dubanta,daga bisani ganin matar bata da niyyar cewa komai ta kafe zahariyyan da ido yasa ta tambayeta
”kamar yaya?”ajiuar numfashi tayi,wannan karon zama tayi dirshan kan ledar dakin
”malam ga aureki ba tare da sanin cewa shi kika aura ba ko”
”inji uban wa?,ni ba malam na aura ba,aljani zul’anfaini na aura,kuma ina sane,kada ki zomin da maganar banza,malam din da sai da safe yake leqoni mu gaisa ko ya kawomin saqon aljani”
dariya ta subucewa matar sai da tayi iya yinya kana ta tsagaita,zahariyya bata samu faragar tsaidata ba don kanta a qulle yake tamau
qasa qasa tayi da muryata kana tayi yan dube dube don tabbatar da babu wanda yake jinsu
”akwai wani aljani ne bayan malam na hayi?,ai malam shine aljani,zul’anfaini yana biyo dare yana turmusheki da sunan aljani,dalili,kenan da ya kafa miki sharadin zama cikin duhu daga magariba har gari ya waye”
tsawa zahariyya ta daka mata jikinta ya soma bari
”ke malama,banasom hauka don na fuskqnci duka jama’ar cikin gidan nan kamar daga gidan mahaukata aka debo ku”
murmushi fa kuma yi
”kema din kwana nawa ne kinbi sahu,badai kin gama kwana goma sha hudunki ba,ki fara duban hanya to”daga haka matar ta miqe tana niyyar ficewa,ganin indai ta fice din kuma babu lallai zahariyya ta sake samun wasu bayanai ba tunda babu da wanda take magana hakanan babu wanda ke magana da ita ya sanya ta riqo gefan daddaudan zaninta
”ya zaki sakani a duhu kuma ki tafi,don Allah zauna kimin bayani mana”sai data qarewa zahariyyan kallo na kusan minti biyar har taji ta tsargu sannan ta koma ta zauna inda ta tashin
”suna na habiba,ni nan da kika ganni ada yadda kike haka nake koma nace na fiki”cike da mamaki zahariyya ke kallin habiban wadda babu mugumin da zai kalleta baice mahaukaciya bace
”mamaki kike,to ki daina mamaki don kema lokaci kadan ya rage ki koma kamar mu,ba kanki malam ya fara haka ba,’yar gata ce ni gaba da baya,don gaba daya a buja muke zaune ni da iyaye na,haka da na tashi aure ma acan nayi aure na,na auri mijina mai kudin gaske saidai na taddashi da matarsa da yaransa uku,matarsa fatima sam bata da fitina,duk yadda taso mu zauna lafiya fur naqi,burina kawai shine na koreta daga gidan na mallake enginer abubakar,iya adalci yana nina shi tsakaninmu babu zalunci tattare da shi,wani abun ma haqqinta ne fatima amma zata ce ta barmin sabida haqurinta da kawaici,duk inda nasan zan samu malami da zai mini aiki na kutsa kai na sai dai babu nasara,sabida fatima irin matan nan ne masu yawan azumi duk litinin da alhamis bai wuceta,haka tana da yawan salla musamman ta dare,don nasha tashi aiwata da mugun nufina a kanta sai na taddata tana sallah,haka karatun alqur’ani,kafin ka samu fatima kan wata tasha ba saudi qur’an ba kai da wuya,amma hakan bai isheni iahara ba,da yake bata da haqqina Allah na tare da kta kuma yayi nufin kareta sai muka samu labarin malam na hayi
Babu bata lokaci muka shirya ni da mahaifiyata wadda ita ke taya bera bari na yiwa enginer qaryan zamu kano ziyarar yan uwan mama duk da salinmu ba kanawan bane yan katsina ne ya sani amma baice komai ba ya amince ya barni,har da bani kudi nayi tsaraba,har bakin mota fatima ta rakoni tasa yaranta na min a dawo lafiya amma ko kallo basu isheni ba muka taho,tun zuwan mu na farko yaci ace idan da ni mai rabo ce na gane inda malam na hayi ya dosa saboda kalamai da hanyoyin da riqa bi da ni neman biyab buqatarsa amma na kauce na qiya,qarshe ya harhada min duk wani abu da zan aiwatar cikin gidan muka taho bayan iyayen kudi da muka zube masa,amma wani abu da ya bani mamaki tsakanin fatima ko ‘ya’yanta babu wanda yayi ciwon kai bare na sa tsammanin wani mummunan abu zai faru da su,ta tsaya tsayin daka wajen yiwa yaranta addu’ar tsari,hakanan lokuta da dama zaka ga ta cika botiki da ruwa ta musu tofin ayoyin tsari ta sa musu a frigde shine ruwan shansu duk da ruwan roba da mahaifinsu ke cika mana firizai da shi
ko cikin dare udan ta farka duk da ba dakinsu daya da yarqn ba sai ta leqa dakinsu ta tofa musu addu’o’i take komawa nata dakin nasha ganinhakan da idona,to duk abuna musulma ce ni kuma masan addu’a takobin mumini ce nice dai nasa qafa na shure,na tabbatar bazan nasar a kan fatima ba don,haka hankalina ya tashi ba bata lokaci muka sake dawowa,ashe zuwan tsautsayi da qaddara mukayi
cemin yayi kada na damu akwai wani abban aljaninsa da zai bawa kwangilar aikinsu fatima amma shifa ba biyansa ake da kudi ba,ana biyansa ne ta hanyar auransa na wasu satitika ko watanni,da fari tuburewa nayi ganin da akwai auren enginer a kaina,amma da dadin baki malam ya ciyo kaina yace sati biyu kacal zanyi zaman auren ina komawa gida na zan taras buqata ta biya,nace ta yaya za’ayi mikina ya barni nayi tafiya har ta tsawon sati uku,wani garin magani da wasu layoyi ya,bani yace na samu dutse cikin gidan mu qato na daga qasanshi na saka na danne,yadda na danne layoyin nan haka engineer zai kasa min musu duk sanda na tambayeshi,haka kuwa akayi baice komai ba face Allah ya kiyaye hanya sai na dawo