ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

satina daya cikin gidan ina wahala don ban saba ba sam,cikin daula na tashi haka cikin gidan mijina ma,amma da yake son zuciya da son duniya ya rufemin ido na daure a haka har nayi kwana goma sha biyu,kamar irin wannan lokacin da na zo miki haka daya daga cikin matansa tazo min da irin maganar da nazo miki uadda kika yimin haka nayi mata nima,yadda na zauna na baki labarina haka ta bani labarinta ita din ma duk kusan hakane,saidai ita maganin mallaka tazo ta karba,mallakar ma ra saurayi,saidai ita tasan malam ne zai aureta don yace wani rubutu zai dinga yi a alqalaminsa yana wanke mata acikinta,ta gayan har yau ta kasa kubuta daga gunsa,na fiki shiga tashin hankali sabida tuno mijina da gidana da iyayena da nayi da yarona qwaya daya da na haifa yana gida hannun fatima tace zqta riqe minshi har na dawo

Na fita da niyyar guduwa daga gidan saidai kinsan me?,wuni nayi ina shawagi cikin duhun masada da na dawa,an qullemin kaina tamau na rasa hanya,duk inda na kewaya ina tsammanin zai fita sai inga na dawo gidan nan,daga qarshe da duhun dare yamin babu wanda ya neme ni haka na dawo,kwana na bakwai ina wannan wahalar cikin gidan babu wanda yace min ci kanki hatta da shi malam din haka zan gama walagigi na na dawo,daga qarshe na tabbatar bazan iya kubuta ba haka na dawo naci gaba da zama na fawwalawa Allah lamura na,ina zaune cikin uqubqar malam din,matansa mu goma sha hudu ne kowacce tana da rana daya a matsayin ranar girkinta,yaransa guda hamsin ne,wasu suna nan tare da mu wasu sun watsu duniya,nima haihuwata uku da shi suna mutuwa yanzu haka yaronmu daya da shi shine wanda kika mara rannan kaltime ta janyeshi,mamata kuwa ban kuma jin duriyarta ba,wani abun ya manta ta manta ni ko itama kasa gane gidan tayi Allah masani”ta qarashe maganar cike dq dacin rai da danasanin butulcewa ni’imar Allah da tayi,ta kasa zama lafiya a gidan aurenta bayan babu abinda ta rasa,dama ance idan baka godewa ni’imar Allah ba ka godewa azabarsa.

Tuni har zahariyya ta saki fitsari a zaune,gumin da take kuwa tuni ya ninka na dazu,ta tabbatar idan da za’a auna jininta banu makawa za’a ga ya hau over ma akuwa
taya za’ayi ta zauna da wulaqantaccen mutum kamar malam na hayin
Tayaya zata yarda ta zama mallakarsa,wallahi bazai yiwu ba”ta fada qarfi kuma a fili tana miqewa ta fara hada akwatunanta
kallonta habiba tayi
”wai me kike shirin aiwatarwa”a fusace kuma cikin ficewar hayyaci
”wallahi sai na bar gidan nan ko da me malam yake taqama din ni ba kalarsa bace,kudin ma raina muku wayau yayi”dariya habiba tayi
”duk yadda kike jin isa taurin kai da kafiya na fiki,malam mutum ne da baisan kalmar imani ba bare tausayi,ina mai baki shawara ki haqura ki maida lamarinki ga Allah ki roqeshi,watan wata rana idan da rabo kowa sai Allah ya kubutar da shi,amma,ina mai tabbatar miki koda kin fita ba zaki iya tsira ba,idan kuma baki yadda ba kina musu bismillah”daga haka habiba ta miqe ta gyara daurin zaninta ta fice

ko kadan zancan habiban bai shiga kunnuwanta ba don haka bata fasa shirinta ba,ta hada kayanta ysaf ta canja kayan jikinta ta jawo akwatunanta tayo tsakar gidan,da ido suka bita duuu kamar ko yaushe,wanann karon sam bata damu da kallonsu ba burinta kawai shine ta ganta ckkin gidansu

Cak ta tsaya a qofar gidan tana wara ido,ruwa ne a gabanta yake ta qugi iya ganinta,,duk hanyar da zata bi ta wuce ta zam hamshaqin kogi wanda ko da kwale kwale zaiyi wuya ka iya tsallakeshi don har wani murdawa igiyar ruwan take,duk lokacin data yi taurin rai ta tunkari kogin ta yunqura dan shigewa ruwan sai yayo ambaliya yayo,kanta tilas ta koma da bay
ta shafe fiye da awa biyu a gun tana abu daya daga qarshe ta gaji ta faahe da kuka don ta fara ganin alamun maganganun habiba

zubewa tayi a dandaganyar gun ta saki kuka tana addu’ar Allah yasa mafarki take,ya rayuwa zatq juya mata baya haka lokaci guda ba tare da ta shirya ba,dabara ta fado mata ta dauko wayarta ta soma lalubar nene don neman daukinta

Daidai lokacin da nene da adnan ke tsaye cikin daki cike da tashin hankali sakamakon waya da muugu yayi wa maman kan ta taryi zuwansa,kuma kada ta taba darsawa aranta zata gudu duk inda suka shiga sai ya bincikota kuma babu shakka kasheta zaiyi
”yanzu adnan meye abunyi?,meye abunyi?,na kikkira malam wayarsa bata samuwa,babu shakka aikin da yayiwa muugu ne ya warware”ta fada cike da tsananin tashin hankalin,shi kansa adanan din a tsorace yace don har yau bai warke ba daga bugun da suka masa,jikinsa na rawa yace
”don Allah mama ki nemo kudinsu ki basu kawai mu rabu lafiya,wlh basu da imani mutanan nan sun saba da kisa fa”
cikin jin zafi take kallinshi,saida ta zageahi sanann tace
”fashi da makami kake so na far ko karuwanci,a ina zan samu wata miliyan biyu?”
”yauwa mama”ya fada da sauri yana dubanta
”ki cewa hajiya bintu ta baki mana bana ko kokwanto akwai a hannunta”
”mtsweew,wlh bansan na haifi jaki mai toshashshiyar qwaqwalwa ba sai yau,ina cewa a gabanka malam ya gaya mana kada mu sake magana ta qara shiga tsakaninmu,ni ko kai ko zubaida idan ba haka ba asirin da yake jikinta zai karye?bacin haka ma kwananta nawa bata cikin gidan nan ni da kai duka babu wanda yasan inda ta tafi?,kuma wa’adin cikar aikin zahariyya har tau bai cika ba saura sati niyi bare mu sa ran samun wani abu”
”gashi babu company din da muka karbe qwaya daya dake aiki yanzu bare mu samu cikinshi,duk a qulle suje mun cinye duk wata dukiya nene dake ciki”ya fada yana kallon nenen da ta kasa amsawa sai ido ta take binsa da shi cikin damuwa
shiru yayi cike da tsoro
”to nene ko gwalagwalan su zubaida zaki karba ki bashi ya saida,idan yaso muji nawa zamu cika masa”
”haka za’ayi”ta fada cikin rawar jiki tana barin dakin ya rufa mata baya

ta tura qofar dakin ta shiga babu kowa ciki saidai tana iya jiyo kakarin amai cikin toilet dinsu,da sauri ta qarasa bandakin,zubaidan ce tsaye gaban sink tana ta faman kwara uban amai,cak nenen ta tsaya tana mata kallon tuhuma har ta kammala ta kuskure bakinta ta juyo
”zubaida me nake gani?”
ta tambayeta cike da tashin hankali,ko kadan zarafin da ta shiga na kwanakin nan yasa bata samu damar zama agida bare ta qarewa zubaidar kallo,ta dashe tayi fari ga cikinta da ya fara dan dagawa kadan,kallo daya tak mai hankali zai mata ya bawa kansa amsar ciki ne da ita

fuska ta yatsina tana kallonta tare da qiqarin boye cikin
”wlh nene nima bansan me yake damuna ba”hannu ya saka ta daki cikin jikinta tace
”don uwarki don ubaki tsinanniya ga abunda yake damunki nan”take zubaidan ta durqushe tana dafe da cikin hadi da cewa ”wayyo Allah na”nenen bata damu ba ta finciko ta sai ganinsu adanan yayi tana janye da ita bata saurara mata ba taci gaba da janya sai da ta kawota har falon qasa kana ta watsar da ita
”don uwarki sai kin gayan wanda ya miki cikin nan,shegiya tsinanniya mara amfani,gwara na kasheki na kashe banza bani da asara,cikin shege a jikinki zubaida”ta kai mata duka ta kuwa sameta,qara zubaidan ta saki wanda yayi daidai da shigowar kira a wayarta
a niyyarta ta cilla da wayar sabida tashin hankalin da ta fada amma ganin sunan zahariyya yasa jiki na rawa ta daga tana fadin ‘yar albarka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button