ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

komai sai ya tsaya mata cak jin bayanan bakin zahariyyan data yi wanda tana kuka tana zayyane mata,bata ma gama ji ba ta dakatar da ita tana fadin
”gani nan zuwa har gun malam din,shi ya isa shi din banza,a kaidina baisan komai ba yau zai sani”qita taji wayar ta katse haka zahariyyan taji,tana dubawa taga kudinta ne suka qare haka wayar ta soma warning na battery low,dama a power bank dinta da ta taho da ita take chargyn tunda ko sau daya bata taba ganinsu da wutar lantarki ba,kai ko igiyoyin wutar ma babu a ina ma zasu samu suna dajin Allah?,tana ji tana gani wayar ta mutu,hannu ta dora aka ta saki wani sabon kukan ta kife kanta tsakanin cinyoyinta
Sau uku nene na trying na kiranta sai ace mata is switched off,tilas ta haqura ta kalli adnan
”muje adnan gurin malam,wani bala’in yake son jawo mana”adnan ya zaro ido don shi,kam ya gaji da jin wannan bala’i kala kala har yau kuma babu sauqi,zaiyi magana tace
”kame bakinka muje koma mene kaji a mota”ta juya ta kalli zubaida dake durqushe
”ke kuma idan ba shirya barin duniya kika yi ba to ki nemo wanda ya miki ciki tin kafin na dawo na aikaki lahira”ta kaimata mari tana sake tsaine mata ta kuwa sameta akuncinta,dafe kuncin tayi tana fidda qwalla ba don komai ba sai don azabar zafin marin
”ga wanda yamin cikin nan”taji zubaida ta fada,ta dago kanta daga qoqarin sanya mayafin ta da take tana duban inda zubaidan ke nuna mata,saura kadan numfashinta ya dauke sakamakon ido hudun da sukayi da muuugu da yaranshi,fuskarnan yadda kasan wanda ya dauko saqon mutuwa a hade take tsaf,abu biyu zuwa uku ne suka daki zuciyar nene lokaci guda,kudinsa da yazo karba wanda a yanzu bata da shi bata da shi bata da dalilinshi,na biyu cikin da yake jikin yarta wai nasa ne?,na uku yadda taga sun cukuikuye adnan ko cikakken numfashi baya shaqa
sakin adnan din sukayi yaci qasa kana ua tako a hankali gaban nene yana jujjuya wuqar dake hannunshi,batason ta nuna masa tsoratarta don haka ta tattaro yar mitsitsiyar dauriya ta dorawa fuskarta don bata kai zuciyarta ba,hannu ya miqa mata,sai ta kalleshi sheqeqe
”me kake nufi?”dariya ya kece da ita wanda har hantar cikin nene sai data kada balle adanan da ya dade da sakin gudawa,don b qaramin tsoron mutuwa yake ba arayuwarshi
”banda ke mara mutunci ce har sai na miki bayani ma,zan mkki bayani amma ki tabbatar a bakin rayuwarki”
ta tsorata ainun amma sai ta fara masa haukan qarya
”banda kai matsiyaci ne baka da kunya ko misqalazarratin,ka dirkawa diyatq ciki sannan kuma kace na biyaka wadansu kudade,to wallahi na fika iya iskanci,baka isa ba”
Daya dagq cikin yaransa ya matso yana fadin
”ke hajiya ki iya bakinki,ai dama kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa,bamu da mutumci kamar yadda ke ma baki da shi don babu mai mutumcin dake hada sabgarsa da mu”
”kai yaro dakata a haife na haifeku gaba dayanku,to wallahi duk ba tsoronku nake ba,kudi ne bazan biya ba kuma ku saurari sammacin kotu sai nayi shari’a da kai kam cikin da ka yiwa diyata tun…….”
wani kyakkyawan duka da ya sauka tsakiyar kanta ya haddasa wa qwaqwalwarta daina aiki na wucin gadi,wasu taurari suka kewaye idanunta take ta sulale ta fadi a gun,sai da ta kusa kusan minti biyu sannan jinta ya dawo sai ta kasa bude idanunta,mugu ya tako inda take ya tsaya qerere a samanta yana dubanta
”da niyyar kasheki nazo ke da wancan wawan dan naki qauran mata,amma kunci darajar abinda yake cikin yarki wanda dana ne kuma jikanki,nasan kina jina don ban miki dukan da zaki mutu ba,amma zan baki zabi biyu,ko ki biyani kudina ko kuma na dauke yarki ta zama matarmu,na baki nan da kwana biyar kiyi shawara”
ya juya ya isa inda zubaida take ya dagata ya rungumeta yana shafa cikinta
”kada ki sake ki bari wani abu ya samu cikinan don ina buqatar wanda zai gajeni,duk dan kaza kazan(ya duro ashar) da ya kuma takuraki ki takashi kema yadda ranki keso”ya fada yana sakinta,ga mamakin adnan murmushi yaga tana yiwa mugu har suka juya suka fice daga gidan wanda shigowar mami suka yi kacibus suna ficewa a qasa ita kuma tana shigowa da motarta
bayan ta faka motar cikin mamaki ta fito ta nufi gun security guda uku da su kadai yanzu suka rage a gidan
cikin girmamawa suke gaidata don har yau suna son uwar gijiyar tasu,tambayarsu tayi
”wadan nan mutanen kuma daga ina suka fito”
daya daga cikinsu ne ya amsa mata
”daga cikin gida”fuskarta qunshe da mamaki ta sake tambayarsu
”cikin gida kuma?,gurin wa suka zo?”
wannan karon wani daban ne ya amsa mata
”gun hajiya nene,ai sun dade suna zuwa gunta,ko kin manta ne hajiya,kwanaki ke ta saka kika basu kudin mota”
cike da mamaki ta nuna kanta
”ni?ni kuma usaini?”
”eh hajiya ke”
ganin sun zuba mata ido sunata kallonta sai ta dauko wani batun
”yanzu ina su samuel da ibrahim”
”hajiya duk an dakatar da sh daga aiki,kuma da aka tambayeki kika ce kin amince,yanzu saura security biyar daga cikin goma sha biyar dake aiki cikin gidannan”
wani mamakin ya sake kamata,jinjina kai ta dinga yi don duka batasan anyi haka ba,ta yaya zata kori su ibrahim bayan sune manya manyan security na gidan tun zamanin alhj abdulkareem mai nasara na da rai,muta ne ne masu amana da cikon alqawari
”ka nemi numbers dinsu ka kira ka kirasu gaba daya kace ina son ganinsu daga yau zuwa gobe,wanda baka samu,contact dinshi ba ka dauki mota ka bishi inda kasan zaka sameshi”
cikin jin dadi yace
”yes madam” don dukkansu suna fara ganin alamun lallai sauyi ne wata qila yake tunkaro gidan
Har tayi gaba ta dawo
”kada a sake barin wani mutum makamancin wadancan mutanen su shigo gidan nan”
cike da bin umarni suka amsa
waiwayo wa ta sakeyi
”amm…usaini,bama su ba duk baqon da za’ayi ku tabbatar da wane shi kafin shigowarsa gidan nan kamar dai yadda aka saba a daa”nan ma amsa mata sukayi a ladabce kana tayi gaba
idanunta suka kai ga hanyar sashen abdallah,can qasan zuciyarta taji tana son shiga saidai wani abu ya taso ya danneta,haka tana ji tana gani ta sauya akala ta shige bangarensu tana ambaton ya Allahu
har zata shige ta ringa jiyo ihu ihu a bangaren nene,juyawa tayi ta nufi sashen nenen don ganin meke faruwa
????????????????????????
A hankali ta qarasa shigowa cikin dakin hannunta dauke da tray dake jere da kwanukan abinci a kansa,gabanshi ta qarasa ta ajjiye tray din,wanda har ta shigo ta ajjiye din yana zaune kan wheel chair dinshi kanshi a duqe a qasa,shi kadai ahi da Allahn sa yasan abinda yake ji cikin qirjinsa,wani irin zafi radadi da quna,da zai iya yana kin fiddo da zuciyarshi zaiyi waje ya huta irin azabar da yake ji,bai taba sanin so da kishi masifa bane sai yau,baiyi tsammanin son da yake mata har yayi irin wanann girman ba,ya sani cewa yana ganin qimarta fiye da duk yadda yake ganin qimar wata diya mace a duniya idan ka dauke maminsa,tana da wani girma na daban a idaniyarsa da zuciyarsa ma baki daya,wannan ne karo na farko da tunda yazo duniya kishinsa kan wata diya mace ya motsa,shi kansa baiyi zaton kishinsa ya kai haka ba,duk da agefe guda qoqarin goge firman laifin da ta yi masa yake ta faman yi saidai ina zuciyar taqi aminta,idanuwan su gaza daina hango masa maryamunsa tsaye da wani