ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

batasan gurin da ya tsaya ba tare suka taho daga rafin malam dogo amma sai gashi har ta shigo gidan sukayi sallar magariba da isha bai shigowa ba,sai bayan isha’i ya shigo bai kuma tsaya ba kanshi tsaye ya shigo dakin dama kuma bai tadda inna wuro ba a tsakar gida ta ahiga daki dauko kayan kadinta

Jikinta gaba daya a sanyaye take,wani saahen na zuciyarta na ganin wane laifi tayi ba ita ta kira ahmad ba kuma ta riga da ta gaya masa tare suke,Allah kuma shaida ne bada wani abu ta kula shi ba,gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu
wannan tunanin ya qarfafa mata gwiwa tana tsaye a gabanshin tace
”abdallah”
”abdallah”shiru taji tamkar ba da shi take ba
”abdallah ga abincinka,ina ka tsaya na ahigo inna wuro tana tambayata inda ka tsaya sai qarya na mata,me yake damunka ne?”
shiru nan ma taji
”na zuba maka tuwo ne inna ta…..”
dagowar da yayi ya sanyata ja da baya zuciyarta na bugun uku uku,wani irin birkicewa ta ga idanunshi sunyi,wani matsanancin tashin hankali take hangowa qarar cikin idanunshi,farar fuskarshi ta hada ja kamar wanda aka mammara

Ga mamakinta sai taga ya saki murmushi yana fadin
”na gode da abinci,amma bazan iya ci ba”ya maida kansa qas kamar yadda tazo ta taras da shi,ajiyar zuciya ta sauke cikin,mutuwar jiki ta sake dawowa gabanshi ta duqa tana mai janyo kwanunkan
”dazun da rana baka ci abinci ba,bazai yiwu yanzun ma kace ba zaka ci ba”ta fara zuba masa kana ta miqa masa

Sake kallonta yayi,wannan karon raunin dake tattare da idanun abdallahn yafi na dazu,ita kanta sai da abun ya taba ta,irin raunin da ko sanda lalura ta sameshi bata gani,cikin idanunshi ba,murmushin ya kuma yi kana yace
”haqiqa Allah na iua jarabtar bawanshi ta kowanne fanni da yaga dama,ban yarda cewa ni abdallah cikakken maraya bane sai yau,na rasa mahaifina na rasa soyayyar mahaifiyata haka na rasa soyayyar macen da na riga nayi amanna cewa zata zauna da ni a duk yadda nake ko kuma nazo mata,saidai tunani na ashe kuskure ne?,duk da bai kamata naga laifinki ba maryam baki rufeni ba,kin gayamin baki sona bani kike so ba amma na gaza cika miki muradinki na rabuwa da alaqaqai abdallah,baqinciki na daya maryam igiyar aure na da aka hau kan martabarta aka tuburbudawa qasa,na yaba miki kuma ina kan yaba miki kan namijin qoqarin da kika yi kike kuma kan yi na bawa,rayuwata kariya,haqiqa bani da abunda zan iya biyanki da shi,na miki kuma alqawarin da zarar na samu lafiya zan cika miki burinki na rabuwa da ni,kici gaba da yimin alfarma zama da ni kada wasu su fuskanci wani abu,na miki alqawarin daina saki yimin duk wata wahala,kidai ci gaba da zama da ni din har na samu lpy idan da rabon haka ni kuma na baki ‘yancinki da kike da muradi”

Hakanan taji maganar ta daki zuciyarta sosai,tayi yinqurin duban qwayar idanunsa saidai ta kasa tilas tayi maganar tana kallan wani gurin daban
”yanzu me nayi maka haka da kake gayamin wadan nan maganganun,duka mai ya taso da su?idan maganar ahmad kake ni babu komai tsakani na da shi hasalima zuwa yayi ku gaisa”
ambatar sunanshi shi ya dago hasalar da yaketa qoqarin dannewa,cikin tsawa yace
”ahmad yake ko watever ba ruwa na da shi,ba maganarsa muke ba anan,magan ce tsakanin na da ke,don kin kula shi kun saba har kunsan juna wannan tsakaninku ne,igiyar aure na nada qima da mutunci a wajena tunda na biya sadaki,ni ba ragon namiji bane tun fil’azar jarabtar da Allah yayimin bazata zama silar zamowa na rago ba,kin cancanci kiyi hakan don a yanzun kinfi qarfin abdallah nakasashshe,sai cikakken namiji mai lafiya ba irina ba,saidai ki sani,har yanzu igiya ta na kanki so kiyi respecting dinta,sannan a hakan na tabbata nima akwai masu sona wadanda zasu iya zama da ni duk yadda nake”
sai ta qarasa gigicewa baki daya,kamar zata shide da jin fassarar da ya mata,kanshi tayo gaba daya tuni idanunta sun fara fidda ruwan hawaye,da sauri ya dakatar da ita
”kada ki cemin komai,bana buqatar naji komai”daga haka ya danna gefan keken ya soma yunqurin ficewa daga dakin,wani irin kuka ta saki ta fada saman katifa bai dakata ba har ya fice daga dakin

tana iya jiyoshi shi da inna wuro suna hirarsu abinsu tamkar babu komai cikin zuciyarsa,yayi qoqari matuqa wajen kawar da duk wata damuwa da yake jin tana taso masa
”bawan Allah in sha Allahu jibi tsoho alhaji zai dawo daga qasa mai tsarki,da izinin Allah kasa rqn warkewarka nan kusa”a fuska ya nuna jin dadinsa sosai,amma farincikin da yake sa ran ji duk lokacin da aka gaya masa tsoho alhaji zai dawo sam baiji shi ba,bai san dalili ba,amma yana zaton hakan baya rasa nasaba da abinda zuciyarsa ke gaya masa na cewa yana warkewa rabuwarsa da maryam tazo

Shigowar musatafa kenan abdallah ya maida shi yace yake ya kira masa mairo,babu jinkiri ya fice kuwa,ya dubi inna wuro yana fadin
”sam yarinyar nan ta daina shigowa inna ko ta miki wani laifi ne?”
kai ta kada
”a’ah a’ah,ni,babu abinda ya hadamu,abinda na lura kawai tana wasan buya ne da maryamu,ban sani ba ko ita ta yiwa laifin”karon farko amsar dalilin wasan buyab ya fado zuciyarsa,tana kwancen ta jiyosu batasan dalili ba sai taji ruwan hawayenta ya dadu ta sake qunshe kanta cikin filo hawayen na sauka qamshin turaren abdallah da ya kama katifar na ratsa qofofin hancinta,cikin sakanni ya haifar mata da wani baqon yanayi cikin zuciya da gangar jikinta

duban inna wuro yayi yace
”inna”
”na’am bawan Allah”ta amsa masa bayan ta dubeshi tana ci gaba da kadin
”magana nakeson muyi da ke inna ta fahimta”sai ta ajjiye abinda takeyi din tq bashi dukkan hankalinta”uhmmm ina saurarenka”
”inna na daukeki tamkar kakata haka nake jinki had zuciyata akwai maganar da nakeson gaya miki tuntini”sai ya matsa gefan kekensa take ya qara matsawa da shi gaban innar kadan sanann cikin qasa da murya ya fara mata maganar

lokacin da taji sallamad meron sai da taji wata faduwar gaba,haka siddan ta kasa zama sai ta miqe ta yaye labulen window din dakin,shi abdallah yake fuskanta don haka ta sake lafewa sosai don kada ya hangota

Tare da mustafa suka shigo,tana ido biyu da abadallah ta fara sussunne kai cikin duqunqunan nan hijabinta,inna wuron ce ta dubeta
”au,to kuma meye hakan,wa kike kunya ne?kinga bani na kiraki ba dama tunda kin gujeni kinga mai kiran naki”
gaban abdallah tazo ta zauna kana ta gaida shi
”bani amsawa tunda bamusan laifin da muka yi miki ba kika gujemu”
qara dunqule kanta tayi guri guda wani dadi ya rikito mata kamar ta tashi tayi rawa
”ni dai babu komai”haka ta fada,abdallahn ne ke janta da hira abunka da gwanar surutu tuni ta saki jikinta suka fada hirarsu,daga bisani maryam taga inna wuro ta tattre kayanta ta shige daki ta barsu

qasa qasa suka koma magan ta yadda bzata iya jiyosu ba,sai fuskar mero da ta gani ta fadada ta fara’a tana sake boye kanta,ji tayi ta soma jin juwa juwa sabida haka ta saki labulen ta koma kan sofa tana dafe da qirjinta
”kada ki jawomina bunda bazan iya ba,kada kimin irin wannan rashin adalcin,ki rabu da abdallah bai dace da ni ba,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,abdallah ba mate dina bane”abibda ta ringa fada kenan qasa qasa wani hawaye mai zafi na bin kuncinta

tun tana duba agogo har ta haqura,sai da ya buga qarfe sha daya daidai har ya dora da mintina sannan ta sake jiyo muryarsu
”ki tabbatar gobe tare zamu fita rafi dake kinyi alqawari?”kai ta gyada kamin tace
”eh nayi alqawari”
shima kan ya jinjina
”to shikenan sai da safe goodnight sweet dream”duk da bata fuskanci mai yace ba sai ta saki dariya tana waiwayensa har ta fice

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button