ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????

Ranar wunin gaba daya akanta ta qare tana zaune qofar gidan ta tasa uban ruwan dake ambaliya agabanta,tun tana zuba ido taga ta inda jirgin agajin su nene zai dira har ta sare baki daya,ta sake laluba wayarta da niyyar kunnata ko zata iya kira saidai sama ko qasa ta nemi wayar ta rasa,wasa wasa ta miqe ta hau zazzage zazzage saidai ko qyallin kalarta bata hango na,abu kamar wasa sai da ta zazzage dukkan akwatunanta amma babu ita babu alamarta,dariya taji ana qyqyata mata ta dago kanta da sauri,malam na hayi ta gano yana keta ruwan yana takashi da qafafunsa tamkar wanda yake kan tsandauri ba ruwa ba,ya qaraso gabanta ya ya daga hannunshi sai ga wayar
”duk abinda kike aiwatarwa yau na sani,kina tsammanin kubuta daha hannu na ne?,to kinzo gidan da idan aka shiga saidai a fidda gawarka,ina jinku habiba ta baki labarin abunda ya faru da ita ko?,wato wanna bai zamamiki izina ba ke yar masu taurin kai,bari na baki shawara qwaya daya a taqaice,ki fidda sa dan komawarki gida muna tare mutu ka raba,koda yan uwanki ma sunzo basu isa su gane hanya ba haka zasu qaraci walagiginsu su koma,mune maganin makwadaitan mata irinku masu butulcewa hanyar Allah,kunqi Allah muma munqi shi kinga kenan mu muka fi dacewa da ku,kin riga da kin zama matar malam na hayi na zama mijinki”

cikin zafi ta bude bakinta da niyyar yaba mishi rashin kunya,bakinta cike yake fal da maganganu masu zafi da takeson ta gaya masa,raahin mutunci ta nado mai uawa zata masa wanda tana tsammanin tunda yazo duniya ba’a taba yi masa makamancinsa ba,da saurinsa ya daga hannunshi na hagu take bakinta ya rufe qam
”daga yau ba zaki sake magana ba sai idan na baki izini ko naso,ba zaki sake min musu ba ko wani ma ba ni ba”kai kawai take gyada masa kamar bawa da ubangidansa
”wuce ki tafi dakinki,daga gobe zaki amshi girki,yau na daga miki qafa kiyi jimamin rabuwa da gida irin na amare iya na yau kawai”nan ma kai ta gyada masa ba tare da tace komai ba ta tsugunna zata kwaahe akwatunta
”shiga ciki kawai,kafin ki isa su sun riga ki isa”nan ma kai ta gyada kana ta juya sum sum sum ta shige cikin gidan,ya isa gaban kayan ya dafa su take suka bace a gun bat,wata magaukaciyar dariya ya saki yaba yiwa kansa kirari kala kala,sai kuma ya dinke fuskarsa cikin yan sakanni tamkar bai taba dariyar ba ya juya ya shige cikin gidan

????????????????????????

Su biyu ne ita da inna wuron zaune qarqash bishiyar lalle take kwabawa innan wanda zata saka a qafarta saboda dawiqar tsoho alhaji gobe daga qasa mai tsarki,har mamakin tsohuwar take bata ganin tsufan kanta ko na mijinta,adonta take daidai shekarubta wanda zai burge mijinta,dazu ta saka sabulu mai qamshi ta wanke kanta tas tace maryam din zata yi mata kitso

Tun kafin ta dago ta jiyo muryoyinsu,gabanta ya soma faduwa don ko kusa ko alqma bata sha’awad ta bude ido taga yarinyar,haka suka shigo cikin gidan tana tura wheelchair din suna hira abinsu,tunda ta dago kanta suka hda ido da abdallah ta dauke kai bata sake marmain kallonsu ba,miqewa tayi tsam ta isa bakin rijiya ta wanke hannunta sai tayi shigewarta daki duk da ba wani abun zatayi cikin dakin ba,tsaye tayi tana jin uadda suke hirarsu su ukun sun ma maisheta tamkar wata bare,kada ma abdallah yaji labari wanda a a yanzun ya koyi zuwa masallaci daga nan idan yaga damq yayi zamansa qofar gidan nenen suyita hira da samarin qauyen,idan kuwa ya tashi dawowa to mawuyacibe ka ganshi ya dawo shi kadai ba tare da mero ba,duk yadda taso danne zuciyarta da hanata jin kishin abdallah abun ya faskara yafi qarfinta,daga qarshe ta yiwa kanta hukunci ta yarda tana kishin abdallah saboda amanarsa da mami ta barta amma ba wai don so ba

Ko daya bata ji shigowarsa ba sai gyaran murya da ta ji a bayanta,ta dan waiwayo da sauri wanda hakan kadai ya isa ya gaya maka tunani takeyi
”excuse me madam”ya fada yana nuna mata hanyar da zai wuce din ba tare da ya kalli fuskarta ba
sai ta janye gefe ta zauna saman kujera ya qaraso ya wuce bangon dakin inda laptop dinshi ke ajjiye,tayi qasa da yawa hannunsa bazai iya kaiwa ba,tayi zaton wannan karon zai nemi taimakonta sabida gaba daya yanzun duk abinda hannunshi zai iya da kansa yake yi,ta manta yaushe rabon da ya sata wani abu,ko kwanciya ce ko dorashi saman kujerarsa mustafa ke taimaka masa

Bata ankara ba taji yana kiran mero,cikin rawar jiki ta qaraso dakin ganin maryam sai jikinta ya mutu kuma,ta soma rabe rabe
”shigo mana,wancan computer din zaki dauka min da ita zamu tafi saboda hoto ko?”sai ta washe haqoranta ta rave maryam ta wuce ta dauko conputer tana qare mata kallo din ba qaramin burgeta tayi ba ta miqa masa suka fice a dakin,wani dubqulallen abu ne ya tokare mata wuta ya hanata ta hadiyi koda yawu ne,tana jiyo su suna yiwa inna wuro sallama sun tafi rafi sai kawai ta qarasa zamewa ta kwanta gaba daya kan kujerar tana hawaye sosai

”meramu fito,ki saka min lallen nan mana,so nake na cireshi kafin mangariba ki kitse min kan nan,don malam alhaji saukar hantsi zaiyi”ta jiyo inna wuro tana fada,da zata iya da ta cewa inna wuron ba zata iya fitowa ba ta saka da kanta,tilas ta miqe ta goge fuskarta bayan ta sake saka kwalli duk don kada innar ta gane ta fito

tana kan tabarma lallen na gefanta,kallo daya ta yiwa maryamun ta maida kanta kan kwanon lallenta ba tare da tace mata komai ba,tun inna wuron na sako hira taga maryam din bata karbarta hannu biyu itama sai taja bakinta ta tsuke suka ci gaba da zaman kurame,duk yadda taso ta hana qwallar fita hakan ya faskar,haka ta dinga sulalowa tana sa gefan dankwalinta cikin dabara tana gogewa
”hmmmm,duniya kenan,Allah yana baka kana bana so,ba shikenan ba,garin kallon ruwa dama kwado kema mutum qafa,dana dam kuma dama ai butulcinsa yawa gareshi”shiru tayi gana jujjuya maganganun inna wuron cikin qwaqwalwarta masu zubi da gugar zana,sai tayi ta maza don kada ta gano kuka take ta tambayeta kanta na duqe kan qafar inna wuron da take sawa lallen
”lafiya inna,wani abu ne ya faru?”
tabe baki tayi ya kau da kanta
”a’ah a’ah,babu abinda ya faru,Allah dai ya rufa asiri,amma shi aure komai lalacewarsa ai aure ne,yafi gaban ace za’ayi shakulaton bangaro da shi”
”hakane”maryam din ta fada tana ci gaba da abunda take,wani takaici ya kama inna wuron har taja qwafa duk da yadda taso daurewa

bayan ta gama sa mata sai taja gefe,gani,zaman shirun ya,isa don innar bata sake tanka mata ba sai ta jawo kwanon lallen wanda yayi ragowa ta qunsa a yatsunta na qafa da hannu
daf da kiran sallar magariba suka cire duka ita da innar,yatsun sunyi kyau kam,lallen ya kama ram da shi gwanin sha’awa

tana gama daura alwala taji sallamarsa,wanann karon ma sai da gabanta ya fadin,idanunta ya sauka kan mero dake riqe da laptop dina abdallah taba ta shafawa bakin nan kamar gonar auduga,har uanzu jan jambakin data sanya kan ta kile yana nan radam baje baje kan bakinta,ta sake saura dankwalinta sai ta shige kawai dakinsu don ta tabbata zaman hirar,nan zasuyi,hirar da ayanzu babu abinda ta tsana kamar ta

Tana shiga ta shimfida abun salla ta tayar da sallar,ko bayan ta idar zamanta tayi kan daddumar bakinta cike da addu’o’i wadanda suk riga da sun zame mata jiki,a kunnenta abdallah ya fita sallah ya dawo,inna wuro tayi kiranta ta fito taci abinci to tace mata har suka kammala bata fito din ba saboda tana jiyo muryar mero

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button