ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

amina maca ce mai matuqar haquri da kawaici tsantsar kyau nafulanin usuli,hakan yasa take da farinjinin samari da dama wanda hakan ya kusa haifar da rigima cikin qauyen nasu,dalili kenan da yasa babanta yayi saurin aurar da ita ga mahmuda dan maqocinsa wanda duka cikin samarin nata dama tafi karkata gashi,kasancewarsa shine kadai mai ilimin primary a cikinsu,amina maca ce maison karatu matuqa da gaske saidi a lokacin lokaci ne da ake qamatar karatin boko hakanne yasa bata samu wannan damar ba shi yasa tayi kwadayin auren mahmud din

kusan shekara uku da auren nasu kafin Allah ya azurtasu da samun qaruwa,da namiji ta haifa saidai baizo da rai ba,sosai mamuda yayi takaici kasancewarsa mai son ‘ya’ya musamman maza,babu yadda ya iya haka ya haqura

bayan wannan haihuwar saida amina ta sake wata guda biyu duka maza kuma babu rai sai akan maryamu Allah ya tsaida mata,saidai wannan karon mahmuda baiyi wata murnar azo a gani ba kasancewar ba abunda yake so ba ya samu wato namiji,itakam amina hakan yayi mata dadi don a ganinta duka daya ne fatan dai Allah ya kawo mai albarka

bayan yaye maryam ta sake wata haihuwar macen itama babu rai a haka sai da ta haifi hudu dukkan ajajjere tsiran watanni ne ta kuma samun wani cikin duka dai basu zauna ba,lokacin ne mamuda yace ahikam aure zai qara,bata wani tada hankalinta ba tace ”Allah ya sanya alkhairi”
huwaila ya dauko wadda tunda tazo gidan ta fuskanci ba wani girmamawa yake wa amina ba,don haka ta tayashi takata,kusan tuni ya sakar mata duk wata ragamar kulawa da ta rataya tasu a kansa

Ba’a taba yiwa Allah dole,hakan ce ta faru ga mamuda domin huwailan ma da ya qwallafa rai a kanta haihuwarta ta fari da mace ta fara,a haka ahaka saida ta tara yara shida duka mata,ganin ita din ma babu biyan buqata sai ya tafi ya auro hadiza ya kuma zubar da lamarin huwaila kamar yada ya yowa aminatu

to ita din ma hadizan bata sake zani ba,matan ne dai sai da ta haifo bakwai sai daga qarahe ne Allah ya kawo namijin wato ISHAQ da suke kira isyaku,sunan mahaifin mamudan ne,to fa,babu zama wai an saci dan barawo,nan fa hadiza aka shiga daga kai an haifi namiji,rashin mutunci babu kalar da bata shukawa cikin gidan,hakkane yasa huwaila boye kishinta ta shige jam’iyyar hadizan suke gallazawa aminatu baiwar Allah wadda a lokacin ta sake samun qaeuwar diya mace shekarunta takwas kenan

Rayuwa tayi da rayuwa,yau da gobe kayan Allah,babu da talauci ta ishi jama’a hakan ce ta sauka gidan malam mamuda,ya taraau ya sanar da su cewa saidai fa kowacce tayi haquri da abunda zat gani don gaskiya bai da abun ci da su,ranar da ya samu ya bayar a dafa,ranar da babu kowa ya ci da kanshi,to dama ko can baya ba abinda yake masu,abinci ne zai baki kudin awo ranar cefanenki sai makaranta mai sauqin kudi ya sanya yaran ita din ma don ya dan san dadin ilimin kadan,to sai kuma salla salla ya dinkawa kowa kala daidai dama maryamu bata cikin duka wani budget nasa,idan akayi magana sai yace ai ita babbace ta dauki girma daga haka babu dadi babu ragi

huwaila da hadiza sukayi tsallen albarka suka ce sukam ba zasu iya ba,dukkan yaran nasu suka fidda su daga makaranta suka hau yin sana’a suna dora musu talla,to yaya lafiyar kura balle tayi hauka,dama can ba tarbiyya yaran suka cika ba balle yanzun da suka zama ‘yan talla,tashin kunya kule kule kulen maza da diban albarka kala kala,tun malam mamuda nayin magana har sai ya saka ido,don bashi da ikon yayi maganar sai gori

kisan hadiza ce ke juya malam mamuda itace mowar mata sakamakon haifar masa namiji da tayi,duk abinda isiyaku ya fada kam baya qarya,sai ya zamanto aminatu baiwar Allah da yaranta sun zama yan kallo cikin gidan,duk da itama huwailar na baqincikin yadda hadiza ke yadda taga dama amma tilas ta bunne cikin zuciyarta don samun damar cin arziqin samun ‘yanci a gidan

Amina cire yaranta tayi ta maidasu ta gwamnati,da yan kudaden hannunta tayi masu dukkan abinda ya kamata,ko dama can ita din ba mace ce mai matacciyar zuciya ba,ba’a rabata da ‘yan sana’o’i,sune kuwa auka zama marufar asirinta,ita ce kitso,daka,wanki,’yan qulle qullensu kuka daddawa kubewa su lalle ne,da sauransu,da su take samu ake gurgura rayuwar da dadi babu dadi

lokacin da maryamu ta kammala primary taci common entrance G.G.S.C duka wuya ta samu dake qofar famfo,wanda yayi daidai da fitowar manema wa yaransu hadiza wato SHEMA’U,HARIRA FURERA DA RABI,uku yaran huwaila ne daya ce ta hadiza,dukkaninsu basu wuce sha biyu ba sha uku sha hudu,tsabar son aure ne da suka saka aransu ya sasu zama dika dika,ba bata lokaci kuwa aka sa musu ranar aure,malam mamuda ya samu amina da auke kira mama ya sanar mata zai hada ne harda maryamu ya airar da su gaba daya,tunda su gasu qannenta ma sun fidda miji

cikin ladabi da son fahimtarwa tace”amma malam ni a ganina dukkaninsu basu yi girman da za’a aurar da su ba,yanzu haka ita kanta maryamun bata kai sha biuar ba bare su,ba zata fi sha hudu ba gaba daya,ni a nawa ra’ayin malam nafison maryamu tayi karatu,idan ta qara girma tasan ciwon kanta sai a aurar da ita”
wannan abun ya qullata yace indai bata yarda an aurar da ita ba to babu ashi babu duk wani shirgi nasu,bata damu ba don dama can ba wani abu yake musu ba

tofa,wanna ya sake hura wutar tsanar da sukayiwa maryam wanda dama tun suna qanana aka horesu da ita,don ko wasa bata isa ta shiga cikinsu tayi ba,gashi lokacin bata da ‘yar uwa don ba’a haifi hindatu ba alokacin,bugu da qari,kyau da Allah ya bata fiye da duk wata yarinya dake cikin gidan,duk da suma Allah ya basu nasu kyan babu laifi saboda mahaifinsu malam mamuda kyakkyawan bafulatani ne

Allah yayi maryam mai hazaqa da qwaqwalwa,tana da matuqar son karatu,haknne yasa bata yadda ta kula kowanne saurayi wanda su kuma suka fassara hakan da cewa girman kai ne kurum don tana ganin ita kyakkyawa ce,cikin zuciharta ita din tasan ba haka bane tunda ba haka take din ba azahirance

maryam doguwar mace ce wadda Allah ya yiwa baiwar diri da structite na jiki duk da tsahonta hakan bai boye kyawun zubinta ba,fara ce amma ba tas ba,idan kaso ma zaka iya kiranta da ja,don irin farin nan ne mai cakude da ja,gashinta sosai irin na fulani mai laushi da santsi,zara zaran gashin ido da na gira da madaidaicin baki,dimple dinta hagu da dama wanda ko magana murmushi tayi sai ya lotsa,hancinta ba mai tsani ba tafe yake da tsohonsa da kuma tudu,idanunta irin idon nan ne da ake cewa oily eyes wanda zakayi tsammanin qwalla ko ruwa ne suka taru cikin qwayar idon,bata da baqin qwayar ido sosai,sanyin muryarta da zaqinta ke dada bayyana kyawun halittar da Allah yayi mata wanda hakan ya ja mata yawan masoya da maqiya ciki harda ‘yan gidansu

haka aka sha bikin yan uwan nata su hudu yayin da ita kuma ta duqufa karatunta,maryam badai qwaqwalwa ba,hakan ne ma yasa bata samu cikas ko ksdan a karatunta ba,cikin nasara komai ke tafiyar mata,janye jiki da masoyanta sukayi a lokacin bai dameta ba don dama bata buqatar wani damuwa karatunta ne kawai damuwarta,cikin nasara ta shige B U K inda anan ta samu shaidar degree dinta kan fannin girke girke

ba jimawa,da kammalawa kuwa ta samu aiki da wani katafaren gurin cin abinci da shirya bukukuwa ,wanda cikin qanqanin lokaco ta samu matsayi mai girma na shugabantar dukka masu girka wani abunda za’aci ko a gurin ko kuma aka basu kwangilar yi na biki,qwazo himma gaskiya da amana su suka jawa maryamua wannan matsayin wanda hatta da wadda ta kafa gurin HAJIYA ATIKA ABUBAKAR BAFFA ke qaunarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button