ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”To banga abun damuwa ba don nayi aiki da hudubarki,kyan da dama…..ya gaji uwarsa,sai haduwa ta gaba nene”
ya fada yana shirin barin dakin
”wallhi adnan idan ka sake ka tafi min da dukiya sai na tsine maka albarka,butulcin da zaka yimin kenan matsouaciyacin yaro?”dariya ya sheqe da ita kana yace
”kin dade baki tsinemin ba nene,kinga idan ma kinso a sama miki lasifiqa a abaki duro ki hau kiyita gayawa duniya kin tsinewa adnan damuwarki ce,nidai na debe kasona don na gaji da gafara sa banqo qaho ba,idan na gurin abdallah ya samu kya iya kirana muci tare,byeeee”ya fada yana daga mata hannu tare da sake rungume jakar da ya lodawa duk wata kadara ta nenen yana fucewa adakin
ihun barawo take ta faman zabga masa saidai a banza don babu kowa cikin gidan idan ba security dake bakin aikinsu ba,su kuwa sunsan babu kowa cikin gidan daga ita sai danta don haka basu kulaa ba domin suna tsammanin ciwonta ne ya tashi wanda dukkansu sun dauka ciwon hauka ne ya sameta
hakanan ta qaraci ihunta ta fashe da kuka mai cin rai tana tsinewa adnan mummunan tsinuwa a haka zubaida ta tadda ra,koda ta gama mata bayani dogon numfashi ta ja tana fadin
”tabdijan,nice zan tashi a tutar babu,wannan wace iriyar magana ce ma mara dadin ji,to wallahi bazan zauna da kyau na da komai ba rayuwa ta ta qare a tantal bataiti ba,a banza wancan tsinannen mai qirar sanudawa yazo yayi awon gaba da ni ko ya kasheni,gwara tun yanzu na samawa kaina mafita,zuwa zanyi na cire cikin nan na shiga sabuwar rayuwa,ga masoya ina sa su masu yawan gaske masu kudi na gani a fada,gwara naje wlh na yagi rabona nima na kafa kaina”tana gama fadar haka ta haura gadon ta fara cire dan kunnen gwal dake kunnen nenen mai hade da banguls da zobensu wanda ta tabbata adnan bai kula da su bane,domin da ya kula da su babu abinda zai hanashi yin hauzi da su kamar yadda yayi da wadancan
”au kema zubaida haka zakiyi min,ashe dukkanku matsiyata ne,yayana na cikina babu mai tausayi na kune masu rusani?”’tsayawa tayi cak tana kallonta
”tab lallai ma nene,ke don Allah baki ji kunyar kanki ba?adnan ma yayi miki haka ballanta na ni?”
”yanzu don adnan ya yimin haka kema sai ki biye masa?”
”hmmm,sai kuma kiyi,ina ga kin dade baki bata yawun bakinki ba,ai tunda kika ahiga tsakani na da abdallah kika min asirin da aka ciren sonsa to wlh babu ni babu aure,rayuwar bariki ta fiyemin inda zan zuba jarin jikina na samu kudi”tana fadan haka tana sabule da lalube duk wani abu da yayi saura wanda adnan bai kai ga daukewa ba,cikin haka tayi katari da takardar wani gida ta dauke abinta,tana jin nenen na qwala mata kira har ta koma rsine mata itama amma kallon arziqi bata iaheta ba tayi gaba abinta,don ta riga ta sani uwar tasu ba imani gareta don me ita zataji tausayinta kuma?,ai raba arne da makami ibada ne
A ranar bata bari ta kwanan ba ta hada ya nata ya nata ta nufi gidan wata aminiyarta da ta jima tana mata hudubar shaidan kan cewa ta mori kyanta wlh ta qyale wani abdallah ta tsaya ta nace masa yana wulaqantata bayan ga samari nan da alhazawa na sonta ido rufe
????????????????????????
Duka hidimar ranar ita ta karbeta don inna wuro da abdallah na gurin tsoho alhaji wanda ya sauka qasa nijeria da misalin sha biyu na rana,tayi mamakin ganin hisham shima ya iso a ranar
”ina sane da ranar dawowar tsoho alhaji a lissafe nake maryam,abdallah na raina da shi nake kwana da shi nake tashi ko yaushe”qwarai ta gasgata hakan tunda gashi taga zahiri
Gidan kusan a cike yake da yan sannu da zuwa wanda basu samu sararawar mutanen ba sai bayan sallar la’asar
Tsoho alhaji wanda asalin sunanshi muhammdu dattijo ne mai cikar kamala da nutsuwa,dattijo ne da ya amsa sunan dattijo bawai muna dattijo ba,dattijo ne da kallo daya zaka masa kwarjininsa ya cika maka idanu,yadda matarsa inna wuro(fatima)ke da kirki haka shima yake
Murmushi ya saki har ya dan fidda sauti bayan ya kammal jin dukkan wasu bayanai daga bakin maryam da abdallah hisham harma da inna wuro daga dan abinda ta sani
”in sha Allahu da izinin Allah indai sammun ne bi’iznillah na bada gaskiya ga Allag nan da kwanki bakwai zaka miqe abdullahi ka taka qafafunka komai yazo qarshe,zan yabaki miki maryam kinyi namijin qoqari qwarai da gaske tunda wuro ta gayamin ba haka kuka zo ba,kamar yadda naji bayanai daga bakinki,na abubuwan da kika dinga nasa amfani da su,ayoyo yine masu kyau matuqa da gaske,gakanna masu tasiri qwarai da gaske wajen ruguza sihiri ko wanne iri ne bi’iznillahi ta’ala,yanzu akwai wasu magunguna da saiwayoyi da Allah ya horemin saninsu,yau basai gobe ba zan fara hadasu guri guda insha Allahu baka wuce kwana bakwai ka warke abdullahi kaci gaba da haquri wannan wata jarrabawa ce Allah ya maka don ya gani shin zaka gode masa ne ko zaka butulce masa?,a baya ya maka duk wata ni’ima ta dukiya kyau ilimi nasaba da gata a yanzu ya amshe abinsa yayi ne duka don ya jarabci imaninka,to alhamdulillah bisa dukkan alamu ka karbi duk wata jarrabawa daga gareshi kuma ina maka kyakkyawan fatan samun cikakken lada”
cike da girmamawa ya duqar da kansa
”na gode qwarai da gaske alhaji,Allah ya qara girma,Allah ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani”
haka hisham da maryam suka bi sahun tayashi godiya ga dattijon
Ya dubi inna wuro
”muje ki tayani duba kayan nan,don na san yanzu kin canza musu guri”bata ce komai ba ta miqe tabi bayansa
hannun hisham abdallah ya kama ya riqe
”ka taya ni murna abokina na kusa angwancewa”
dan satar kallon maryam yayi
”mtswee,har yau abdallah baka da kunya,ni kake wa irin wannan maganar?”
ya dubeshi a hagunce
”to akan me bazan maka ba?,rashin aure fa nasifa ne abokina ban sani ba sai yanzu”cikin rashin fahimta yake dubanshi
”like how,kana da mata kana kiran rashin aure a kanka?”
”neman wani auren nake cikin garin nan hisham na wata ‘yar fulani”
wani irin kallo hisham din yake masa
”kanka daya kuwa abdallah?,kana da mata kake cewa wani auren kake nema?”
”tunda anqi ka meye na cusa kai hisham don Allah fa,matar tace bata yi zaka mata dole ne?”ya fada qwayar idanunshi na sauya kala,da alamu abinda yake fada din na taba zuciyarshi
”kuma a shekaru na bazan iya zama babu mace ba,kai ka sani da din ma rakawa kawai akeyi”
duk da maganar ta taba hisham yaji wani iri amma maganar abdallahn ta qarshe taso bashi dariya kafin yace komai mero ta kwada sallama bakin qofar dakin wanda duka wunin yau bata shigo gidan ba sai yanzu
”yauwa shigo ga abokina zaku gaisa”inji abdallah yana duban hisham din
jin haka yasa ta dago labulan ta shigo kanta a qas alamun kunya,gefe ta rabe ta gaidasu su duka banda maryam da da qyar ta iya amsaqa can qasab maqoshi,kasa sakewa meron tayi ta miqe zata fita abdallan ya tambayeta ina zuwa tace zata yiwa tsoho alhaji ne barka da dawowa
”idan kin masan ki dawo ina son ganinki”inji shi ta gyada kana ta fice hisham ya bita da kallo,sai da ta fice din baki daya kana ya dawo da kallonsa kan abdallah
”wannan kuma wace ce,yar fillo haka”murmushi ya saka irin mai hade nishadin nan yace
”daina saurin yabawa,itace wadda nake gaya maka ina neman aurenta a qauyen nan”
Wata guduma maryam taji ta sauka kan qirjinya,kanta da gangar jikinta sukayi mata nauyi gaba daya,a hankali ta soma fusgar numfashinya yana son qwace mata,sai ta miqe sama sama tana jiyo sa in sarsu shi da hisham,ganin tana niyyar fita ya sanya hisham kiranta,shi din ma sama sama take jin muryarshi don haka bata bi ta kansa ba ta lalubi hanya ta fice,ba kowa tsakar gidan kai tsaye dakin inna wuro ta shige,gadonta irin na qauye ne da ake kira gadon bunu mai rumfar shi ta haye,can qurya ta takure kanta tana jin wani abu na mata yawo cikin zuciyarta kuka take so tayi ko zata ji sanyi cikin zuciyarta,shin wannan shine kishin?,da gaske kishin abdallah take?sune tambayoyin data ringa jefawa kanta ta kuma takurawa kan nata sai ta fidda amsarsu