ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶5⃣3⃣
Daga Abu hurairah Allah ya qara ya yarda shi yace:Manzan Allah S A W bai taba aibata wani abinci ba ko kadan,idan ya burgeshi(abincin)sai yaci,idan bai masa(bai kwanta masa ba ko ba cimarsa bace)sai ya barshi (ba tare da ya aibata shi ba ko ya wulaqanta shi ba)
ina kuke ‘yan
huguma conversation and novels room
maman aysha hausa novels group
haske writers asso
*DA*
*Z.B.I*
bazan gaji da sadaukar muku da shafuka na ba,ina yabawa qwarai da qaunarku gareni,ina roqon Allah ya tashe mu qarqashin inuwarsa ranar gobe qiyama,ya bar mu tare bisa soyayya ta domin Allah????????????????
Sake lafewa tayi kan gadon inna wuron tana matse idanunta don fidda hawayen dake maqale cikinsu
tun tana jiyo maganganun mutane masu ahigowa jifa jifa yiwa tsoho alhaji barka da dawowa har jin nata ya dayke baki daya,wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita
Qaton fili ne dake malale da koiyar ciyawa wadda ake kira da grass carfet jifa jifa kuma jajayen furanni ne ke dashe ta tsakanin ciyawar
Iska mai dadi ke kada fingilar rigar dake jikinta wadda bata da nauyi ko kadan sai santsi,kamar yadda gashin kanta keta yawo tsakanin kafadarta da fuskarta,dauke take da faranti fari qal wanda akanshi kofuna ne fuda uku da jug tsakiyarsa wanda cike yake da madarar shanu,a hankaki take tafiya yana daga nesa cikin fararen kaya hannayensa harde a qirjinsa,dukkan wani hankali nashi da tunaninshi yana a akanta ne,kyakkyawan murmushinsa kadai ya sata mance a ina rake har ta qaraso gareshi,hannu yasa ya karbe farantin ya ajjiye a tsakiyarsu kana ya riqo hannunta
”maryama”
”na’am”ta amsa masa kanta a qasa
”maryam ki kalleni tun kafin na zauce”
ya fada qasa qasa yadda dagashi sai ita kadai zasu iya jin abinda yake fada,babu musu ta daga kanta idanunsu suka mannu da juna,kallon juna suka shiga yi babu qaqqautawa tamkar zasu hadiye junansu,kowanne na ganin zallar qauna qarar cikin idanun dan uwanshi
Shi yafara bude bakinsa
”maryam,kinsan yadda nakeji game da ke cikin zuciyata kuwa”ya fada yana tura hannunta cikin qirjinsa bayan ya balle maballan rigarsa,take tafin hannunta ya mannu da fatar qirjinsa dake cike da gashi
”kina iya jiyo bugun zuciyata a haka?”kai ta gyada masa tana murmushi don tana jin yadda zuciyar tasa kera fat fat fat da sauri
kai ya girgiza
”abinda kika ji yanzu baikai kaso daya cikin dari na yadda nakeji cikin zuciyata game da ke ba,idan da zan iya zuciyar zan ciro miki dungurun gun na ajjiye miki ita wata qila kya iya ganin kaso hamasin cikin darin abinda nake gaya miki,ragowar hamsin din sai ni da Allah”
qayataccen murmushi ta sakar masa tana sadda kanta qasa,da sauri yace
”dago ki kalleni da kyau maryamu na,kallon da kike min kawai na rage radadin da nake ji”bata musa din ba ta dago taci gaba da kallon nashi fuskarta dauke da murmushi
ya matso kusa da ita har suna gwaren numfashi
”i love d look in ur eyes maryam”murmushi ta kuma yi tana dan kawar da idanunta
”i luv ur smile,maryam ke ta musamman ce u make me feel safe nd secure,ban damu da duk wani abu da na rasa ba idan ka cire mami na matuqar ina tare da ke,i know u luv me 4 who am,pls maryam tell me kina sona…kina son abdallah”
idanunta ta lumshe kana ta bude tattausan labbanta
”abdallah”
”yes ina jinki”
”abdallah ina…..”
”umh comeon baby ina jinki”
”abdallah”
”na’ammmm”
sai taji amsawar ta qarahe tamkar ido biyu ne ba cikin mafarki ba,a hankali ta fara bude idanunta don tantance a inda take,yana zaune sosai kan kekenshi idanunsa akanta kamar wanda ya samu hoto,a firgice ta miqe ta zauna dirshan kan gadon innna wuron tana mutstsuka idanu
”me nayi miki da kika zo kina mafarki da ni?,kin daga mana hankali muna ta nemanki tun la’asar gaahi har magariba ta gota ana shirin yin isha’i ashe ke mafarkina na ma kika zo kina yi?”ya fada fuskaraa dauke da murmushi wanda sai ka kuka sosai zaka gane shi kwance kan fuskarshi
haushin kanta ya kamata,kunya da taoro suka dirar mata,kada dai ace kamata yayi tana ambatar sunansa,kai amma kam da ya gama da ita,duk da ba haske bane tarwai cikin dakin sai data harareshi
”waya damu da kai da zaiyi mafarkinka? kai kadaine mai sunan?”
hannayenshi ya ware na alamun ba ruwana
”bani na kar zomon ba,ratayar ma ba’a bani ba,kuma ni din ma na dade da sanin ba’a damu da ni ba,tsabar haushina ne yasa kike ambatar suna na cikin mafarki cikin yanayi ma shauqi ko?”ya tambaueta tana tsatstsareta da kallon nan nashi,bata san me zata ce masa ba duk da barazanar kare kanta da takeyi ba,sai kawai ya juya kekenshi zai fita yana dariya qasa qasa
”ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,na bada darasi abdallah ba rago bane,ki fadi abinda ke damunki idan ya kama taimako sai a taimaka miki”ya fice daga dakin,ba qaramin quluwa tayi ba,ya akayo ya sake ma ya kamata tana mafarkinsa,ta ciji yatsa tayi dana sanin ma yin barcin nan gaba daya,dole haka ta sauko daga gadon tazo ta wucesu suna zaune abinsu hisham tsoho alhaji inna wuro da abdallah,garwashi ne da wasu magunguna gaban tsoho alhajin wanda da alamu duka hade haden abdallah ne,taje ta dauro alwala tana jinshi yana basu labari
”gadonki taje ta naushe miki inna,taji laushin katifa tana ta mafarki barkatai,inaga alhaji sai ka bata magani ma don ina zaton akwai wani aljani abdullahi mai irin suna na da ya kamata”dariya ya basu yayin da ita kuma ta sake quluwa
ta daura alwalarta ta wuce dakin inna wuron ta tada sallarta
Cikin kwanakin gaba daya tayi qaura dakin inna wuro nan take kwana saboda hisham na gidan tare suke kwana da abdallan,iyakarta da tsakar gida ta fito ta taya inna wuro aikace aikace ta koma daki abunta,sam ta hana haduwar da abdallah duk cikin qoqarin tana hana kanta jin duk wani feelings dake barazanar kamata,kusan tayi a banza tunda ko shi bai ganta ba ita tana ganin giftawarsa ko ta jiyo muryarsa shi da su tsoho alhaji wanda ya duqufa ka’in da na’in wajen magungunan abdallah wanda alhmdlh cikin jikinsa yan jin wani irin sakewa da sukuni
Ko daya inna wuro bata ce mata uffan ba kan zaman daki data aura,sai ta tuqe kana zakaji tace
”ummm,Allah ya kyauta,kowa dai ya debo da zafi bakinsa”ta fuskanci sarai da ita take
cikon kwana na ukun tana kwance kan qaramin gadon inna wuron misalin uku na yammaci da littafin riyadul jannah a hannunta tana dubawa,yaye labulen inna wuron tayi tana fadin
”ki tashi kije ki gyara dakinsu hashimu,shida malam sun fita bayan gari debo ganye,amma fa idan zaki iya(da yake haka innan ke kiransa)”
ta fuskanci kamar da zafin ta innar ta fada,bata ce mata komai ba ta ajjiye littafin gefan gadon bayan ta saka alama,hijabinta ta,ciro ta ware ta saka kana ta fice innan ta bita da kallo tana tabe baki
”Allah dai ya sawwaqewa matan maraya wallahi”ta jita amma bata tanka ba
tsaye tayi a bakin qofar dakin zuciyarta na wani irin bugawa,kamar ta juya ta koma haka ta dinga ji,fargabar shiga takeji,jin motsin futowar inna wuro daga daki ya sanyata yin saurin daga labulen ta fada dakin tare da sallama idanunta a qasa
kan kujerar dakin wannan karon ta tadda shi zaune,yayi kyau cikin baqar rigar jallabiyya data haska fatarshi,a haka sai kayi tsammanin lafiyanshi qalau saboda kyan da yayi,ganinshin da batayi ba kwana biyu sai taga kamar an canza shi ne,wayarshi ce a hannunshi yana danne danne,da alama wani muhimmin abu yakeyi,amsa mata yayi kallon farko kadai yayi mata yaci gaba da abunda yake kamar bai santa ba
tana kallon kan katifar da kaya ke baje a aki da sauran tarkace tace
”zan danyi gayaran daki ne”
”oh,na bayar baki gidan ne har nasa a gayara din ma”
wani abu ya dan taba ranta sai tayi shiru wanda hakan yasanya ya dago kai ya saci kallonta
qasa qasa taji yace
”if u luv some one be sure to hold them close,if u don’t some one else will”