ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”me kace?”ta fada cikin son nuna mishi bata ji abinda ya fada din ba
”no,ba dake nake ba,bismillah”ya fada yana ci gaba da abinda yake yi
katifar ta soma kintsawa,tana aikin amma jikinta na gaya mata kallonta yake,batayi qarya ba don gaba daya ya bar hankalinshi daga kan wayar ya maida kanta,duk wani motsi nata na kan idonshi,cikin zuciyarsa hakanan yaji tana burgeshi,bai taba zaton zai samu macen da zaiso ta wofantar da soyayyarshi ba,bil haqqi da gaskiya take son nuna masa iyakarsa

Wannan karon duk yadda yaso kauda idonshi kada ta kamashi yana kallonta abun ya faskara sai da suka hada ido,kamar kuma an manne idon ya kasa daukewa,ta juya ga zatonta zai daina kallonta amma sai taga yaci gaba,bata rai tayi
”gabana faduwa yake idan aka fiya samun na mujiya”murmushi ya sake yana janyo laptop dake gefansa
”ayyah am sorry”ya fada yana kunna system,bayan ta saitu ya shiga gun hotuna ya bude daya daga cikin hotunan ciki

Gefanshi taje zata dauke abun sallar dake shimfide a gun idanunta ya kai kan system din,hoton mero ne ya cika screen wanda da alama shi abdallah yake kalla
batasan ta fincike laptop din a hannunshi ba saida ya dago ya zuba mata idanunshi
”me kuma nayi?,ai na daina kallon naki ko?”ya fada a shagwabe kamar qaramin yaro
bata kula shi ba saida tayo shutting down fuska a hade cikin zuciyarta a tsinke tace
”saika tsagaita na gama gyara na tukun,baxaiyiwu ina gyaran kaya ana min janye janyen wani shirgin ba”ta fada tana canzawa computer mazauni nesa da shi
idan banda jarumtae daya aro ya tabbatar babu abinda zai hanashi fashewa da dariya

sai ya wayance da dora hannunsa guda daya kan tattausan sumarshi
”oh Allah na,mami na kin barni gashi ana nan ana gara miki ni”
shi da yayi maganar da ita kanta sai maganar ta soki zuciyarsu,tabbas ba kadan ba sukayi rashi da kewar uwa ta gari irin mamin

????????????????????????

Sosai ta qaranta baccinta don tayi imanin babu masifar da addu’a bata da maganinta,tana samun nutsuwa qwarai da gaske saidai gaba daya hankalinta ya karkata ga abdallah da maryam

yammacin ranar lahadi tana gida bayan ta kira baba uwaani,su biyu ne cikin parlour din,a yanzun kam da baya ga ‘yan uwanta baaba uwani ce ta biyu wadda take shawara da ita
”amma hajiya tunanin da nayi,ba zamu zauna bamusan inda suke ba,mai zai hana mu nemi gidansu maryam ko suna da labarin inda suke?”
cike da gamsuwa mami ke gyada kai
”qwarai da gaske baaba,wannan shawara ce mai kyau,amma cikin ni da ke babu wanda yasan gidansu maryamu tunda a lokacin bikinta bamu samu damar zuwa ba tunda ya hade da na abdallah”
”eh hakane hajiya,amma ai da hajiya ruqayya aka kai lefan maryam dinko,ina zaton ki tambayeta zata iya tuna gidan”
”af,qwarai kuwa,bari nayi kiranta”

Cikin sa’a kuwa ta samu ruqayyan qanwarta ta tabbatar mata zata gane gidan,a nan suka shirya tafiyar nayan sallar la’asar don zata tsaya ta sallami mai gidanta zaiyi tafiya da azahar

Su uku ne cikin motar hajiya bintun ruqayya sai baaba uwani,jifa jifa suke tattaunawa kan batun har suka isa unguwarsu maryam din,sukayi parking qofar gidansu kana suka dunguma zuwa cikin gidan

Gidan yana nan yadda yake daga soro zuwa tsakar gidan suka fara sallama,inna hadiza dake kan tabarma a tsakar gidan ta amsa musu don babu kowa a tsakar gidan idan ka debe ita da huwaila dake kitchen tana fama da tuwon dare
kallo daya tayi musu ta fahimci daga irin gidan da ta fito,don haka jiki na rawa ta miqe tana fadin
”lale marabanku,sannunku da zuwa”mami batasan wace ba amma ruqayya tuni ta tunata saboda diban albarkar data yi danar kawo lefe,sake karkade musu tabarmar da take kai tayi tana fadin
”bismillanku ko zauna,ko daga ciki zamu shiga?”
ruqayya ce ta karbe cikin tabe baki tana girgiza kai
”mama muka zo nema,maman maryam”turus tayi kamar bata ji abinda suke fada din ba,don ita har yau babu abinda ta tsana irin taga wani abu na ci gaba ya samu maman,har yau bata dauki izina ba,rayuwar maman kullum sake inganta take,don hindatu kadai tafi dukkan nin yayan da ita ta haifa wadanda duk suka dawo gabanta,daya ce gidan aure saboda rashin kyakkyawan training na zaman auren,hindatun bata bar maman nasu ta nemi wani abu ta rasa ba,ta sake inganta rayuwarta fiye da da,ta sani rashin adda maryam dinta ne a akusa da ta tabbatar maman ma sai ta fi haka,duk da a yanzun ma ko hasidin iza hasada sai ya daga mata qafa

Shirun taci gaba da yi har sai da huwaila ta fito daga kitchen dinsu wanda zuwa yanzu hindatun ta gyara musu shi duk da maman ta bata girki ciki,tayi me saboda babanta da kuma huwailan wadda a yanzu ta saduda,tun ranar da aka gyara kitchen din inna hadiza tabar girki a cikinsa saidai tayi daga waje
”sannunku da zuwa”inji huwaila dake wanke hannunta bakin famfo
”yauwa,don Allah maman maryam tana nan?”
”eh tana cikin daki ina tsammanin sallah take,ga dakin nata nan ku shiga”ta fada tana musu nuni da shi suka amsa kana suka shige
”an dai ji kunya wlh,an zama ‘yar kora da haka za’a qare”
”ba komai,don ma zama ‘yar korar amina ai tafi minke,don qaruwar da nayi da ita banyita da ke ba”ta sa kai ta shige dakinta don tasan halinta idan ta tsaya sai su raba abun fada yanzu ba kunya take ji ba

kan abun sallar kuwa suka taddata tana raka’ar qarshe,falon nata qal da shi yanata qamshin turare,koda can ma mai tsafta ce bare yanzu da babu kowa a dakin nata sai ita kadai,suna tsaye har ta sallame,duk da batasan kosu waye ba da fara’arta ta karbesu
”ya zaku tsaya ku zauna mana”ta fada tana miqewa tare da ninke abin sallarta
sai data ajjiye musu ruwa da lemo kana ra dawo ta zauna mami nata kallon ta,take ta tuna mata da maryam dinta babu tantama ita tayo,kyau tsafta da kirki

Sun taba lemon kana suka gaisa,mami ta dubeta
”nasan baki sanni ba hajiya”murmushi tayi
”gaskiya kam,ban gane fuskar ba”
”nice mahaifiyar abdallah surukinki”
Sabuwar gaisuwa suka sake yi da mamin cikin mutunta juna kana daga bisani mamin ta gabatar mata da abinda ke tafe da su,sosai mama taji dadi don ko mamin bata fada ba takowar da tayi ta fara neman yaran ya tabbatarwa mama sihirin dake jikinta Allah ya kawo lokacin karyewarshi
a nutse mama ta gaya mata inda su maryam din suke,fadar irin dadin da mamin taji bama ita kadai ba harda baaba uwani bata baki ne
”ba shakka gobe zan je na dauko yarana,alhmdlh Allah na gode maka”
a take ta daga waya ta kira baffanta ta sanar masa,cewa yayi ta jinkirta zuwa goben,don bai kamata kai tsaye a dawo da su din ba,akwai abubuwa da ya kamata mafin dawowar tasu,baya ga haka magani yake karba,ta bari nan da wasu yan kwanaki idan ya gama tsara komai zai mata maganar

Bata musa din ba saboda tasan baffab akwai hangen nesa,cikin farinciki da zumudi suka baro gidan zuciyoyinsu fal farinciki da godiya ga Allah,ba qaramin qimar mama mami ta sake gani ba data hada diyarta da danta ta kaisu ga mafaka cikin ikon Allah,sosai ta kuma ganin qimarta

????????????????????????

Washe gari hisham ya shirya don komawa katsina,yanason duba company din abdallah guda biyu dake can wanda abdallan yace a fidda wa ma’aikatan companies din salary dinsu tunda wata yazo qarshe

Kai tsaye ya isa dakin tsoho alhaji wanda dama abdallah na ciki suna tare bayan gama shan rubutunshi wanda ya zama shine ruwan shansa a yanzu,yana duqe gaban tsohon
”banda abunka hisham tafiyar dare ai sam bata da dadi,da ka jinkirta zuwa gobe”cewar tsoho alhaji da yaje yiwa sallama,murmushi yayi kanshi a qasa
”banso komawa ba ma malam,naso naga yadda jikin abdallah zai kaya duk da yanzun ma alhmdlh yana gayamin yana jin canji a jikinsa,tafiyar ce ta zo min haka amma insha Allahu kwana uku kawai zanyi na dawo”
”to shikenan Allah ya tsare hanya,a gaida manyan”
”ameen ameen,Allah ya qara girma”ya fada yana miqewa,ya juya ya miqawa abdallah hannu suka yi musabaha,inna wuro ta shigo da jarka biyi daya man shanu ne a ciki daya nono tace ya kaiwa gwaggonshi,godiya ya mata sosai kana suka juya dukka zasu rakashi bakin motarsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button