ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

hannunta taji an riqe da sauri ta juyo,abdallah ne,ya wani narke yana mata wani krin kallon dake sake karya duk wani makaman zuciyarta,tanajin da biyu yake mata irin wannan kallon
”baby maryam”
”abdallah mene haka”ta fada a zuciyarta
”inaji a zuciyata na kusa warkewa nan kusa,hakan na nufin mun kusa rabuwa?”
wata mummunan faduwar gaba taji,ta lumshe idonta kana race cikin muryarta nai sanyi
”sun fita fa,ka sakarmin hannu muyi sallama”
”hisham ai ba baqo bane,gwara ki zauna nayita kallonki,naga alama da gaske so kike kifi qarfina,tun jiya rabona da na ganki,jiyan ma batan kai nayi na sa kai na bandaki ashe kina ciki kina wanka”
Ba tare data shirya ba ta waiwayo tana dubanshi idanunta a waje,take kuma suka kawo qwalla,dama abinda yakeson gani kenan
”ina wanka?,ba kaya a jikina kenan”
dariyar da bai shirya ba ta subuce masa,ya dinga yi yana kallonta,sai yaga gaba daya ta kuma qaramar yarinya sosai da bazata wuce shekaru sha hudu ba
”wai ke kam shekarunki nawa,i thought ba zaki wuce twenty four ba,kamata yayi Allah a maidaki shekara goma,dubeki kamar wadda aka cewa saurayinta ne ya ganta”
ta lura ma ya maidata wata abar tsokanarshi bayan wasan kura da yake mata da zuciyarta duk lokacin da suka hadu
”Allah sai na gayawa inna wuro leqen mutane kake a bandaki…”
”a’ah,ba dai mutane ba gyara zancanki yammata,leqen mata ta nake,sai kuma mero……”
”mero?”
ta maimata sunan ba tare da tasan ta fada din ba
girarsa ya daga mata
”eh mero mana,itama matata ce baki sani ba?”ai a,hanzarce ta qwace hannunta ta fice a dakin,dariyarsa yasha sosai yana raina wayon maryam din da ta gaza gano abinda yake nufi
Ta gama shirin baccinta ciki doguwar riga mai sulbi mai hannun shimi maroon doguwa ce har qasa ta maida qaramin farin hajabinta jikinta ta haye gadon inna wuro tana karanto addu’o’in bacci,bayan ta kammala ta ja bargon inna wuron ta lulluba zuwa qugunta bayan ta lumshe idonta
Da sauri taji an yaye bargon,ta bude idanunta inna wuro ce tsaye a kanta riqe da torch light donta kashe qwan solar din dakin
”me nake shirin gani meramu?”
cikin rashin fahimta tace”me ya faru inna?”
tana nuna qofar dakin nata da yatsanta tace”ki baro dakin mijinki kizo kimin qabe qabe kan nawa gadon da yake ni ba miji gareni ba ko?”
fuska ta yamutsa
”kai inna,naga dai tsoho alhaji ai yana da turakarsa ko?”
”iyeeee”ta fada tana kama haba
”to tashi ki barmin daki,idan yaso in kinga dama kiyi shimfida a tsakar gida ki kwana can”
ta sake yamutsa fusjar tana kallon innar ba tare da ta ko motsa da niyyar tashin ba
”kai inna ni wallahi kamar ma kwanan nan kin tsaneni”
”eh koma me zaki fada ki fada amma saikin fitarmin a daki,dama kuma ni bana tarayya ai da mai kynnen qashi….zaki taahi ko sai na samo madoki?”ta fada tana dube duben abinda zata dauka na duka din,tasan kadan daga aikinta yadda take qaunar abdallah yanzun ta maketan ta sauko tana guna guni taja bargon
”ajjiye min bargona,kuma kuna da shi”ta fada tana kallonta,tilas ta ajjiye mata din ta fito
tana gab da shiga dakin taji maganar tsoho alhaji yana fitowa daga dakinsa,ta qarasa cikin girmamawa,wata ‘yar farar roba ya miqo mata yana fadin
”da dakinnaki zani,tunda kuma gaki shikenan,wannan maganin banason ya wuce yau ba’a shafa shi ba,daga cinyoyin abdullahi zuwa yatsunsa na qafa,a tabbatar ko ina ya samu,kada ki barshi ya taba da hannunshi don a qa’idarsa wani ke shafa maka,sabida jikin shi har yanzu akwai ragowar abinda aka yi masa”
”to malam,Allah ya qara girma”ya amsa nata ya juya ya koma dakinsa ita ma ta shige
kan katifar ta hangoshi zqune jingine da pillow,laptop ce kan cinyoyinshi kallon wani film yake na tarihin sayyadina umar,vest ce a jikinsa da short nicker wanda iyakacinshi saman gwiwarsa,dauke kanta tayi da sauri,shima tunda ya amsa mata din ya maida kansa kan allon computer din,ta haura kan katifar ta dauki pillow qwaya daya,har zata sauka sai ta tuna da maganin
”tsoho alhaji yace a shafa a daren nan”ta fada tana miqa masa maganin
fuskarshi ba walwala yace
”wa kike son ya shafamin bayan na jishi yana gaya miki kada na taba?”shiru tayi cikin rashin sanin amsar da zata bashi,bata ankara ba taji ya damqi hannun nata bayan ya ajjiye computer din tasa can gefe ya janyota yana fadin
”malama zauna ki shafa min”take kuwa ra samu masauki kan cinyoyinshi,qoqarin miqewa tayi take amma ya danne rigarta,yasa idanunshi sosai cikin nata
”kika sake kika gudu….q’nnn,ni dake ne”ya fada cikin dakiya
”dagan rigarta to zan shafa maka”
bai amsa mata ba sai hannu da yasa yana qoqarin,zare hijabin jikinta,hannayenta ta hada ta cukuikuye hijabin saboda rigar jikinta mai fadin wuya ce bugu da qari kuma mai lafewa ce a jiki
kicin kicin yayi da fuska kamar bai taba dariya ba
”ki bar ganina a zaune bazan iya tashi ba,to kada ki kuskura na sa miki qarfina zaki sha wuya,daga ni sai ke a dakin,na bama kallonki zanyi ba,zan cire miki don kada ki shafa min ba daidai ba ko ki bata hijabin naki,ki shafa min kawai idan kinso ki koma soro ma ki kwana”
ta gama amanna da gaske yake ganin uadda yayi maganar ba wasa a fuskarshi,sakin hajibin tayi yasa hannunshi ya zare shi ya ajjiye mata shi gefe
”fatabarakallahu alhsanul khaaliqin” ya ambata cikin ranshi saboda ba qaramin kyau night gown din tayi mata ba
”tafaddal”yace da ita bayan ya tattare short nickers dinsa can sama,kallo daya tq masa ta dauke kai,bata taba ganin wani namiji a haka ba tunda take,santalan santalan fararen cinyoyinshi masu wadatar gargasa baqa suduk suka bayyana
ta lakato maganin mak kama da man kadanya ta mutstsuka a hannunta,tamkar wadda zata taba kunama haka ta dora hannunta kan cinyoyin nasa,sai da ta runtse idonta kana ta fara shafa masa a hankali tamkar mai sanda
Shiru ya ratsa dakin dukkaninsu suna ji cikin jikinsu kada ma abdallah yaji labari,ajiyar zuciya ya dinga saki a bobboye idanunsa kan maryam wadda bata sani ba gaba daya wuyan rigarta yayo qasa,tsuntsu biyu ya dinga jifa da dutse tsaya sam ita bata sani ba,har ta gama durqusan nata ta zauna sosai
dan jan qafar tasa yayi yana fadin
”kaiiiii” da sauri ta dubeshi tana fadin
”da zafi”kai ua girgiza murmushi ya qwace masa don dama idn nata yakeson gani ya gani din ya kuma gano abinda yakeson ganowar
”nikam gaskiya da biyu kike min irin wannan shafar mero”
baki ta muguda masa
”kada ka sake bani sunan wannan baqaiyiyar budurwa tak,ni ba suna na kenen ba”mirmushi ya kuma saki saboda tsabar iya tsokana
”ke da ita din ai duka jirgi daya ya kwasoku,gwara ma ita tunda ta iya ta sace miki miji”haushin da ya bata yasa ta kasa tanka mishi,sai qara speed din shafar da take masa da tayi
ya sake fadin
”wayyo Allah”bata ko kula shi ba har sai data gama ta rufe man tana shirin miqewa sai ya sake fincikota jikinsa baki daya ya matseta,tana sonvta qwace amma yaqi don riqon tsauri yayi mata
”ki hutar da kanki yau a jikina zaki kwana,ina zaman zamana kin jawomin,dole ki ragen zafi kafin nayi aure tunda ke kika jawo komai”
Da gasken kuwa yake don tuni har ya fara sakin layi,hannunshi ta riqe tamau tana kiran sunansa,a hankali ya janye hannunshi yana fadin
”am sorry na manta”ya fada yana kissing goshinta kana yaja musu bargo ya rufesu,tun tana a darare a jikinsa har ta saki jikinta jin shiru bai qara motsawa ba,da alama ma bacci yayi awon gaba da shi,don dole ta saki jikinta amma still tana jin yadda zuciyarta ke gudu,daga bisani ita din ma wani daddadan bacci ne ya sureta