ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
5⃣4⃣
Allah yana cewa cikin alqur’aninsa mai girma”haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu akwai tambaya a kansu”(ranar qiyama game da abinda suka ji ko suka gani)
lokacin da mami ta koma gida ita da baaba uwani bayan tayi horn an dage mata makeken get din gidan ta wuce ciki sai ta lura duka ma’aikata da security na gidan na tsaye ne cirko cirko a guri guda
kan ta fito daga cikin motar ibrahim ya qaraso cikin girmamawa
”lafiya ibrahim,me ya faru na ganku a tare guri guda?”
mamin ra fada tana kashe motar tare da qoqarin fitowa daga ciki
”wallahi mami hajiya nene ce?”
”nene?,me ya faru?”ta tambaya don wata irin tsanarta tame ji na mamaye zuciyarta,macan da ta jefa tilon danta cikin bala’i,macen da taso ganin bayan su ita da yaran da tafi qauna abdallah da maryam,ta mata alkhairi ita kuwa ta maye gurbinsa da sharri,ta zauna da ita zuciya daya yayin da ita take zaune da ita da ziciyoyo barkatai marasa kyawun manufa,ko a mafarki daidai da rana daya bata taba qullatar nenen da sharri ba sai gashi abun mamaki ita din taso abzata cikin wani rami mai tsananin hadari badan Allah ya dibi ysarkin zuciyqrta ba ya tsallakar da ita daga dukkan wasu tarakuna data dana wa rayuwarta
”ina baya ina rangadin gidan su husaini kuma suna nan zaune da sauran abokan aiki,kawai saiga husaini yazo yayi kirana waiga nene can babu ko kaan arziqi sai daurin qirji ta fito a guje daga bangarenta wai fita zatqyi nemansu adnan,kuma idan ta gansu sai ta kaagesu don sun cuceta sun ha’inceta sun gudu da dukiyarta,da farko na zata ma qarya yake saboda naga ko motsi bata iyawa komai sai an mata,amma da na bisi sai na gasgata maganarsa,to muna shawarar yadda zamu hanata fita sabida kowa yana tsoron tabata tunda ba muharramrsa bace kawai sai ta faki ido ta fice a guje,muka bita tuni har ta fita daga gidan,muna daf da zamu cimmata wata mota ta tsaya,wadan nan mutanen da kika ce kada mu sake barinsu kwanaki su shigo gian nan sune aahe a ciki suka figeta suka jefata ciki,na sa bindiga na harbi tayar har sau biyu saidai ban samesu ba”
shiru mami tayi tana jinjina kai,ibrahim ya kuma cewa
”amma mun dauki nimber din motar,gata”tsaidashi tayi
”babu bin sahunsun da zamuyi ibrahim ka qyaleta da su,qila hakan da Allah ya mata shine mafi alkhairi a gurinmu,bata dace da zama cikin mu ba shi yasa Allah ya hadata da mutanen da suka dace da ita”tana maganar ne yanayin fuskantar ya sauya saboda bacin rai da tashin hankali,ibrahim ya dubi mamin,shekara da ahekaru suna zaune tare,macace mai tausayi jin qai da taimako ga na qasa da ita,ya tabbatar ba qaramin abu bane zai sanyata tace a qyale nene ba,duk da idanuwansu sunga wasu muggan ayyukan na nene da yadda ta so maida uwar dakin tasu mamin amma ya tabbata da abinda ta aikata din yafi haka,take kuwa ya cukuikuye takardar ya yagata gutsi gutsi
”ku koma bakin aiminku ibrahim,kowa yasa cikin zuciyarsa tamkar ma baiga abinda ya faru,irin nata hukuncin da Allah zai mata kenan,don na tabbatar ba mutanem arziqi ne suka dauketa ba,kowa ya shuka na gari kai nasa”
”gaskiya ne mami,Allah ya shige gaba”
”ameen”ta fada tana juyawa cikin gidan,cikin zuciyarta tana qara jin imani kan cewa duk abinda zakayi kayishi domin Allah,matuqar kace don wani zakayi shi to kana tare da wahala,zaka kyautatawa mutum iyakar iyawarka da zuciya daya amma shi sam bai gani,qarshe ya buge da cutar da kai ko ya shiga sahin manyan maqiyanka na farko,amma idan kayi ne don Allah koda shi din wanda ka yiwan bai gani ba baka da kaico ballantana asara zaka samu ladan aikinka ne gaba ga Allah,Allah kasa mu dace,ka bamu ikhlasi
Sai data sake wanka tayi sallah tana kan abun sallar ta dau wayarta ta kira daya cikin qannenta sa’adiyya sukayi magana kan saukar qur’ani da aka raba makarantu makarantu,ko dq can lokacin marigayi alhj abdul-kareem mai nasara an musu,bayan mutuwarshi ne daga baya ta watsar,a yanzu kam ta dauki dambar ci gaba da sawa ana mata don ta fuskanci duk yadda kakai ga kirkinka kamun kai da kayuatatawa mutane wani yana nan duk duniya babu wanda yaqi jini sama da kai koda naman mahaifiyarka zaka dinga yanka kana dafawa kana bashi yana ci tsabar so,sadiyyan ta gaya mata an kammala kaso na farko gobe zasu dora kana sukayi sallama
cikin ‘yan uwan nenen mami ta nemo matar babanta tace suzo su kwashe duk wani abu da ya danganci nene daga gidan don tuni kowa ya sani alfarma karamci sa darajar zaman tare yasa mami ta bar nenen a gidan,matar baban nata cewa tayi gaskiya babu abinda ya shagesu da kayan nenen,don bata manta irin cin mutuncin da tayi musu kan gadon mijinta na farko,hatta da mahaifinta ya dade da zare hannunsa cikin lamuranta
mamin tace dole kam su debe don sun gama zama tare da nene
matar baban nata ma yaba mata sukayi zaman datayi da ita don sunga namijin qoqarinta ma data zauna da ita ba dangin iya babu na baaba tsawon shekarun nan
Da qyar suka zo suka debe komai na natan suka loda a kodi kura,part din ya koma wayam babu ko tsinke nata bare na ‘ya’yanta,sai a lokacin mamin ta fara jin sanyi cikin zuciyarta
”na barki da Allah nene,ko iya haka ma ya ishi yan baya ishara”abinda mamin tace kenan
????????????????????????
Qal gidan yake a share kamar kowanne lokaci,rairayin filin gidan tas kamar an zauna an tsince dattin cikin,banda shati shati na tsintsiya da alamun yayyafar ruwa da suka sa qasar ta danyi danshi da qamshi babu komai
gidan shiru yake kasancewar babu kowa sai ita da abdallan kawai,inna wuro ta je cikin garin gaya bikin sunan wata jikarta,tsoho alhaji kuwa kano ya tafi karbo jakarsa a hajj camp da yake kayan sun dan samu tsaiko sai ranar suka iso,ya dauki mustafa suka tafi tare don yafi jin dadin tafiyar
qasan rumfar yake a zaune kan wheelchair dinsa sanye da baqar t.shirt da red din trouser mai sulbi da kyau,yayin da maryam keta kai kawo na hada abincin dare
idan ka dubeshi a haka sai ka zaci tabbas karatunsa yake tuquru saidai ina zaman sa’ido yayi don da zarar ta kuya zqi zuba mata ido har sai ya fuskanci tana shirin sake waiwayo wa,wani kyau yaga ta yi masa cikin baqi da ja din pakistan riga da wando,duk da rigar har gwiwa take amma gefe da gefe an tsaga shi wanda hakan ya sake taimakawa wajen fidda sharp dinta,ta nanade kanta da baqin dankwali da ya sake fidda hasken fatarta muraran,sau tari yakan raya cikin zuciyarsa kodai ta hada jini da larabawa ko indiyawa
Darensu na shekaran jiya yake tunawa har yau daren yaqi fita daga tunaninsa,wani babban matsayi ya bashi don bai taba samun dama kamar ta ranar ba,har hanzu idan ya tuna yadda take shafa masa maganin sai yaji taikar jikinsa ta zuba,taushi ta laushin tafin hannunta kamar auduga,itakam ta bada hankalinta ne kan girkinta saboda haka bata lura da kallon da yake mata ba,saidai lokaci lokaci tana jin gabanta na faduwa ko taji tafiyarta na hardewa



