ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Habawa ai duk tsawon gadon inna wuro mai rumfa batasan lokacin data dirgo daga kai ba kana ta kwasa a guje,bata dire a ko ina ba sai tsakar gidan,saura kadan suci karo da MAMI wadda ke tsaye tana son sake yin wata sallamar ga zatonta masu gidan basu jita ba
Zubewa tayi gaba daya a gaban mamin ta saki wani kuka mai cin rai,bata taba tunanin ganin mamin na a irin wannan lokaci ba dama zuciya kuma a kusa,ita ma mamin kasa daurewa tayi ta durqusawa ta dago maryam din hawaye na fita daga idanunta,rugume maryaman gaba daya tayi a jikinta cikin wani irin yanayi,daidai lokacin da inna wuro ke fitowa daga bayi dauke da buta a hannunta tana mai amsa sallamar don tana cikin bayin yake jiyo ta ya zaci maryam na bacci ne,dan tsayawa tayi tana kallonsu,take jikinta ya bata mahaifiyar abdullah ce saboda diban kama kadan da sukeyi
Dukkansu suna zaune kan tabarmar suna jimanta al’amarin,har yanzu maryam ta kasa matsawa daga kusa da mamin ganin take kamar har yanzu mafarki take,don ranaku daidai ne bata mafarki da mamin cikin baccinta
kasa daurewa mamin tayi tace
”banga Abdallah ba,ina yayi ne?”
”ya fita tattaki shi da hashimu nan bayan gari bakin rafi,kinsan an kwana biyu ba’a taka qafar ba”
cikin mamaki mamin tace
”hisham dai,dama hisham na tare da ku?”kai maryam kawai ta iya gyadawa
”Allah mai iko,shi yasa na rabu da ganinshi,babu irin cigiyar da ban ma hisham din ba ashe kuna tare”
kasa zama maryam din ma tayi ta shiga dauki ta dauki hijabinta ta sulale ta fice
tun daga nesa ta hango su zaune su biyu shida hisham da alamu magana suke mai muhimmanci sosai,a hankali ta dinga takawa tana qarasawa inda suke dukka idanunta na kan kyakkyawar fuskar abdalla
”taqi ta gane hisham taqi ta fuskanta,basan ta yadda zan fasalta mata ba,bansan hanyar da zanbi ba hisham,am doing my best hisham,ka gaya min ya zanyi?”
abinda taji yana fada kenan ba tare da ta fuskanci kan me yake maganar ba,sai ta qara sauri ta isa garesu data tuna maqaaudin zuwanta gurin,ji yayi kawai an kama hanninshi kana ta fara jansa,a mamakance ya dago yana kallonta,kasa tambayarta ma yayi sai ido da ya zuba mata,ganin yadda ta dage tana janshi ya sanya shi sauqaqa mata wahalar ta hanyar tashi ya bita tamkar raqumi da akala
bata bar jan hannunshi ba har sai da suka isa ga tsakar gidan inna wuro kana ta kauce daga gabanshi,tashin farko idanunsa suka sauka kan maminshi,runtse idonsa yayi ya sake budewa don ya tabbatar shin da gaske ne ko kuwa mafarki shina yake yi kamar yadda ya saba
”mami ce”hisham dake tsaye gefansa ya fada,ita din ma ajikinta ta ji zuwan nasa a hankali ta waiwayo suka hada ido da tilon dan nata,wani irin rauni abdallah yaji ya shigeshi,kewa qauna da soyayya irin ra da ya iyayensa ta taso masa,take jikinsa ya kama rawa yaji qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba,yau maminsa ce a gabansa?
durqushewa yayi a gun a kan gwiwoyinsa kansa na duqe a qasa,hawaye ne ya balle masa tamkar mace,jikin mamin a mace ta miqe ta isa gabansa ta kira sunanshi
”abdallah,abdallah na ka yafewa maminka” da sauri ya miqe ya kama hannayenra hawaye na sauka kan fuskar kowannensu,rawa bakinsa yake yama kasa magana,duk abinda yayi niyyar furtawa sai ya kasa,qaunar mahaifiyar yasa ke sake tosa masa,shaquwa da soyayya dake tsakaninsu ba qarami bane,yana jin bashi da kowa idan ba mamin ba,a lokacin data guje musu ji yayi kamar ya mutu,tawakkaki da imani da Allah ne yasa ya iya danne zuciyarsa yasa mata yadda da qaddara kafin daga bisani ta gano cewa koma meye ta aikata musu ba bisa hankalinta bane
Qarshe fadawa yayi jikinta yana jin nauyin da zuciyarsa na dada raguwa,wani sauqi ma samuwa cikin zuciyarsa daga abinda ya cunkushe mafa a da
hagu da dama suke zaune sun sanya mamin a tsakiya,ko qwaqwaqwaran motsi sunqi yi,ta dubesu cike da tausaya da qauna
”abdallah ku tafi ku kwanta hakanan,Allah ya kaimu gobe ko?”murmushi duka sukayi abdallah ya girgiza kansa
”yau mami komai iya satar baccin banjin zai iya saceni,ko na kwanta din bazan iya baccin ba,itama haka don babu ranar da bazata yi maganarki ba koda cikin zuciyarta ne,saidai idan ke kinajin sai mu qyaleki ki kwanta ko”
girgizq kantq take cikin zuciyarta tana sake jinjina qaunar dake tsakaninsu,tsanar nene ta qara cika zuciyarta,tana jin mawuyacine ta iya yafe mata haqqinsu data dauka,raba qaunar data yi dake tsakaninsu na tsawon lokaci ba tare da sunji ko sun gani ba,haqiqa Allah ne ke saka soyayyar dan adam cikin zuciya
A taqaice kwanan zaune sukayi su duka ukun don sai bayan sallar asuba kowanannsu ya kwanta
Qarfe uku na rana suna tare da ita maryam abdallah da hisham,mamin ta dubi Abdallah
”gobe nakeson mu koma gida abdallha,saboda haka ku fara hada iya abinda ke da muhimmanci,saura ku barwa mutan gidan kafin komai ya qarasa daidaita ku sake waiwayarsu”
cikin shagwabar da ya jima baiyi wa mamin ba yace
”mami a daga min qafa zuwa jibi,akwai muhimmin abinda nakeson qarasawa kafin mu wuce din”
girgiza kanta tayi
”a’ah,gobe zamu tafi”cike da ladabi yace
”shikenan mami,amma sai la’asar ko”
”Allah ya kaimu la’asar din”
wani abu ya darsu cikin zuciyar maryam,duk da zuwan mamin ya mantar da ita kaso sittin cikin dari na damuwar data shiga duk da cewa abun na manne cikin zuciyarta,ta bisu da kallo lokacin da ya miqe yana cewa hisham yazo ya raka shi,wani dan banzan kishi ua lullubeta hakanan zuciyarta ke gaya mata gurin mero zashi
”sannu maryama”maganar mami ta dawo da hankalinta,murmushi maryam din tayi ta sunkuyar da kanta,kama duka hannayenta mami tayi
”na gode na gode na gode maryam,haqiqa bani da abinda zan iya biyanki da shi,halaccinki da alkhairinki mai tarin yawa ne a garemu,haske ce hakanan alkhairi ce ke a rayuwarmu ni da dana ABADAN ba zamu taba mantawa da ke ba maryamu,tabbas babu wadda ta cancanci abdallah sai ke maryam,’yar halak ce kw gaba da baya,kin riqe amana da alqawarin da kika yimin tun washegarin ranar da aka kawowa abdallah ke,baka taba sanin masoyinka na asali sai wani abu ya sameka maras dadi a rayuwa,maryam ina sonki kamar yadda nake son abdallah,hakanan ina sake baki amanar abdallah,ki kasance a gefansa ABADAN duka tsawon rayuwarsa,na tabbatar cewa matuqar kina tare da shi koda bani duniya bazai shiga mawuyacin hali ba,don Allah maryam kici gaba da riqe abdallah kamar yadda kika yi a yanzun”
Gaba daya maryam taji mami ta rikito mata wani qaton nauyi ta dora mata ne,kamar ta daureta ne da jijiyoyin jikinta,girman mamin na da yawa a idanunta,tana daukarta ne kamar mamanta data haifeta,ta rasa mai zata ce da mamin
kuyi haquri da wannan
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶5⃣6⃣
Daga abdullahi dan umar Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace”mutum bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) had sai yazo ranar qiyama fuskarsa babu tsoka daya ta nama(qwarangwal)”,ruwayar bukhari da muslim ce