ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

FANS NA ABDLLAH DA MARYAM,YA BANI SAQO YACE NA GAYA MUKU BA’A SHIGA TSAKANIN MIJI DA MATA FA????????,TSAKANIN MIJI DA MATA SAI ALLAH,WANDA YA SHIGAVTSAKANIN MIJI DA MATA QARSHE SHI ZAIJI……….????????????

Itama kama hannun mamin tayi
”insha Allahu mami muna tare,babu abinda zai raba mu da ke tare zamu rayu”
giriza kanta tayi
”ko ba dade ko ba jima dole wataran na tafi na barku maryam,baya ga haka ma duk musulmi na qwarai ana son ya dinga tunawa da mutuwa ko da yaushe,haka annabi muhammad S A W ya horemu yace mu yawaita tuna mai yanke jin dadi”

”haka ne mami amma don Allah kiyi shiru,kina tare da mu insha Allahu”
mirmushi kawai mamin ta sake yi

????????????????????????

Kayan sawarsu kadai suka diba amma komai sun barwa inna wuro
”bawan Allah ku cire wannan abar taku mai karbar hasken rana ku tafi da ita”daroya ta basu abdallah yace
”a’a inna,ku barta ai kuma zata muku amfani,kudin shekara guda aka sanya mata kinga idan aka cire ai anyi asarar kudin ciki,tunda mu muna da inverter acan”bata fuskanci me yqce ba dai amma ta masa godiya
”mune da godiya inna,karamcin da kika mana bazai fadu ba”

Kudi mamin ta ajjiyewa tsoho alhajin amma qeme me yaqi karba,yace shi abdallah jika ko da ya daukeshi,ba don a biya shi ya masa aiki ba,ko a hanya ya ganshi yana da buqata irin wannan shi mai taimaka masa ne
mamin tace itama ba biyansa tayi ba Allah ne kadai zai iya biyansa amma sam tsoho alhaji yaqi karba bisa dole ta haqura,itama inna wuron qin amsa tayi,sai dabara mami tayi ta cusa mata qasan tabarmarta yadda bazata gani ba har sai sun tafi

Dukkaninsu suka rakosu har bakin mota cike da kewa,maryam kam harda qwallanta don tasan zatayi kewar qauyan ba kadan ba
”ka shiga motar hisham kai da hisham din idan yaso ma taho a tawa ni da maryam”
cikin shagwaba irin wadda ya sabawa mamin yace
”gaskiya mami qafata qafarki,a zamu raba mota ba”qememe yaqi yarda kuma ya kasa ya tsare maryam ba zata shiga kowacce mota ba

Dole hisham ya shige motarsa shi daya,maryam da abdallah na gaban motar mamin ita kuma mami na baya,gaba daya ta hade gabas da yamma na fuskarta don mami ce tace dole ita zata shiga gaban,shi kam dadi ya kamashi ya dinga satar kallonta yana son ta kalleshi ya tsokaneta,kamar kuwa tasan da hakan taqi uarda ta dubeshin

Yana shirin tashin motar mero ta leqo daga soron gidansu da alamu tana labe ne tun dazun a nan,idanh shabe shabe da hawaye,sai abdallahn ya kashe motar ya bude murfin ya fice yana fadin
”ina zuwa”
maryam na kallonshi ya qarasa inda meron take,sai ta rufe fuskarta da mayafi ta hau kuka sosai,tana iya hango yadda bakinsa ke motsi da alamu wani abun yake gaya mata,daga qarshe dariya ta saka,yasa hannunshi cikinaljihu ya fiddo da dubu biyar cikin kudin da jiua hisham ya rakashi cikin gaya ya ciro a ATM machine

Sai sata shige gidansu sunan ya juyo ya dawo cikin motar,yana shirin daura belt mami da hankalinta ke kan wayarta tace
”ita kuma waccan yarinyar fa wace?”
murmushi yq dan saki kana yace yana kunna motar
”zan miki bayani idan mukaje gida”
bata amsa masa ba ya tashi motar bayan yayi addu’a ta matafiyi ya soma tafiya

La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu kinaz zalimin ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta sakamkon wani irin daci da take ji,yana tuqin shima yana satar kallonta,so yake ta kalleshin kuma taqi kallonsa,ya juya ya dubi seat din baya mami ta kashingide abinta tana gyangyadi,ai dole kam sam tunda tazo garin bata yi wani barcin kirki ba tana ta ‘ya’yanta

Ya cire hannunshi guda daya daga kan sitiyarin ya saka cikin tafin hannunta
”baby,me ya faru?,naga kamar baki farinciki da dawowarmu gida”
zame hannun nata tayi cikin hade rai
”ka kula fa malam da kyau,tuqi kake,kada kaje ka zubar da mu”murmushi ya kuma yi yana qoqarin sake lalubar hannunta
”mutane biyu wadamda duk duniya babu wanda ke muhimmanci a gurina sama da su fa nake tuqawa,kinga ya zamarmin dole na kula iya kulawa”

bai qyaleta ba sai da ya kuma kamo hannun nata yana murzawa a hankali kuma atausashe yana lumshe ido,ta sake zamewa wannan karon tana fadin
”ada ka jimin ciwo bana bayan kai ka adana taka amaryar”
ba don ya daure ba saura kadan ya sheqe da dariya,ya sami sarai abinda ke cin zuciyarta kenan
”anzo gurin kadan kika gani yarinya,nayi alqawari kuma sai ya cika,da bakinki zaki furtawa abdallah kina sonahi,sai kinsam ABDULLAHI ba kanwar lasa bane,a jininmu yake”ya fada cikin zuciyarsa,a fili kuwa shima sai ya janyr hannunshi ya maida kam tuqinshi yana fadin
”au haka ne fa,am sorry”sauran qiris ta fashe amma bangaren zuciyarta ya tausheta

????????????????????????????

Dan qaramin biki suka je suka tadda anayi a gidan duk na taryar abdallah,duka ‘yan uwan mahaifi da mahaifiyarshi ne da sukasan halin da ake ciki,saidai babu wanda baiyi mamaki ba ganin abdallahn kamar ba wanda ya kwanta cuta ba,ya sani sarai hakan ya samu asali ne daga kyawun weather na garin ni’ima da kuma kyakkyawa kuma cikakkiyar kulawa da ya samu daga maryam

Cikin mahalarta taron harda SALMA da JIDDA wadanda ke ta binshi da kallon sha’awa da kishi,kishi kuma na banza,eh na banza mana don tunda ya kwanta babu wadda ta tako qafarta da niyyar gaisheshi,a zatonsu abdallan ya gama aiki ne cutar data sameshi ba qaramar mummunar cuta bace babu ranar warkewa
to ko dama can shi ba yinsu yake ba ballanta na a yanzu da yasan ajin kowa

babu batun komawa bangarensa a yanzu don mami tace bata yarda da gidan ba ma baki daya balle bangarensa don haka cikin dakunan dake corridor din nan guda hudu tasa aka gyara biyu,abdallah ya dauki daya maryam ta dauki daya,tana sane ta raba musu dakin don tuni tayi magana da hajiya laila ta sudan next weak ta zata shigo nijeria zata yiwa diyar mr presdent gyara jiki na bikinta da za’ayi so zata sauka gidan mamin don sabon gyara mamin tace tana so ayiwa maryam din,a cewarta ba zasu tare sabon gidansu da tun asali a can aka yi jeren maryam ba sai ta gama gyara diyarta,daga maryam din har abdallan ba eanda ya sani,ita dai maryam raba dakin da mamin ta yi musu da kanta ba qaramin dadi yayi mata ba don nata son ko yaya tayi wani abu da zai fallasata gurin mamin,shi kuwa abdallah ckkin tunani mamin ta sakashi da tunanin ko maryam ta gaya mata wani abu ne game da yadda aurensu ya samo asali?

????????????????????????

Ita kanta tayi mamakin baccin da tayi,ta jima sosai rabon da tayi bacci irin wannan,don a qauyen ni’ima yawanci daga ta idar da sallar asuba bata komawa,zama take kan abun sallah tayi addu’o’inta da karatun qur’ani sabida lokaci ne mai falala da akeson yin addu’a a cikinsa,gari na yin shaa zata jiyo kwaramniyar inna wuro take zata fito su hau aikin kintsa gidan da hada abun kari,bata farka ba tunda ta kwanta sai shida,tayi sallar asubahi ta sake komawa,sau biyu abdallah na leqota ba tare da ta sani ba tunda bata qulle dakin ba ta kwanta

sai sha daya na safe ta kuma tashi,kayan jikinta ta cire ta daura towel ta shiga wanka,bayan ta fito tayi tsaye gaban madubi tana goge ruwan jikinta kana ta ja dressing chair ya zauna akai tana qoqarin fara shafa mai
”amma fa yau garin kamar da zafi zafi,ki shafa kadan kada ya saki gumi da yawa”taji an fada,a tsorace ta waiwayo,yana kwance abinsa daidai kan gadon nata hankalinsa kwance kamar a dakinsa yake,sanye yake da t shirt fara qal mak gajeran annu sai three quater shima din fari ne tas,yayi saisaye da gyaran fuska ya sake yin kyau kmar wanda aka canza shi daren jiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button