ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ta bangaren ‘yan uwanta kuwa saidai ace Allah ya rufa asiri kawai domin dukkaninsu cikin shekara guda babu wadda bata da tabon saki wanda tsantsar rashin tarbiyyarsu ya hanasu zaman arziqi da mazajensu,a haka dai ake gurgurawa har kawo wannan lokaci,hankalin maryamu bai fara tashi ba sai da aka zo auren qannanta zagaye na biyu wato azara shamsiyya da maraqisiyya,tsantsar gori habaici da baqar magana idan da tana tsiro a lokacin to da tuni ta yiwa maryam,sai Alla ya halicceta mai haquri da kawaici hakanne yasa bata fiya zafafawa kan lamuransu ba,idan suna yi dauke kanta take kamar yadda tun usuli ta tashi taga mamanta nayi
samuwar aikinta ya taimaka qwarai wajen kyautatuwar rayuwarsu,wanda alfanun ilimin da ta gani ya sata jajircewa da tsayawa qanwarta daya tilo don ganin itama ta amfana,duk lokacin da ta daki albashinta bata fasa siyan wani muhimmin abu ta kaiwa mahaifinta ko ta ciri kidin tsaba ta bashi,babu kuma wani jin nauyi zaisa hannunshi ya amsa da sunan ai yarshi ce,haka rayuwar maryamu ta taso cikin tsangwamar ‘yan uba wanda har yau ita take gani ba kuma tasan ranar qarewarta ba
WANNAN KENAN
Mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
▶8⃣
Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a yanzu kam ta sanya jabir ne kawai cikin addu’o’inta kamar yadda raliya ta shawarceta,domin tausayinsa ne fal cikin zuciyarta,tana ji a cikin zuciyarta ta sanadinta ne ya afka wannan qaddarar
abu guda ne ta kasa tinsa komawa walwalarta da aikinta tamkar,yadda take yi a da duk da yadda take son aikin,ta barwa ranta cewa ta ajjiye aikin zata kuma jira har lokscin da ubangiji zai musanya mata da da wani mijin ko da baikai jabir dinta ba
????????????????????????
misalin biyar da rabi ne na yammaci,zaune take a rumfar tasu wadda ta sha mopping tayi fes,dai qamshin turaren tsinke take,mamanta na dakin babansu tana gyarawa don ita ta amshi girki,don sam bata lamunce don ranar girkinta bane ta tura yaranta su share dakin baban nasu ba kamar yafda taga su huwaila nayi tsabar ganda,yayin da hindatu ke makarantar islamiyya
sanye take da maroon din material dinkin doguwar riga da yake ma’abociyar son dogayen riguna ne ko don tsahon da take da shi,yatsunta sunyi kyau da jan lallen da tadan qunsa iya yatsu,a lokaci irin wannan idan bata da abinda duka zatayi,taka duqufa wajen research din girke girke a daga sashukan dake watso kalolin abinci na qasashe daban daban,kadan kadan hankalinta ke rabuwa gida biyu,wani lokaci yayi tsakar gida da yaran inna hadiza keta faman ta’adi cikin falon gyatumar tasu da hayaniya na ‘yan fadace fadace atsakaninsu kuma babu wanda ya isa yace zai tsawatar musu
cikin haka ta jiyo sallamar inna hadizar,abu na farko da ya biyo bayan sallamarta shine ashar da ta dura wanda har sai da maryamu tayi ta’awizi cikin zuciyarta
”kaga tsinannun yara shegu,ke balaraba da na bar muku dakin a bude shine kuka maida min shi sansanin fada da kokaye kokaye,kuma saboda tsabar baqincikin Allah yayi maka arziqi a rasa mai tsawatrwa uaran salon su fasa ma abu kosu lalata ma su jawo maka asara,dadin abun ma yanzu kana da arziqin da zaka gyara”
sarai mama tasan da ita take amma kasancewar ko da can ma da jini ajika ba kula shirginta take ba yasa yanzun ma tayi mata dif,saiga huwaila ta fito daga wanka takalleta
”a’a,ina kuma kikaje?”
”yo ina kuwa zanje da ya wuce gidan doyar albarka jamila”ta fada tana shirin shigewa dakinta
sakwatoto huwailan tayi
”amma inace baki tafi ba don wanna wanka da nayi na shirin zuwa ne,tunda munyi tare zamu je”
”kiji hiwaila da wani zance,don,lawai zaka girin naka sai ka jawo bare?”binta wadda tare suka je da innar tata ta maidawa huwaila raddi
”kinga ba dake nake ba ‘yar ayi jikar na saba”
”a’a,dakata don ta fadi gaskiyarta,kada kiyi haushin kaza huce kan dami”inji onna hadiza cikin salon tare mata
”au bayanta kike goyo kenan?”
”qwarao,yo akan me?”
baqinciki ya,hanata cewa komai sai qwafa kawai da ta ja ta shige dakinta
qarar wayarta ce ta sata dawowa daga diniyar da su inna jadizan suka shigar da ita,a kullum kwanan duniya sake gasgata zancan raliya takegame da abinda ya faru tsakaninta da jabir,jikinta a sanyaye tabi wayar da kallo ,da kamar ba zata daga ba amma ganin sunan mama ya sata babu jinkiri ta daga,cike da,girmamawa take gaidata
”babu abinda zaki cemin maryamu,wa yafi qarfin qaddara a rayuwa?,abun nan ya riga ya wuce addu’a ce kawai mafita,amma anyi anyi ki koma gun aikinki kinqi,na tambayi haj rabi ko wani laifin aka miki sunce babu komai,ko an miki wani abu ne agun?”
cike da girmamawa tace ”babu abinda aka yimin mama wallahi”
”to shikenan,indai da gaske haka ne kizo gobe gida ki sameni da la’asar,da akwai aikin da aka samu kuma gaskiya a iya hasashena babu wadda ta dace da aikin sai ke,don na yaba qwarai da tarbiyya gaskiya da riqon amanarki”
ba zata iya musu da mama ba wato hajiya atika abubakar,banda haka da wata ce zqta ce mata ta gode bata buqata,amma girmanta da qaunar da take gwada mata ta wuce haka a gurinta don haka tace
”to mama,na gode Allah ya saka da alkhairi insha Allahh goben ina hanya”
”to shikenan a gaida mutan gidan”
”zasu ji insha Allah”
ta sauke wayar tana jin wani abu na dan taba zuciyarta,mama da bata kima da shigowa ba tace ”ke da waye?”
ajiuar zuciya ta saki
”haj atika ce,wai tana nemana gobe”
”to Allah yasa lafiya,ko zancan komawarki ne gurin aikin?”
”a’a,tace wani aiki ne ya samu,amma sai naje goben zanji”
”Allah ya rufa asiri ”ta fada maman tana ficewa dauke da wankakken zanin gado da rigar filo
murmushi maryam tayi tana jinjina kai,wato miji da mata sai Allah,maman ta tana burgeta matuqa,bilhaqqi take kula da mijinta,bata duba komai sai zatin Allah da kalmar nan ta aure bautar ubangiji
????????????????????????
washegari ta shirya tsaf cikin atamfa dinkin riga da skert yaluwa sosai tayi,mata kyau ta qara haske da rama,hakan sai ya sake fidda tsayinta,kasancewar lahadi ce yasa ta nemi rakiyar hindatu ko zata ji dadin tafiyar,don ita kanta bata son tafiya ita kadai,gani take kamar idan ta fita nuna ta za’a dinga yi,tsawon watanni kusan biyar amma tunda abin ya faru baifi sau biyi ta fita ba zuwa uku shima sai dare
babu dadewa suka isa gidan maman,a falon qasa aka saukesu mintina biyar aka haura da su samanta wanda ba kowa take kaiwa ba,cike da fara’a ta tarbi maryam din,ita dai ranta yanason maryam din,natsuwarta na burgeta,
kayan ciye ciye ta sa aka kawo misi ta dan basu lokaci kadan sannan ta dawo
”maryam”abinda ta fara cewa kenan
”kamar yadda jiya na shaida miki a waya aiki ne ya samu,yayi shige da na gurina amma yana da bambanci domin wannan a gida zaki dinga yinshi,zaki samu albashi mai tsoka fiye da na gurina”
ta,dubeta da aily eyes dinta”mama wanne irin aiki ne a gida?”
”kinsan marigayi alhaji abdulkareem mai nasara?”
sai da tadan shiga tunani sannan tace
”eh ina jin sunanshi mama”
”yauwa,kinga sanannen mutum ne kuma fitace tun kafin rasuwarshi,yaro daya Allah ya basu wato Abdallahduk da cewa yana da wata matar amma Allah abi bata haihuwa da shi ba,saidai ya riqe mata nata uaran da ta taba haifa awani gidan mata ne su biyu da nimiji daya yanzu haka duka suna tare a gidan duk da rasuwan shi alhj abdulkareem din hakan baisa sun raba mazauni ba,mamanshi na matuqar sonshi da kaffa kaffa da lamuranshi,duk da haka ana farautar rayuwarsa don kusan sau biyu kenan ana zuba poising abincinshi,ta rasa daga ina matsalar take,kuma duk lokacin da hakan ya faru idan aka tashi binncike sai a samu da hannun kukunshi,hakan yasa take canza masa kuku kala kala,amma har yau babu wanda hankalinta ya kwanta da shi