ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Hada kai sukayi suka fashe da kuka kowacce da irin tata nadamar,sun qi Allah bayan ya musu ni’ima,idanunsu ya rufe basu ganin baiwar da yayi musu da tarin ni’imominshi a garesu sai yanzu da ya karbe abinsa,dama ya fada cikin littafinsa mai tsarki”idan kuka gode min zan qara muku,idan kuma kuka kafirce to haqiqa azabata mai tsanani ce”,sun yarda sun dauki hudubar shaidan,wanda dama bashi da burin da ya wuce batar bayan dama ya sani cewa tun can dama shi batacce ne,kuma dama yayi wa Allah alqawari sai ya batar dq bayinsa kamar yadda yazo cikin wasu surori na qur’ani lokqcin da Allah yace ya fita daga aljanna la’ananne ne shi
”kuma la’anata tana tare da kai har zuwa ranar qarshe”
sai shaidan din yace
”ya ubangiji ka jinkirta min izuwa ranar qiyama”sai Allah yace an jirka maka,har uzuwa rana da lokaci sananne,sai shqidan yqce da ubangiji
”na rantse da isarka da buwayarka sai na batar da su gaba daya,saidai bayinka daga cikinsu tsarkakakku”sai Allah yace da shi
”haqiqa bayina baka da wani iko a kansu sai wadanda suka bika dagq cikin batattu,kuma haqiqa jahannama ce makomarsu gaba dayansu,tana da qofofi guda bakwai”a wani gurin kuma shaidan din yace
”zanzo musu ta tsakaninsu data damansu data hagunsu mafi yawansu zaka samesu marasa godiya”
haka ya sake fada a wani gurin cewa
”sai na batar da su,sai na sanya musu buri sai na umarcesu su canza halittar Allah(kamar bleeching yana daya daga ciki)
shi yasa Allah da kansa yake fada mana
”haqiqa shaidan abokin gabarku ne ku ruqe shi abokin gaba”,muna mantawa ne da ranar mutuwa ranar tonon asiri ranar hisabi,ranar da duk wata rai saita bi ta saman siradi ta wuce wanda qarqashinsa wutar jahannama ce,aikinka mai kyau gaskiyarka zumunci da ruqon amana ne kawai zai qetarar da kai cikin salama
Son zuciya ya mana yawa,muna biyewa soye soyen zuciyoyinmu baka iya hana zuciyarka aikata mummuna wanda hakan ke kaimu ga halaka,Annabi muhammad S A W yana cewa”an lullube aljanna da abinda rai baya so(kamar salla azumi zakka,zumunci,da sauran ayyukan alkahairi da bamu son yi ko muke jin wuya gun aikata shi)an kuma lullube wuta da sha’awe sha’awe(kamar zina,caca,cin dukiyar marayu,annamimanci,sata da sauran abubuwa da rai kejin dadi yayin aikashi)”
Allah ya sake cewa ba don falarlarsa da rahamarsa ba da duka munbi shaidan face ‘yan kadan
Allah kasa mu dace duniya da lahira
Sun jima cikin alhini da jimantawa kansu kafin habiba tace
”zahariyya nifa na gaji,anya ba kashe malam zamuyi ba?”duk da yadda taso ga neman mafita amma sai da shawara ta tsoratata,don bata manta ba irin wannan kuskuren taso aikatawa ya kawota ga wannan matsayin da take ciki yanzu
”habiba,in sake yunqurin aikata wani kuskuren kenan?”
”kashe malam,zahariyyq rage mugun iri ne cikin al’umma,bakiji abinda yace babe,malam fa bazai taba shiryuwa ba,shin kin san shi mutum nawa ya kashe cikin wannan qazamar harkar tasa?(hmmm,sai yanzu data ritsa da su suka san qazama ce)”
cikin rashin gamsuwa ta girgiza kai
”wannan shi da Allahnsa amma mu dq muke neman kubuta kuma inamu ina kisa,shawara daya ce kawai tunda mu bamu tsaya munyi karatun addini ba boko muka sa a gaba,ba wasu addu’o’i garemu ba kawai kullum mu dinga karanta masa fatiha ba adadi,ai Allah yana jinmu,kuma nasan da yardaraa wata rana zamu kubuta”
take ta yarda da shawarar zahariyyan don tafi tata fidda maslaha
mrs muhammd ce
????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶5⃣9⃣
An karbo daga Abdullahi dan amru dan Aas Allah ya yarda dasu baki daya,haqiqa Manzan Allah S A W yace”yana daga cikin manya manyan zunubai mutum ya zagi iyayensa(uwa da uba)”,sai sahabbai suka ce ”shin mutum zai iya zagin iyayensa?”,sai Manzo S A W yace”eh,a zagi mahaifin mutum,mutum(wanda aka zaga) shima ya zagi mahaifinsa(mahaifin wanda ya zageshi din),ya zagi mahaifiyarsa shima(ya rama) ya zagi tasa(wanda ya zageshin)”
ruwayar bukhari da muslim ne
Itakanta ko ba’a gaya mata ba tasan ta canza,wani santsi da qamahi fatarta ke fitarwa na musamman,wani lokaci har shanshana kanta takeyi kota tsaya kallon kanta a madubi,magani masu kyau mamin ke bata na ainihin ‘ya’yan itatuwa ba gamje gamjen bature ba,tana jin naiyinta da kunyarta haka zata karba ta sha tana rufe ido,mamin takanyi murmushi tace
”babu kunya tsakaninmu maryam diyata ce ke kamar yadda nasha fada,namiji kuwa dan son gyara ne bashi da kunya ta wanann bangaren,balle abdallah da ina kula da rawan kanshi,idan kika zaune kara zube cikin lokaci qanqani zaki wargaje fes babu kunya zai dauko miki wata,shi yasa har yau ina alfahari da lambar yabo da na karba agun daddyn abdallah har ya mutu yana yabamin,so haka nakeso ki zama gurin abdallah koma kifi haka,koda akwai wata ma kisha gabanta”
kunya ta kuma kamata duk da maganar ta taqarshe ta dan haifar mata da fargaba
????????????????????????
Tun ranar bai kima kiranta ba,har ta dinga zaton ko fishi yayi,cikin ranta take jin ba dadi idan fushin kuwa yayi,can qasan ranta ake tsinkularta ta kirashi taji muryars amma da zarar tayi kamar ta kira din sai kunya da nauyi su hanata
Kusan tara na dare ne suna zaune ita da mami da baaba uwani,baaban ce ta musu sallama ta wuce bangarenta mami ta duba agogon kana ta miqe ta haura sama bayan ta ce da maryam tana zuwa,kallo take amma batasan ya akayi idanunta suka kai kan hotkn abdallah window size dake kafe a can kusurwar falon ba,sai ta kafe hoton da ido,a hankali wani abu ya dinga motsa zuciyarta,ta miqa hannunta ta duba call history inda num dinsa take wadda ko serving bata yi ba,ta shiga canki camkin ta kira ko a’a,kamar wadda aka tankwabi hannunta ta danna kiran gakin ya soma tafiya sai ta qyaleshi.
Daidai lokacin da yake cikin dakin hotel din da suka sauka,shi da manyan yaransa ne guda biyu,a gaggauce yake shiryawa cikin wadansu baqaqen kaya samfurin kayan jami’an tsor,duk da kqyqn qiki ne amma ba qaramin kyau suka yi masa ba,yana cikin daura belt dinsa bayan ya sanya bindigarsa a aljihun wandon na baya yaga shigowar kiran,bai lura ba sosaj ya dauke kai yaci gaba da sanya boot a qafarshi baqi don muhimmin aiki ne a gabanshi bai saba qa’idar lokaci komai nasa a tsare yake
Tana dab da tsinkewa ya kai hannu da niyyar dauke wayoyin nashi ya kashesu don bazai fita dasu ba,ba dasu zaiyi amfani ba already ya gama maqala na’urar da zasu dinga communicating da abokan aikin nasa a jikinsa,mamaki ya kamashi ganin sunan honey sweet bisa screen dinshi,katse kiran yayi kana ya kirata
sai da gabata ya dinga bugawa kafin ta amsa kiran,a kasalance ta kara wayar a kunnenta hade da yin sallama,duk da kuzarin da yake da shi sai da yaji an zare masa shi tas,shi da yake ta shiryawa a gaggauce yana basu order din baison bata lokaci sai gashi yana shirin kwanciya saman gado,yaran nashi suka kalli junansu da lamar tambayar ya haka?a tsakaninsu saidai babu damar furtawa oga suka ja bakinsu suka tsuke,alama ya musu da su fita su jirashi a qofar dakin yana tsoron kada ya tafka abun kunya a gabansu,don tunda yaji muryarta komai ya kwance masa.



