ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Shima dai a kasalance ya amsa mata sallamar,daga nata bangaren ma wani dafin ya kuma zuba mata,shiru ne ya ratsa tsakaninsu tana jiyo saukar numfashinsa,ya shiryawa sata tayi magana koda bata so,ya santa da qin yarda da gaskiya ta wannnan bangaren,saida yayi dariya ciki ciki sannan yace
”Allah sarki baby,kafin kice komai nasan kewata ke damunki kika kira kiji sweet voice nawa ko?”
gabanta ya dan fadi ta zaro ido kamar tana a gabansa ne,sai data cire wayar daga kunnenta ta sake dubawa shidin ta kira sanann ta maida kunnenta

”sai kace wata kai,niba wannan yasa na kira ba,dole ce ma ta sani kiranka”
murmushi ya saki mai sauti wanda ya kusa wucewa da imaninta
”attitude naki din nan yana burgeni,kina da jarumta da yawa,aiki ne ya cushe min shi ya hanani kiranki my suger”wani sanyi taji yana ratsata har sai data cure gu daya,rake idea din yadda zata bagarar da shi yazo mata
”hmmmm,gida nakeson naje naga mama”
shiru ya danyi kana ya sake sanyaya muryarsa
”nima zanso kije ki ganta din,amma sorry baby,gaskiyq ina kishinki da yawa,na tabbatar idan zaki din saidai driver ya kaiki fa,kinga kun kadaice daga ke sai shi cikin motar….har zuciyata ta fara zafi ma wallahi da tuna hakan da nayi”
ta hade rai don gaskiya tana matuqar son ganin maman

”amma fa ka sani yaushe rabona da mama,tun ranar da kasa aka fiddani a gidan”ta fada cikin shagwabar da batasan tayi ba ma,shikam tuni taso sauya masa lissafi don sai da yayi ajiyar numfashi kana yace
”shine kuma sai kin illatani da muryarki?”
”me kuma nayi?”
”kinfi kowa sani,gaskiya my kiyi haquri idan Allah ya dawo dani na miki alqawarin kaiki da kaina ki wuni har dare sai nazo na daukeki kinji?”
hawaye taji kawai na silmiyo mata,don haskiya ta qagu taga mamanta,tayi kewarta sosai,sai kuma yqce sai ya dawo sanann zata je,bayan shi kullum sai yaga tashi maman saidai idan baya gari,kasa magana tayi shima shiru yayi yana saurarenta,can qasa ya jiyo kamar sautin kuka,da hanzari ya miqe ya zquna yana fadin
”ya salam,maryam me yasa kika maida hawayenki masu araha irin haka?,daga cewa sai na dawo zaki je?”

”eh,ai baka kyauta ba,banson rashin adalci fa abdallah ka san halina sarai”cewar mami data amshi wayar bayan ta maidata handsfree,sam maryam bata san ma ta iso ba sai da ta qaraso gabanta
kanshi ya dafe
”shikenan mami nikam abdallah bawan Allah,naga ta kaina an hade min kai”
”har hanci da goshi ma zamu hade maka indai zaka dinga matsantawa irin haka”
”mami ina da kishi sosai kin sani,dole idan zata je mami driver ne fa zai kaita,mami banason wallahi yani ya kalleta”
”oh abdallah,halin naka dai yana nan,to zuwa kam sai tajeshi haka kawai,wake raba da da uwa,yaushe rabon da tq gansu,haba abdallah”
”shikenan mami na yarda mata taje,amma ba kwana ba,yauwa……baaba sule ne zai kaita,kuma don Allah ta saka hijabi don Allah”ya fada a sanyaye,wani mugun kishinta yake ji yana yi kamar yasan gyaran jiki ake mata dan ubansu
kama bakinta mamin itama tayi kana tace
”iyeee,sannu fa ubana”marairaicewa yayi
”mami pleaseeeeee…….”
”ya isa”tayi saurin tsaida shi
”taji zata saka,ince ko shikenan?”
”i love u my mommy”ya fada cikin murmushi
”me too my son”ta fada itama,tana shirin katse wayar yace
”yauwa mami…..i need your prayer mami zami fita aiki kan mutumin nan kimin addu’a mami kamar kika saba,i know ita ke kaini ga yin kowacce iriyar nasara”maryam dake gefe duk dai taji ba dadi wani kewa da karayar zuciya na son kamata
addu’a tayi masa sosai y
hannayensa a sama kamar suna tare ta gama suka shafa su duka,sai yaji wata nutsuwa da dukka qarfinsa sun dawo.

Miqawa maryam wayar tayi dom suyi sallama
”baby….ki kulamin da kaina”
”kanka kuma?”
”eh i mean you,nine ke kamar yadda kece ni,byee love u much more”ya fada ya katse wayar sai ya barta da waya a kunne,a sanyaye ta cire wayar bayan ta sauke ajiyar zuciya

????????????????????????

Cikin atamfa excellent ta shirya pure cotton,duk da mai qaramin kudi ce amma ta matuqar amsarta,kalar blue black dark blue and navy blue da sea green ce,sai ta samu kanta tana aiwatar da umarnknsa duk da ba’a tuna mata ba,hijabi ta sanya blur black wanda ya rufe ilahirin jikinta,mai hannu ne hakanan yayi matching sosai da atamfar ta,ita kanta data kalli madubi sai taga tayi masifar yin kyau,hakanan tana jinta compertable sabanin mayafi,duk da cewa dama ita gwanar hijabince musamman sanda tana gida
baaba sule dinne kuwa tana fitowa suka gaisa da kanshi ya bude mata motad duk da bata so kunya ce take rufeta,don aqalla ya kusa sa’an abbanta

Ta dinga kallon unguwar tasu,babu shakka gida akwai dadi,baka gane hakan sai randa aure ya daukeki daga cikinsa ya kaiki wani gu,komai rashin sukuni na gidanku randa ka barshi sai kaji kana kewa da begensa,ta samu gidan auren da ya ninka gidansu nesa ba kusa ba amma bata daina kewar gidansun ba,may b home is nothing but two arms holding you tight when you are at your worst

Cike da zumudi ta saka kai cikin gidan da saurinta saboda yadda jama’ar unguwa keta binta da kallo,suna ganin ta sake zama ta daban,wata ma yaranta ke kai mata gulmar maryam tazo sai a hau leqe saboda ta tsaya suna magana da baaba sule ashe mami ta cika boot da kaya bata sani ba sai yanzu yace ta turo yara su kwashe

Farinciki ya cika,zuciyarta ganin gidan qal a share sabanin da da iyakacin tsaftar qofar dakinsu ne zuwa,cikin dakin nasu,lubabatu ce kan tabarma zaune da qananun qannensu wadanda suke daki daya da da qatuwar farar takarda ta shimfideta kan tabarma ta zana alifun ba’un har zuwa ya’un manya manya da alamu tana koya musu ne shi yasa ko sallamarta basu ji ba,kafin ta sake maimaita sallamar ta hango isyaku ya fito daga dakin uwarsa kanshi tsaye yabi takan takardar ya take rubutun kana yayo hanyar waje,lubabatun ce ta yunquro da sauri ta cafko wuyanshi ta baya
”wannan iskancin naka isyaku ya isheni wallahi yau sai jikinka ya gaya maka”

Da sauri maryam ta qarasa don kada abun ya kwabe tana banbare hanunta daga wuyan isyaku wanda keta kici kicin qwace kansa cike da rashin kunya
”sakeshi lubabatu kinji sakeshi”sai a lokacin taga maryam din ba musu ta sakeshin ya kuwa fice abinsa da gudu,ta saki fuskarta daga daurewar da tayi tana fadin
”sannu da zuwa adda maryam”
”yauwa lubabatu,karatu ake yi ne?”ta dubi yaran kana tace
”eh,makarantar dare suke zuwa malaminsu yace su tabbata sun iya zuwa anjima zasu je kuma naga basu iya ba”farinciki ya kama maryam ganin an fara samun ci gaba a harkar karatun yaran
”da kyau kin kyauta kuwa lubabatu”
yaran suka zuba mata ido suna shakkad zuwa gurinta,ko dama can ita ba mafadaciya bace bata dai shiga shirginsu ne saboda gudun rashin kunya irin tasu,su kuma suna ganin a yanzu ta zama yar gayu kada ta makesu idan suka matso gurinta tunda haka jamila ke musu sanda tana aure gidan jabir
sai ta bude hannayenta tana fadin
”kamar baku ga yayarku bane,ku taso mu gaisa mana asiya”
ai kuwa har rige rigen zuwa suka dinga yi,sai taji farinciki ya rufeta,zaman lafiya babu abinda ua kasihi dadi haka dan uwa,baka da kamarshi cikin duniya,hamsin hamsin ta fidda ta raba musu su biyar tace su sayi alawa

Ganin har suka gama budurinsu,aka gama shigowa da kayan da mama ta hadota da su samfurin kayan masarufi babu wanda ya leqo daga matan gidan ya sanyata tambayar lubanatu wadda gaba daya maryam ta karanci nutsuwa sosai a tattare da ita
”ina wai matan gidan ne?”
”au…”ta fada tana murmushi tare da dafe bakinta
”na manta ban gaya miki ba,sun fara zuwa makarantar matan aure qarfe tara na safe zuwa daya na rana mamata da maman hindatu(maman maryam din)ke zuwa,ya hindatu ce ta sanyasu”
cike da nuna kara tace
”inna hadiza fa?”
sai da ta kalki qofar dakin nata kana ta tabe baki
”tana ciki tana bacci,tata makarantar kenan”ta fada tana bushewa da dariya,daquwa maryam ta mata
”mamarki ce itama”daki lubabatu ta shiga ta daukowa maryam maqullin dakin maman tace
”adda ga key din ko”ta karba kana ta budr dakin maman ta shiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button