ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna cikin dakin suka jiyo shigowar hindatu,shigowarta ne ya tunowa da baba sabon babur da jabir din ya siya masa ya dinga zuwa kasuw ko wata guda ba’a rufa ba yace maryam din ta tayashi godiya
Nan cikin dakin itama ta ahigo bayan sun gama gaisawa da mama suka sha hirarsu da baban,har kusan qarfe tamwas da rabi suna tare,tuni ta kira baaba sule tace ba sai yazk daukarta ba don hindatu tace su zasu maidata
har soro suka rakosu baaba huwaila da yan qannesu,a tsakar gida sukayi sallama da baaba,suna kallo su jamila da binta na leqensu ta window
cikin mota suka tadda jabir din,hannunsa ya dunqule yana mata jinjina irin ta sarakai”Allah yaja da ran antinmu,Allah ya taimakeki uwar gidan abdallah mai nasara”dariya ya bata ba kadan ba
”haba jabir,ka mance cewa ka girmeni irin wanan gaisuwa haka?”
”ai yanzu kece babba,ko kin mance kin bani ‘yar qanwa,gimbiya hindatu,wadda ba qaramin yabawa da zaben da nayi nake ba har yau”dariya ya bas gaba dayansu har suka fara taciya suna hira abinsu
sai da suka fara biyawa ya yiwa hindatu siyayya ya hada harda maryam din kana suka ajjiyeta a gida sannan suka nufi nasu gidan
????????????????????????
kwana bakwai mami bata bari an dakayar da gyaran da ake mata ba,tamkar ana shirin canza mata fata,ita kanta mai gyara ta yaba yadda gyaran ya karbi jikin maruym di sosai da sosai,baaba uwani kuwa zama take kawai tana kallon maryam din
”gaskiya meramu anya ba canza miki fata hajiyar nan me gyaran jiki take ba?”duk sanda ta fadi hakan dariya take basu ita da mami
Kusan tun ranar da sukayi waya da abdalla kan zuwanta gida basu sake samun kiranshi ba,ana gobe kwanaki bakwai din da ya diba zasu cika mami ta nemeshi don taji goben zai dawo,saidai ta nemi layin nasa yafi sau goma bata sameshi ba,har cikin dare tana iransa bata sameshi
da safe ma hakan ce ta faru,damuwarta ta kasa boyuwa ta tadda maryam a kitchen tana goge freezer tare da sake jera kayan ciki don mamin ta hanata yin kowanne aiki
”ni kam maryam kina samun abdallah a waya kuwa”maryam din ta waiwayo ta dubi mamin sai ta rasa amsar da zata bata,don ita kanta tasha kasa kunne cikin dare lo da rana taga ko zata samu koda texs nasa,Allah ya taimaketa tin kafin tace wani abu mamin tace
”sam ba’a samun wayanshi,na kira na kira duka akashe”
jikinta taki yayo sanyi gaba daya,gabanta ya dan fara faduwa kada kadan ta juyo gaba daya ga mamin tace
”to mami ni cewa nayi ko chargy ne babu a wayoyin nashi?”
kai ta girgiza
”bana jin haka,saboda ba cikin wani qauye bane cikin tsakiyar abuja ne fa,kusa da villa,kinga ta yaya za’a rasa chargy a wayoyi?”
sbiru ya sake ratsa tsakani,bayyanar damuwa kan fuskar maryam wadda ita kanta batasan ta bayyana bayasa mami riqe hannunta
”kada ki damu in sha Allah he is safe”
kai ta gyada asanyaye,sai ta kasa qarasa ci gaba da aikin ta biyo bayan mami ta fita a kitchen din ta koma dakinta ta kwanta
Maganganunshi na qarshe ta dinga tunawa
”Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo da ni,kimin addu’a don muhimmin aiki zan gabatar,wanda ko shine aiki na na qarshe da zan aiwatar in sha Allahu sai na gabatar da shi,ki sakani a addu’o’inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam”
Wani irin juyi tayi cikin matsananciyar faduwar gaba ta tashi ta zauna sosai kan katifarta,sai taji kanta ya sara ta dafe goshinta da sauri kana ta maida jikinta fuskar gadon ta jingina
kusan wuni tayi sukuku zuciyarta ba dadi,duk motsin da tayi maganansu ya qarzhe a airport ke mata amsa kuwwa a kunnenta,ko falon bata sake fitowa ba saboda rashin kuzari,mami keta leqota don kada ta takure ranta ta sa damuwa,ta karanci wani kalarson abdallan mai qarfi cikin zuciyar maryam din,da taga ta leqo ta sai ta qirqiri murmushin dole,gaba daya walwalarta ta ragu,ta dinga kiran layin abdallah a jejjere kamar wadda aka bata aikin yi amma ko da wasa bata shiga ba is switched off computer keta faman gaya mata,
Cikin kwana biyu duk yadda taso hana kanta damuwa zuciyarta tace batasan wannan ba,bata taba jin damuwa irin ta wannan lokacin ba,bata taba jin ta damu da wani abu a rayuwarta ba kamar wannan lokacin
cikin kwana na uku ta gaza daurewa
fitowarta a wanka kenan wanda tun safe ta kasa yinsa sai kusan daya na rana ta samu tayi,mai kawai ta shafa ta fesa turare ta zira doguwar riga ta nade kanta da mayafinta,takalmanta plate ta jawo ta saka kana ta fito,babu kowa bangaren don mami ta fita asibiti don haka ta fito waiting parlour ta zauna tana kallon shigewa da ake tayi da sabbin furniture bangaren nene a da,bata cikin nutsuwarta batasan wa zai zauna anan ba bata kuma damu data sani din ba,abinda ke cunkushe kadai a ranta ya isheta jarraba
number din hisham ta laluba ta kirashi,daga yanayin yadda taji sun gaisa har yana zolayarta ta tsinke da lamarin,sai kawai ta fasa tambayarsa ta kashe kiran,lambar abdallah ta sake trying wanda ta maida kiran tamkar ibada a gareta saidai amsar daya ce kamar kullum is switched off,ita kanta ta fuskanci yanayin damuwa kan fuskar mamin duk da bata kai tata ba,jin zuciyarta take kamar ana hura mata wuta
son abdallah
kewar abdallah
duk su suka mata rubdugu,kalamansa na qarshe a gareta ke sake sanya mata karaya,kawai sai ta zame a gun ta kwanta rub da ciki,batasan ya akayi ba ta tsinci kanta ne kawai tana kuka tuquru,bakinta na fadin
”kada ka yimin haka abdallah,kada ka guje ni,kada ka tafi ka barni”take furtawa a hankali cikin kuka,Allah ya taimaka mutanen dake aikin kafa kayan furniture din sun kammala sun fice
Kuka tayi mai yawan gaske har yasa idanunta suka kumbura baya ga zafu da radadin da suke mata amm hakan baisa ta haqura ba,sai da bacci ya lallabo ta taimaketa ya saceta,bacci ne mara dadi wanda tana yinshi tana sayke ajiyar zuciya ma kukan da ta yi
Hannu taji kan wuyanta a hankali ta soma bude kumburarrun idanunta wanda hasken daya cika falon yasa ta gaza budeshi gaba daya,mami ta gani tsaye a kanta tana fadin
”bacci kuma a waiting parlour maryamu?”ta tambayeta ba tare data lura da yadda idanunta suka sauya kala ba
”tashi ki koma daki idan baki gama ba kiyi a can amma nan ai yayi waje”
sosai tayi qoqarin tashi amma ta kasa,ga zaton mamin magagin bacci ne don haka ta kama hannunta don tayata tashin,zafin da taji da hucin zazzabi ya sata furta
”subhanallahi,maryam me ya sameki haka?”sai a lokacin ta lura da yadda idonta ya suntume fuskarta tayi jawur
”ya salamu ya Allah,maryam”mamin ta fada a rude,zare wayar hannun maryam din tayi don ta miqar da ita,number din abdallah ta gani kan scrren din wayar,sai ta dubi maryam din
”abdallah dai maryam?duka a kanshi kika yiwa idanunki haka?,sai kace an ce miki ya mutu ne”kalmar mutuwa data ambata wa abdallan sai ta sake karyar mata da zuciya,take taji ko,mutuwar ma yayi ne tunda gashi mami ta fada?,sabbin hawaye suka soma tsiyayowa,sai mamin ta dafe kanta don ta fuskanci abinda ya sakata kukan
”babu abinda ya samu abdallah maryam,tashi maza mu shiga ciki ki je ki watsa ruwa ki karbi magani,zafin zazzabin nan yayi yawa kada ya zama wani abun kuma daban”
mamin ce ta taimaka mata har ta shiga toilet kana ta fita ta bar mata dakin ta haye samanta don tayi wanka,itama ta hada mata magungunan da zata sha da zai saukar mata da zazzabin,zuciyarta fal da fafinciki jinjinawa da yaba tsaftatacciya kuma ingattaciyar qauna kuma mai qarfi da ya samu daga gun matarshi,wanda tayi imanin koda bafa duniya zai samu kyakkaywan kulawa a rayuwarshi



