ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta kammala watsa ruwan ta canza kaya,da qyar ta iya bada sallar azahar da la’asar da suka shigeta ta dawo ta nade a gado,har yanzu zazzabin tana jinsa cikin qashinta,a haka mami ta taras da ita
Sai data tilastata taci abincin da ta shigo da shi sannan ta bata maganin ta sha,tana nan a gurinta har bacci ya sake daukarta sanann ta fita dakin
Bata farka ba sai da wani amai mai zafi ya farkar da ita,da gudu ta miqe kanta na sarawa ta shiga bandakin ta dinga kwarashi,mami wadda ta idar da sallar magariba tana jiran isha ta dawo falin qasa ta zauna saboda maryam din ta fara jiyo kakarin amai,da hanzarinta ta shiga dakin,ita ta wanke gun data bata din ta maidata gado ta kwantar tana mata sannu,ta taba jikinta kana cikin damuwa tace
”maryam anya ba ciki gareki ba kuwa?”
duk da tana cikin ciwo sai da tambayar tq bata kunya,tayi qasa da idonta tana girgixa kai,sake matsowa mamin tayi tana lallabarta
”kada kiji kunyata idan shine ki gayan kada na yita baki magunguna muyi asararsa don Allah”
nan ma kai kadai ta iya girgiza mata ta kasa hada ido da ita
”to shikenan,allura dama zan miki naji zazzabin yaqi sauka”
sam bata qaunar allura,da kayi mata allura gwara ka zabga mata mari,ita ta sani ciwonta ba na magani ko allura bane,da sauri cikin murya ta marasa lafiya tace
”don Allah mami ba yanzu ba,a barshi sai anjima zai iya sauka”ta fahimci allurar ce bata so don haka ta qyaleta ta sake bata wasu magungunan
Ranar kam har kusan biyu na dare ana fama,qarshe dai allurar da bataso mamin ta mata,bayan tasha fama da ita kafin ta tsaya din,sai kusan uku saura na dare ta samu bacci ita kuma mamin ta koma dakinta
????????????????????????
A daddafe ta tashi tayi sallar asuba sakamakon baccin daya cika mata ido,duk da zazzabin ya sauka baki daya sai ciwon kai dake son matsanta mata kuma,da qyar ta gama sallar ta kwanta saman daddumar zuciyarta babu dadi,duk wani minti idan ya wuce sai taji kamar yana sake nesantata da abdallah ne
A hankali taji an turo qofar dakin,ta daga kai tana amsa sallamar da akeyi,mami ce cikin hijabinta da carbi a hannunta da alama idar da sallarta kenan itama,tayi qoqarin tashi zaune don gaisheta mamin tace a’ah yi kwanciyarki,a haka suka gaisa ta duba jikin taji babu zazzabin,shuru tayi bata ce mata kan nata na ciwo ba din kada ta daga mata hankali
”yanzu maryamu jinkirin dawowar abdallah yasa kika matsantawa kanki da damuwa haka har da ciwo?,lallai ba shakka gaba guduwa zaki dinga yi kibi mijinki kuna barina kenan?”ta fada cikin tsokana da zolaya,kunya ta kama maryam sosai,ita kanta batasan tana misbehaving har haka ba,batasan ya akayi abun ya hudata haka ba har yake bayyana kanshi da kanshi ba tare da ta sani ba.
”a’ah daina jin kunyata,ni hakan dadi ya yimin sosai,Allah ya qara hada kanku,aikin da yayi ne ya tsaudashi jiya kafin na kwanta saiga kiranshi,amma alhamdulillahi an samu nasara ya kama dukkan jama’ar daya shirya kamawar sai mu yiwa Allah godiya”
hakanan taji wani sanyi na sauka tun daga kanta har tafin qafarta,a gida ko a waje abdallah jarumi ne tabbas babu kokwanto,a hanakali cikin zuciyarta ta dinga fadin alhamdulillah
”sai ki kwanta kiyi naccinki sosai,kiyi bacci harda minshari ko”ta sake fada cikin zolaya,murmushi tayi tana sake sunkuyar da kanta mamin ra mata sallama ta fice
Ta lumshe idonta tana jin wani shauqi na kamata,duk da ciwon da kanta yake murmushi sai daya subuce mata,ta dan dafe kanta idanu a lumshe,a hankali bacci mai dadi ya sureta
????????????????????????
Sannu a hankali taji yanayin baccin nata na sauyawa,ta dinga bude idanunta a hankali har ta kammala budesu tas,yana zaune gefan gadon nata sanye da baqar jallabiya mai hula irin ta maza ya zuba mata idanu kamar wanda aka bashi aikin zana fuskarta,wani abu mai kama da farinciki taji ya ratsata
”welcome dear”ya fada a nutse
”an tashi lpy gimbiya?”ya tambayeta idanunsa har yanzu na kanta,kasa amsawa tayi sai cusa kanta da tayi cikin hijabinta,yayi maganar amma taqi dagiwa sabida haka ya tashi tsam ya koma gabanta yana qoqarkn dago fuskarta amma ta qiya,shima bai sakar mata qarfi ba ya qyaleta yana fadin
”kin daga min hankali da yawa baby,tun asuba na baro abuja duk sabida nazo na ganki amma kin min rowar fuskarki,shikenan na gode”ya fada yana miqewa zai fice a dakin,sai ta bude ido daya taba satar kallonshi tamkar ta tsaidashi tana kallo ya fice a dakin a hankali kamar wanda aka qididdigewa iya takun da zaiyi
Kunya da tsoro ranar suka hanata sakewa ko fitowa,sai taci gqba da kwanciyarta kan gado abinta mami na kulawa da ita a tsammaninta jikin da saura,tana son ta fito ko zata sake ganin fuskarshi amma kunya ta hanata,tana jiyo muryarshi a falo lokaci lokaci shida mami suna maganar bangaren nene da ta ga ana sawa sababbin furniture
_WASHEGARI_
Tas ta jita ta warke sosai,ko guntun ciwon kan ma babu shi,qarfe tara ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,muradin ganin abdallah take,shi kuma kamar ya sani tun jiyan bai sake leqota ba duk da ya turo mata guntun sms
sorry dear na zama busy kan wani abu,see u later,iya abinda ya turo kenan
Ta shirya cikin atamfa riga normal da zani rafa,tayi lite make up kana ta feshe jikinta da turaruka masu dadi,ta daura dankwalinta bayab ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici,haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar,ba qarya ta mata kyau matuqa,muryarshi da jiyo a parlour ta haifar mata da fargaba,sai ta koma bakin gado ta zauna ta fasa yunqurin fitar da takeyi,ta dauki wayarta ta fara danne danne kanta a qasa
Raliya take turawa tex don taga missed call dinta na kiran data mata tana bacci
A hankali taji ana taba qofar kana aka turota,cikin qananun sakanni tattausan qamshi ya buwayi hancinta,qamshi ne mai kwantar da rai tamkad zai saka bacci a nata bangaren wani shauqi ya qara mata,kallo daya ta masa ta sauke idanunta qasa,kunya take ji sosai,ga wani maganadisu dake fisgarta cikin idanunshi,wani kyau na musamman taga an qara masa,gani take kamar mami ta gaya masa sirrinta,nauyin hada ido take da shi,yayi kyai sosai cikin light blue din shadda,babbar riga da yar ciki da wando,fadan irin kyawun da shaddar ta masa ma bata baki ne,shadda ce yar ubansu sai maiqo take tasha bugu,a hannunshi riqe da hularse,a gogone baqi a hannunshi na fata na kamfanin armani sai takalminsa half cover irin na maza,sai ya tashi sak dan kano don ba baya bane su wajen iya wankan shadda suna sahun gaba,ba qaramin amsarsa shigar tayi ba,do da wuya ya sanya kaya komai rashin kyawunsu suqi amsarsa ,fuskarsa cike da murmushi mai bayyana sirrin kyawunshi
”amincin Allah ya tabbata a gare ki baby,ina fata kin wayi gari cikin qoshin lafiya,af kice ma anko mukayi”ya fada cikin zolaya,sai a sannann ta dubi kalar atamfar da ta saka blue ce da baqi,duk da blue din ya dan dara nashi turuwa da kadan
qarasowa yayi bakin gadon ya tsugunna kana ya dafa cinyoyinta,abinda taji a jikinta shima shi yaji,sai tayi saurin zame hannun nasa,dauke hannun yayi yayi murmushi yana yiwa hular hannunshi kari ba tare da ya dubeta ba
”am too busy jiya naso inzo in sake tozali dake,ina daya bangaren can ana jeran amaryata”
sai tayi dumm ta rasa yadda zara fassara maganarshi