MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kallonta tayi daga sama har kasa kafin ta kada kai tace”Yana Falon bakinsa na kasa,yayi bako ne..”kada kai Malika tayi batare datayi mgana ba Tanufi hanyar Falon tana tafe Gabadaya Hip dinta suna kadawa kamar wata karuwa baki Hajiya ta rike kafin ta bita da sauri ta rikota tana Fadin”A”a malika don Allah karki je ahaka kikoma ki Suturta jikinki don Allah…”
Wani kallo tayi mata kafin ta waigo tana Fadin”Found of corection Hajiya,in Suturta jikina fa kika ce? yanzu ina yawo Tsirara ne..? tafada cikin mamaki tana bin kanta da kallo.
Hajiya binta tayi saurin cewa”Bance kina tsiraraba,nufiba kije ki sanyo ko dogowar riga ki Rufe wannan kayan don Allah…”,Tsaki malika taja tana Fadin”,excuse me Hajiya..”Tafada tana zare hannunta dake kafandanta ta wuce tana wani kada kai kamar wata kadangaruwa.
Fadowa kawai tayi Falon babu sallama,sai dai Alhaji Abdulmalik yaji kikam ta Fadomai ajiki ta Rumgumesa bayan ta sakarmai kiss agoshi tace”Daddylove i miss u…”
Tunda Alhaji Abdulmalik yake da Malika bai taba jin kunyar Hallayarta da banzan Dabi”arta ba irin na yau,duk kunya Abbi ta kamasa,wanda yayi kasake yana binsu da kallon mamaki
Mirmishin dole ya saki yana riko hannunta yace”Me too my Sweetbby,kin tashi lafiya..? baki tawani mele kafin tace”Fine Daddy…”Tafada tana kara gyara zama bisa cinyarsa idonta kur ana Abbi ammh baisa ta gaisheshi ba,duk ta ganeshi tana ganinshi albarai amtsayin IGP na Nageria gabadaya ammh ko agefen gyalenta,duk atunanin yazo maula ne wajen mahaifita tunda haka take kallon kowa.
Alhaji Abdulmalik ne yace”Aermmm Sweetbby baki gaida bako na ba? Shima Abbanki ne,tsohon abokina ne,tare mukayi gwagwarmaya dashi a jami”ar Sokoto yanzu kuma Kinga yadda Allah ya maidashi shine inspector general of police na kasa gabadaya…”,idonta kur akanshi kafin ta dauki Farin hannunta ta mikamai Tana Fadin”Hy….”
Ai ba Abbi ba,har Alhaji Abdulmalik yaji ya muzanta da Abunda malika tayi kunyar Duniya duk ta kamashi,shiko Abbi mamaki tare da al”ajabi sun kamashi,lokaci guda kuma tsausayi suka bashi daga uban har yar domin zahirin gaskiya rayuwarsu na cikin tabewa.
Mirmishi ya sakarmata bai mikamata hannun ba yace”kina lafiya…”,Kai tadaga kafin tace”Fine….Same….”Tafada kafin ta mike tana Fadin”Daddynlove let me go, Zanje nayi breafsat sai ka shigo…”Dagahaka ta juya tana Tafiya Ko”ina na jikinta na rawa mussaman ma hip dinta,da hanzari Abbi ya kauda kai yana Ta’awizi aransa ayayinda Alhaji Abdulmalik ya sadda kai kasa yana jin wani iri aranshi.
Abbi ne ya kaunda Shuru da jansa da wata hira shiyasa yadan saki sai da yaga haka kafin yace mai”Wannan itace malikar..? da kai ya amsa mai kafin yace”Yes itace,my dota ina alfahari da ita,domin acikin kaso mafi yawa daga Dukiyata samuwarta ya samo asali ne daga jajircewarta…”Jinjina kai Abbi yayi kafin yace”,Gaskiya ne kenan ita ke Lura da komai yanzu,kai kana gida kenan..”Girgiza kai yayi kafin yace”Eh gaskiya kusan komai ita ke zuwa ta gabatar takuma tabbatar,wani lokacin sai akirani ta waya mu jadadda bayani,ammh gaskiya yanzu ragamar komai na hannunta don jiya tadawo daga london ma,kan mganar wani kamfani danike da hannu jari dasu..”
Shuru Abbi yana jinjina kai kafin ya kalleshi kai tsaye yace”To kana shirin aurar da ita kuwa Abdulmalik…? Kuri yayimai da ido yana kallonsa gabansa na Faduwa,ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Ban taba sanar da wani wannan mganar ba sai kai kumo,wlh inason malika tayi aure saboda cikar mutucinta,ammh mtsala dayane Malika ,banta ganinta dawani Namiji da sunan suna soyayyah ba,kai infact ma nataba mata mganar aure nace yakamata tayi aure,sai ta sanar dani ita Batasan ma miye aure ba,ta,zauna karkashin wani ? to indai hakane har abada bazatayi aure ba,Abun na damuna sosai kumo narasa yadda zanyi ne..”Yafada muryansa ta chanza kamar yayi kuka.
Riko hannunsa Abbi yayi yana Fadin”Meyasa? ai batafi karfinka ba,in ka Tursasa mata dolenta tabi Tunda kana matsayin mahaifinta,ammh cigaba da rayuwa haka Bazai yuyu ba,domin Duk ranar daka mutu wlh sai Allah tambayeka game da kiwon da kayima yarka..”Shuru yayi kafin yace”Bana iya Tursasa babby tayi abu,saboda ban son Abunda zai mata mata rai,zan dai gwada lallashinta,toh in ma ta yarda ina miji,nifa tsoro nakeji yanzu samarin zamanin nan duk ba don Allah suke aure ba,sai domin hannun jari,kuma samun Tsayayye jarumi wanda zai tankwasa Malika abu ne mai Wuya koni mahaifinta bana iya tankwasata toh balle wani..”Yafada cikin zafin rai,ashe Abun na damunsa bai iya Fadane.
Ajiyar zuciya Abbi ya sauke aransa yana Fadin”An zo wajen…”gyara zama yayi kafin yace”indai wannan ne baka da damuwa,in ka yarda ina so zan neman ma Da’n wajena aurenta,i know My son very well zai iya Zama da ita harma daga karshe zamansu yabamu mamaki..”(Ya sanar dashi hakane saboda bayaso yace Saleem ne yace yana son Malikan,wanda dole zai zargi wani abu..)
Kallonsa Alhaji Abdulmalik yayi bakinsa duka abude saboda Farinciki gefe daya kuma fargaba yakara damke hannunsa yana Fadin”Da gaske kake kumo..?,Gyada kai Abbi yayi kafin yace”Da gaske nake indai ka amince sai mai tattauna mganar…”Rumgumesa kawai Alhaji Abdulmalik yayi yanajin kamar yayi kwallah yace”Ngd ngd…Kabir kumo,hakika ba iya abota kakesona dashi ba,kai masoyin gaskiya ne,Tun lokacin muna mkranrta tare dakai,naji kunya lokacin da kaga irin rashin tarbiyan da Malika ta maka,ammh duk da haka bakaji komai ba,kakeson hadata da Danka wanda ko da banganshi ba,nasan yatara abubuwa dama kumo,sanin da nayi maka mai tarbiya da ilimi da hangen nesa nasani cewa bazaka bar zuru”arka haka,hakika kai abokina ne na nagari,ni kaina ina son Malika ta chanza kumo,ammh ya zanyi domin Na bar Shiri Tun rani,dana barta hannun dangin mahaifiyarta ta girma,duk shi yakara maidata haka..”Yafada yana sharbe kwallah kafin ya dago yana kallon Abbi.
Mirmishi yayimai yana Fadin”Babu komai wlh,dama ita rayuwa haka tagada,ammh kaima danaga kuskuren data dawo wajenka bai kamata ka sakarmata ba Abdulmalik,ita Diya mace ba”a barinta haka ko Da namiji ya fandare balle mace,macen ma wacce ka sakarmata komai sai yadda tagama takeyi…”gyada kai yayi kafin yace”Ko baka Fada ba i know iz my mistake,bana bari wani ya sanar dani haka kabir saboda bani son Abunda zai dagamin hankali,kai ne mutum na farko dake sanar dani kai tsaye nayi ba daidai ba na gyara hakika nagodema Allah daya hadani dakai,yanzu kabar mganar komai ahannuna komai ke akwai zamu mganata ta waya buh yanzu in ka koma ka Turomin yaron wajen naka sai muyi mgana..
Hannun Abbi yabashi suka sarke yana Fadin”Masha Allahu,to ai bakomai zan sanar dashi insha Allahu…”Yafada yana bayyanar da murnansa,nan suka cigaba da tattauna al”amarin Alhaji Abdulmalik nata sanar dashi damuwarsa game da wasu dabi”un Malika bai iya boyemai komai ba,hatta ayadda abagaren addinin bata san komai ba,batayi iya komai na rayuwa ba,gazuwa club da Party ga rashin salla akan lokaci,Bata son komai sai rayuwar gata da jin dadi,yana Fadamai yana kwallah domin iya shekaru daya dauka da wannan takaichi bashi da wanda sai sanarmawa saboda duk Abunda malika tazama ayau Shine silan komai,Hakuri Abbi yayi tabashi yana sanar dashi insha Allahu zata gyaru.