MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yafada Yana jadda  kalamansa,Kukane ya kwacemata ta isa gareshi ta rumgumosa tana Fadin”Kayi hakuri yallabai,wlh nakasa sarrafa zuciyata ne na ganin Saleem ya auri yarinyar nan, da Duniya tagama saninta afannin rashin tarbiya da kamewa mezan cema yan’uwana da kawayena? wlh Abun kunya ne babban Amtsayinka na mai mutunci aji mun hada zuru”a dasu,sai ma afara zargin kila kwadayin Dukiyar mahaifinta ne ya Tsolemana ido…

Tana Fada tana Sheshshekan kuka waigowa yayi yana rikota gefen gado ya zaunar da ita yana Fadin”kalle ni nan Aisha..”kai tsaye ta dago tana kallonsa hannunsa ya mikamata ta kama kafin yace”Tun sanda kika zamo mata nake mika miki hannuwa na domin ki kama,yazama bango da majingini gareki,kuma har gobe zan cigaba da mikamiki ,Toh yau gashi na kara mika ,mi ki ki kama ki damke yazama kariyarki har gobe kiyama ki kuma saka aranki indai Dan dani Kabir na haifa tare da Aisha ne bazai zamo gafalalle ba,sai da ikon Allah,na yarda da zencenki na za”a ce ko muna hangen Dukiyar mahaifinta ne,yes Alhaji Abdulmalik yana da tarin Dukiyar da baisan yawanta da karshenta ba,ammh wlh tallahi Aisha Dukiyarsa bata taba tsolenmun ido ba,mena nema na rasa,akwai Abunda bazan iya mallaka bane anan Duniyan…?Babu shi to kisa aranki Da zuciya daya na yarda da wannan auren,ki kuma toshe kunnuwanki daga zencen mutane,dama wasunsu dayawa basu son akullah alheri,ki kuma yi kyakyawan zato ga Danki,kinsan Abunda zai aikata da wanda bazai aikata ba,don Allah ki Cire wannan Tunanin azuciyarki kisama auren nan albarka kuma ki Rufe kofar da wani zai kawo kushen wannan Auren don Allah….,”

Yafada yana kara damke hannunta hawaye ne suke shatatamata kawai sai tafada kan kafadansa tana Fadin”Na yarda kuma na saka musu albarka…Allah ya sanya alheri,ka yafemin yallabai,Akullum ina alfahari da samun miji gwarzo kamar ka,lokacin da na nemi kauce hanya sai kayi saurin dawo dani,Allah yabani ikon Yima biyayyah har karshen Numfashina,Allah kuma ya Shiryamana Zuru”a….”Da Ameen yayi ta karba bayan ya sanya hannu yana Sharemata hawaye yake Fadin

“Toh bar kukan hakan,Fushi ya kare ko…”Yafada yana dariya Kirjinsa ta fada tana Rufe fuska wai ita kunya,yar dariya yayi yana Fadin”A’eesh dita har gobe bani da kamar ki AISHATUL HUMAIRA…”Yafada yana Mata rada akunne,Rumgumeshi tayi itama tana mai rada akunni,nidai nayi waje Tunda dai naga ma”auranta sun daidata kansu dole na ja Siraran kafafuna zuwa waje????

________

Tundaga Ranar Ummi ta fauwalama Allah komai ta karbi Auren saleem da hannu biyu,wanda harshi sai da takira tana mai Tsiyan yana Fushi da ita kwaso rantsuwa yayi yana bata hakuri,dariya kawai tayi tana sanyama auren albarka,aransa bai amsa da Ameen ba,don cewa yayi ai dama baki sakko ba Ummi,don ba auren gaske bane,na Ramuwa ne kawai na awannin kadan,ammh duk da haka bata makara ba????

Saleema ko kwana uku takara takoma mkranta bayan taga gidan gabadaya anhada kai babu mai goyon bayanta,Ummi ce toh itama yanzu tabi bayan mijinta,Hajiya kuwa batama sauraran mutum indai ta Fahimci zai kawo wata sukane game da auren Saleem,shiyasa ta tattarara kayanta Takoma mkranta,kuma tayi alqawarin ko bikin yatashi wlh bazata zo ba,indai da wannan Jinin Turawan ne.

Ita ta kira ya marwan ta sanar dashi,wanda yaji Abun kamar almara,nan da nan ya hau Shafin instergram,ya bude shafin Malik malik,nan yaga badala kala kala nata,Tunda abokan aikinsa sunsha Tuka jirgin data ke ciki ita da Amintattun Escorts dinta,ammh shi bai taba katari da shegiya ba,duk da yasan lbrinta ba boyayyiya bace,anan nema yake ganin Jiya da misalin karfe 2:00pm jirgin daya tashi daga Abuja zuwa Amurka tana ciki wai tatafi tarin karama yan kasuwa sani da Duniya gabadaya ta Shirya akasar ta Amurka,irin hotunan data daura da shigarta Abun ba kyan gani,nan da nan zuciya ta debi Marwan ya daga waya ya kira Ummi yana Kumfan baki tana gani Saleem zai auri wannan Shegiyar yar iskan yarinyar.?

Ashe Abbi na kusa yako karbi wayar yayima Marwan din Fata fata daga karshe ya bishi da Nasiha mai kashe jiki,shima din jikinsa yayi sanyi Domin yasani Shi da Allah ya Shiryar dashi bayafi sonshi bane,haka Allah yake Abunshi shi zai raya wanda yaso,kuma ya kashe wanda yaso,shi zai Shiryar da wanda yaso,Allah shike da ikon Umartan Faruwan Abu nan take kuma ya Faru ko ya kasance,ya sanar dashi ko ya manta kissan Annabin Allah Annabi Yunus wanda yayi Fushi da mutanensa ya baro garinsu zaiyi hijira ya Shiga jirgi sai aka ga jirgi na tangal tangal,nan masu jirgin sukace akwai wanda yayima Allah laifi acikin Jirgin,nan suka ganoshi suka jefasa cikin kogin,shikuma Allah nan da nan ya Umarci Kifi data hadiyeshi,ya sanar dashi Allah yace acikin alqur”ani mai girma ba domin Annabi Yunus yanemi gafarar Allah ba da ya dauwama acikin cikin kifin nan har ranar tashin kiyama.

Hakuri yayi ta bama Abbi,domin Hakika duk Abunda ya Fada gaskiya ne, domin sau nawa zamu dunga aibata yan”uwanmu da jifansu da  munanan kalamai a maimakon murika musu Fatan Shiriya tunda munsan babu mai batarwa,kuma ya Shiryar sai Allah,kuma hadisi ne ingantattace sau tari Mutum zai Fara aiki irin na yan Aljannah sai yana gabda mutuwa aikinsa ya juye yakoma na yan Wuta kuma ya mutu ya shiga Wutan,ALLAH YA KAREMU…Kuma sau tarin mutum yana ta aiki irin nan yan Wuta kwatsam sai yakoma aikin yan aljannah,kuma ya mutu alokacin ,sai kuma ya Shiga Aljnanah,to mai zamu ce da haka? musani Aibata wani mumina ba dabi”a mai kyau bane.domin babu wanda yasan tsakanin Ubangiji da bawansa…

Allah ka shiryemu kabamu ikon sarrafa zuciyarmu ta hanyar mai kyau

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Shakira

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

8

  “Yana zaune cikin Office dinsa aiki ya kacame mai Sargent musa ya shigo agabansa ya tsaya hannunsa asaman kansa yana Fadin”Weldone sir….”

Bai dago ba ya amsa da cewa”Weldon..Arm ya”aka yi ne Sargent musa..? Baya yaja yana Fadin”Yallabai kayi bako ne,yana waje yana son ganinka,ya shigo ne..?”Shuru yayi kafin ya dago yana Fadin”Bako kuma? Who…? Sargent musa yace” I don”t know sir buh kamar naga na gida ne”Tsaki yaja kafin yace”Let him in,buh dagashi bazan kara ganin kowa ba gaskiya a hv alot to do,koda wani ne yazo yana son ganina matukar iz not imfortant,plz tell dem bani nan ok…”saramai yayi kafin yace “Yes Sir…” Ya Fice da Hanzari,shiko yamaida hankalinsa kan karamar syestem din dake gabansa wanda da alamu dai Abunda yake yaja ra”ayinsa.

Sargent musa bai dade da Fita ya Turo kofar office din ya Shigo yana kwarara sallama.”Assalamu Alaika…”Aka Fada ana yar dariya,Dago kansa yayi ya Jefa cikin na mai sallaman,kai tsaye bayan ya dauki hannunsa wanda ke rike da pen yana sosa gemunsa dashi yana kara kallonsa kasa kasa,shiko Sadiq dariya Abun ya bashi ammh sai ya doje, ya karisa yana Fadin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button