MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Daga haraban gidan kuma ya Faka musu Tafkakan motoci guda biyar Biyu na saleem,Uku na Malika na saleem Daya prado ce,sai dayar kuma matrix ce,sai ta malika Komferesor ce,607 kirar piagion,sai Accord,motocine na gani na Fada,kuma dukkansu sabbi ne, daga kwatano aka shigomai dasu diret kuma nan aka killacesu domin ma mallaka motocin sune zasu Shiga wanna kayatattacen gidan mai kama da Aljannah Duniya.
Lbrin Auren bai Fita waje ba,saboda tsoron kada lbri yakaima Malika tun tana chan,kuma jin hakan zai iya sakata taki dawowa gida ta Shiga Duniya yasan halinta sarai,shiyasa bai yarda gidajen Yan jaridu da sauran kafafan yada lbrai sunji batun baba,so yake sai bayan an daura sai afasama Duniya taji komai,Shiyasa Tun sauran kwana biyar da bikin Sukayi waya da Malika wacce daga Amurka,Babban birnin America ta Wuce U.S Taje kaima abokan karatunta ziyara,dagachan kuma england ta wuce wajen Dangin mamarta,Da sukayi waya sai ya sanar da ita tadawo gida nan da kwana biyu saboda akwai Suprise din daya Shiryamata bata kawo komai ba ta sanar dashi Visarta take jira,tana bisa hanyar Dawowa.
Ana gobe biki gabadaya duka bangarorin biyun gudajensu ya cika da yan”uwansu,na kusa dana nesa, Gidansu Saleem Tuni yan kumo suka hallarta mata anata shagali,ayayinda katsina kuma yan malumfashi kwansu da kwarkwatansu sun hallata mata da maza,saboda bikin dai zahirin batu za”a yi wadaka da abubuwa domin komai mota ke saukeshi kama daga ababen sha,da kuma snacks da sauran Abinci kuwa tun ana saura kwana uku da biki wani kayatattacen restaurant ke yo odar suna kawowa gidan,Abun sai wanda yagani
Joda ma ta iso Tun jiya domin Amminta na sanar da ita tayi alqawarin kallo bazai Wuceta ba,so take ga shin waye mijin na malika,kuma ya malika zata kare matukar taji Abunda mahaifinta ke kulla mata? duk ta anada tambayoyinta ne shiyasa ta tadawo daga mkranta da hanzari domin ganema idonta Abunda ke Faruwa koma nace yana kan Faruwa..
Daga Amaryar har Ango sai daren Daurin Auren suka iso gidajensu,wanda suka tararshi cike da jama”a Saleem bai damu ba domin yana da masaniyar komai,Sadiq ne Maye Tun safe ya iso ya dinga jeramai wayar Shuru haryanzu bai ganshi ba,Shiko yayi niyar daga zamfara su hadu aktsina ne,Ammh ya kama damunshi yasa har Abbi na kiransa,Wani Abun mamaki bai dade da zuwa ba,sai ga ya marwan ya kariso shima,wanda kwata kwata saleem bai so ba,yaso ne kowa yayi zamanshi don zuwan fa harga Allah baida wani amfani,saleema dai tace ayi biki lafiya ammh bazata samu zuwa ba haka ta gayama Saleem shiko yace Gaskiya tayi Dabara don baya gayyatan irinsu dama.
Malika ko koda adawo taga dangin Abbanta bata wani damu kanta ba, domin tariga ta raina musu arxiki duk azatonta anzo Maula da cin arzikin da”a ka saba ne,shiyasa bayan sun gaisa da Abbanta ta Shige dakinta bata kara lekowa waje ba don bata son hayaniya sam,kuma ko aranta bata kawo wa ita aka taru ba, domin ko amafarki batata zaton hakan zai Faru da ita ba.
WASHEGARI..
RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA…… Ayau Jumma”a 17/1/2020 Dubban Mutane suka Shaida Daurin Auren MALIKA ABDULMALIK DANKASUWA Da angonta ACP SALEEM KABIR KUMO Akan sadaki Naira Dubu Dari Hudu da hamsin wanda mahaifinshi ya biya da hannunshi ayayinda wani Baffanshi dake kumo ya karboma Saleem Auren,Itakuma malika Kawun mahaifinta dake Malunfashi ya bada aurenta,wanda ya gudana Ababban masallacin jumma”a dake garin katsina.
Daurin Auren daya samu hallartan manyan mutane,kama daga kusoshi agwannati,yan kasuwa manyansu da kananansu,kungiyar direbobi,kungiyar Kwadago ta kasa baki daya,Sevil defence,yan mofal,Yan sanda manyansu da kananansu sun samu katin gayyata zuwa wajen wannan Daurin Aure,sai bayan da”aka Daura aure ne, kana Alhaji Abdulmalik Dankasuwa yabama yan jaridu,da kafar yada lbria sanin Abunda ke Faruwa,ko kafin kace kwabo Tuni lbri ya zaga duniya ta ko”ina Kowani Shafi ka bude na wasop,instergram ne,Fbuk,twitter,duka lbrin zaka gani yana yawo da cewa” WANI ABUN MAMAKI AYAU MUKA GA TARON DUBBAN JAMA”A WANDA SUKA HADA DA KOWANI MUKAMAI AFALIN JAHAR NAN ANA GUDANAR DA DAURIN AURE BAYAN AN SALLAME SALLAR JUMMA”A ABABBAN MASSALLACIN JUMMA”A DAKE LAYOUT,SAI BAYAN KAMMALLAH DAURIN AURE NE, MUKA SAMU LBRI DAGA BAKIN SHAHARARREN DANKASUWAN NAN WATO ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA INDA YAKE SANAR DAMU DAURIN AUREN DIYARSA CE WATO MALIKA MALIK,TARE DA ANGONTA ACP SALEEM KUMA,WANDA D”A YAKE GA INSPECTOR GENERAL OF POLICE NA KASA GABADAYA WATO IGP KABIR KUMO,SHIN YAYA MUTANE ZASU DAUKI ABUN,ACE DAURIN AURE YA”YAN MANYA KAMAR IGP KABIR KUMO DA ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA BABU LBRI SAI BAYAN AN DAURA AUREN,SHN BAKU TUNANIN AKWAI LAUJE CIKIN NADI..? Haka kowacce jarida ke wallafawa asaman Shafinta kama da leadership,Dailytruth etc.
Shiko Saleem yana gefe shida Sadiq da ya marwan,wanda dukkansu suke sanye da shadda fara taji kyau harda manyan Riguna da hulansu zannah bukar suna ta hannu da mutane,shiko ango tunda aka daura auren yaji wani Faduwar gaba da kasala duk karkashinsa,da wani zumarshi na ramuwa yaji ya Fitarmai aka,yana jin wani Abu mai kama da nadamar Abunda zai aikata ammh kuma bashi da yarda zaiyi domin bakin alkalami ya rigaya daya bushe,Bai ji faduwar gaba sai daya dinga samun waya ta ko”ina da sakonnin Fatan alheri,da kuma tsiyan yayi aure babu lbrin hatta abokan karatunsa da abokan aikinsa lbri yaje musu,Ya marwan ne yake sanar dashu lbri yazaga duniya don harda hotunanshi da Malika ansamu masu hadashi waje daya an dorashi bisa media akasa an saka COUPLES OF D YEAR Shi ahoton yana sanye da kakinsa na yan sanda ne,sanda Sadiq ke numai hoton wanda aka watsashi a Twitter,ya tuna sanda akayi hoton sanda Tsohon Inspector general ke sanya mishi Rank din karin girmanshi ne sanda ya zama ACP abuja akayi hoton,shine aka yanke IGP na lokacin aka hadashi da malika wacce ta ke sanye cikin riga da wando black and white kanta babu dankwal gashinta ta saki jelan ta baya,bayan ta tamke samanshi da band,kunnenta makale da waya,alamar kamar ma tana Tafiya ne,aka yanke hoton aka hadasu, sharrin Na”ura ace tare suka dauki hoton.
Kanshi gabadaya ya dau zafi,barin ma sanda yaga Abbi cikin mutane yana ta gaisawa dasu bakinshi har kunni saboda murna da Farinciki,suna wajen har mutane sukafara watsewa,yan jarida ko sunan suna haskawa abubuwan dake Faruwa awajen kai tsaye harshi sun so suji ta bakinsu ya daure Fuska yaki basu dama,Shiko Alhaji Abdulmalik bayan sungama Gaisawa da mutanen da suka gayyata sai gasu sun jero shida Abbi hannunsu sarke dana juna kowannensu yaci Farar shadda harda malum malum,Fuskarsu na bayyanar da Fara”a da kuma Farin cikin dasuke ciki.
Haka suka kariso wajensu,wanda dukkansu suka zube suna gaishesu,ammh banda saleem don Fuska yayi yaki bude baki gabadaya domin Gabadaya yanzu kowama haushi yake bashi,Alhaji Abdulmalik ne ya Umarcesu kafin su wuce Abuja zai gabatar musu da wani Abu,nan da nan suka shishshiga mota suda tawagarsu sai Gra.
Koda megadi ya bude musu get suka sulala ciki,da mamaki suka firfito suna bin gidan da kallo da alamun dai komai sabo ne kama daga motocin gidan yadda suke lullibe cikin tamfol,Daddy bai yi wata wata ba ya damko hannu Saleem ya zuramai makullaye har guda uku,Tsaye yayi yana kallonsa,shiko kafadansa ya daka yana Fadin”Kowa ya Shaida,Wadandan makullayen naka ne halak malak,daya makullin wannan gidan ne, inda zakuyi rayuwar aure kaida malika,Sauran biyun kuma keys din sabbin motocin dana siya maka ne Gift din Aure amatsayina na Uba gareka…”Gabadaya sai su Sadiq da marwan da sauran mutanen wajen,suka dau kabbara,Shiko saleem suman tsaye yayi aranshi yana Fadin”Kash kayi gaggawa Alhaji,inda kasan Abunda nake shiryama yarka dabaka Bani wadanan kyaututtukan ba…”Ammh Afili ko fadawa jikin Daddy yana matse hawayen karya yana mai godiya,Bayansa yake dafawa yana dariya haka Abbi ma yayi ta godiya,ammh sai da ya nuna dawainiyar tayi yawa gaskiya.