MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Suna Wucewa ya nufi mota yana fadin” Inspector Saleh take me to home now…”Yafada muryansa ya fara rawa saboda bacin rai lokaci daya ya bude gaban motan ya shiga,da hanzari Inspector saleh yayi mgana da sauran yan Sandan kafin shi ya nufi motar ya shiga mazaunin direba yaja sukahau kan titin da Sauri,Suma din dai cikin katsinar suka nufa adaren.
Anguwan LAYOUT suka nufa daya daga cikin anguwannin masu hali dake cikin katsina ta dikko Dakin kara,kofar wani makeken gida motar patrole ta yan Sandan tayi parking Tunkafin motar tagama tsayawa ya bude murfin motan, ya Fita da Sauri yarda yake tafiya kadai zaka gane yana cikin Fushi ne da Fusata.
Inspector Sale ya kalleshi yana kada kai,bai Fito daga motar ba, yamata kwana ya juya lokacin agogon dake hannunsa yake nuna karfe 1:00am na dare,shiko yana zuwa jikin get dinsu yasaka hannu ya shiga bugawa da karfi kamar zai tashi sama,megadi dake zaune gefe gyangyadi yafara dibamshi kamar amafarki yaji bugun get,da hanzari ya mike sanye da yake da uniform irin na yan mopal,koda yaji bugun bai razana ba,Nufar get din yayi yana Fadin”Who iz dis..?
Tsaki yaja kafin yace AM SALEEM FREEKING KABIR KUMO.. Yafada ransa na kuna,da hanzari jikinsa na rawa da bari yabudemai karamar kofar yana Fadin”Am sorry sir did know….”Baigama Rufe baki ba ya wucesa Fuu kamar iska baki ya rike yana binsa da kallo,domin a iya saninsa Saleem baida dabi’ar shariya.
Maida kofar yayi ya Rufe yana Fatan Allah yasa koma miye ya Faru mai dadi yadda yake alfahari da wanda zai gaji Yallabai.
Babbar kofar da zata sadaka da babban falon gidan Abude take,sakamakon ansan komai dare zai dawo yana Shigowa Falon babu kowa yadda yake tafiyane zai ankarar da mai kallonsa kamar agauce yake.
CP KABIR KUMO dake tsaye kofar dakinsa ya kuramai ido yana kallonsa yana neman Shiga dakinsa ne yasa yayi kiransa..”Saleem….”Yafada cikin datattako,Waigowa yayi da sauri yana kallon Abbin nasa,saurin sadda kai yayi saboda kada Abbin nasa ya fahimci halin dayake ciki kakalo mirmishi yayi yana Fadin”Na dawo Abbi…”
Gyada kai yayi yana Fadin”Ai na ganka,ammh why naganga kamar azafafe..? Saurin Washe hakora yayi yana Fadin”la babu komai Abbi,barci nakeji dat why na dawo da Wuri..”Yafada yana Jin takaichin karyan dayayi,kallonsa kawai Abbi yayi kafin yace “Ok sai da safe..”Yafada yana kuresa da ido,da hanzari yace”Sai da safe Abbi…”Yafada yana tura kofar dakinsa ya Shige da sauri,Yana sauke ajiyar zuciya.
Yana Shiga yayi tsaye yana karema dakin nasa kallo,hannu ya dungula ya daki bangon dakin,bayan kunnuwansa suna jiyomai amom muryanta,fuskarsa tana jin zafin karan Tafinta kana idanuwansa suna kallon sanda ta Tofamai miyau,ta watsamai kudi,kana kunnuwansa na jiyomai sanda tace yan sanda basu da wani amfani,sai yima mata fyade da shaye shaye? kenan harda Abbinsa tayi jam”i ? yazama dole ya binciko ko wacece wannan yarinyar domin yayi Saurin ankarar da ita kuskurenta.
Kan gado yafada yana dukan katifan kota ko”ina Yana fadi da karfi..* WLH SAI NA RAMA…”!* yake Fada yana jin wani tukuki daga kasan ransa,har sai da wasu hawaye suka zubomai,yasaka hannu ya sharbe kafin yace”No saleem kuka bana ka bane,juz stand up kayi karatu tukuri domin ka zama DAN SANDA,ka nuna mata cewa ita bata karfin kowa ba,ammh duk hakan bazasu samu ba sai yafara gano ko WACECE ITA…”
Tirkashi….Salon na dabam ne,haka Jimarin na mussaman ne,wannan karon Abun zai taba zukata,wannan karon Abun zai taba kowa ne,Kada Abun ya daure muku kai Abu daya zaku nemo Wacece MALIKA MALIK.!? kuma waye wannan Dan MATASHIN SAURAYIN? miye alakarshi da Aikin yan Sandan? Duk ku biyoni Zan warware muku Zare da Abawa
Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar 09069067488 ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..
Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyi KISHIN MATA na hafnan,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani…
07065481260..Ko kuma 09069067488,am srry a karshen Aliyu gadanga nayi mistake wajen Rubuta nombata maimakon na saka 69 sai na saka 60????Fata zakuman izuri jikin tsufa ne????????????
#Janafty..#
#Intelligent writers asso…#
????MALIKA MALIK????..!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
2
NIGERIAN POLICE FORCE-BIRNIN RUWA ZAMFARA STATE
“””Wata babban Headquater ce mai dauke da haraba mai girma da Fadi,da ban sha”awa,ginin wajen gini mai kyau da tsari domin da Duste aka gina wajen.
Daga haraban Compound din Motocin Police sunfi guda goma Fake,awajen kana ga wasu yan sanda nan na shawagi awajen daga Inspectors sai su sargent suke yawo aharaban wajen Fuskarsu kwata kwata babu Annuri.
Daga cikin Babban ginin, akwai tarin Afisoci kafin kayi gaba karatsa wani dogon lungu ka isa kofar Office din Shugaban Headquater wanda Sunansa yake makale jikin wani dan Anini daga saman kofar Office din, ACP SALEEM KABIR KUMO naga an Rubuta da manya baki,ban tsinke da al”amarin ba,sai da kofar Office din ta wangale kanta,Cak na tsaya ina bin kayatattacen office din da kallo azahirin batu an tsara wannan office din,daga yammah wasu kujeru ne guda uku ga wani karamin center table mai kyau da tsari atsakiyar wajen,kana daga gefe ga wani karamin frigde,mai kyau da tsari,daga kudu,kuma kofar wani daki,wanda yake akulle,daga gabas,kuma wani katon Tebur ne mai dauke da Takardu da kuma Laptop,sai wasu kananun hotuna wanda suke sanye cikin Frame,sai daga chan sama kuma Hotuna ne,Farko na Shugaban kasa ne,sai daya na gwannar Jahar Zamfara,sai guda daya na Shugaban Yan sandan NIGARIA,IGP NA POLICE GABADAYA wato IGP KABIR KUMO..”
Ashe duk wannan Abun kalle kallen danikeyi ma mallakin office din na zaune akan kujeransa irin mai juyawan ne,ta juya dashi yabama kofar Shigowa baya,juyo da kujeran yayi Idanunsa duka suna Rufe ne,kuma dukka hannuwansa suna kan kirjinsa ne,da alamun yayi Zurfi cikin Tunanin dayakeyi,baki na sake ina karemai kallo cike da mamaki da al”ajabi.
Shiba fari bane Bakin mutum ne,ammh Ganin farko zakamai ka zata cewa Fatarshi batayi kama da yan Nageria ba,sai dai tafi chanchanta na yan kasar maroco,saboda yadda tahade tabada wani choculate,na kyau da tsari,doguwar Fuska gareshi sai dai tana da dan Fadi kadan,Hancinsa dogo ne,wanda ya hade da bakinsa karami mai dauke da bakin Sajensa,wanda yakara ma Fuskarsa kyau lebensa Pick ne,yana Fitar da maiko kamar yasanya Man baki,giransa tana cike da gargarsa wanda taso ta hade da yar”uwanta haka gashin idonsa,Bude idanunsa dayayi ne yasa nayi baya ganin yadda Fararen idanunsa suka bayyana awaje,farare kal dasu gasu basu da girma na azo agani ammh suna cike da wani Sirri,mikewa yayi cikin azama yana goya duka hannuwansa abaya yafara zagaya office din yana cije baki,Ashe dogo ne sosai ammh yana da murjewa ta wadanda sukaji dadi da hutu sosai Wadanda ake kira giant,matashin Saurayi dan kimanin Shekaru 28 Aduniya,wanda akallo daya in kayimai zakayi mamakin yadda Yaro matashi mai kananan shekaru kamar sa zai iya taka wannan mtsayin,yana sanye da Uniform dinsa bakin wando da Rigarsa mai launin Ruwan Bula ammh light dinshi,daga hagu dan aninsa ne,mai dauke da Sunansa ajikin bayan gefen duka kafadunsa suna sanye da duka rank dinsa ma”ana amtsayin dayake kai ayanzu.