MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Mikamusu kayan tayi tana umartansu dasu sanya mata su,sake baki sukayi suna bin kayan da kallo,suna mamaki don dai su a iya tsawon zamansu da Madam bata taba sanya wani kaya ba,bayan Suit,ko kuma wando da riga ko Sikat da riga,ganin yadda suke mamaki yasa tayi musu mirmishi tace”Ur Madam she now a bride today….”Tafada kai tsaye tana kallon Malika wacce ke zaune kan Stool kamar mutum mutum banda kwararan hawaye babu Abunda takeyi,kuma bata damu data saka hannu ta share,ba in ka kalleta sai kazata kamar wata wacce tayi loosing din memary dinta,
Zaro ido sukayi cike da murna suka ce”Wow…Congratulation Madame…”,Suke Fada bakinsu har kunne,ammh kuma jikinsu yayi sanyi ,Ganin yanayin madam din,da alamun dai bata marada da wannan Auren,ahaka suka sanya mata kaya,Abun mamaki sai gashi tayi kyau cikin kayanmu na hausa Fulani Fiye da na Turawan data ke sanyawa,Joda ita tayimata Dan Simple make up,wanda anayi tana Batashi da hawaye,ahaka aka gama,Ko motsi batayi ba kamar wata waccce lakanta ta cire bata wani karkashi.
Suna gamawa sai ga Hajiya binta tana Fadin suma su merry su Shirya kayansu dasu Alhaji yace za”ta tafi,kuma su daukan ma malika duk Abunta mai amfani kama daga abubuwanta na Sirri,ammh banda kayanta jikinsu na rawa suka koma ciki suna hada kayansu,Itako tana Zaune kamar an Dasata,sai ga Alhaji Abdulmalik ya shigo har cikin bedroom dinta ganinta haka bakaramin sosaimai rai yayi ba,karisawa yayi gabanta ya durkusa yana riko hannunta yace
MALIKA..… Yakira sunanta cikin taushin murya,dagowa tayi tana kallonsa,ammh kuma hawayenta basu tsaya ba,Mikar da ita yayi tsaye yana kallon kwayan idonta yace”Ki yarda dani mahaifinki ne? kuma kin yarda ni bazan taba yin Abunda zai Cutar dake ba…? Zuru tayimai takasa mgana illah Kallonshi datakeyi tana zubar hawaye,Hannunshi ya kara mikamata yana Fadin”In har kin yarda da Soyayyar dani ke miki malika,ki saka hannuki cikin nawa kizo muje na mika ki gidan mijinki….”,Yafada yana mikamata duka hannuwanshi…
Wajen yayi tsit,ana jiran ganin Malika zata mika ko a”a,sai kawai tabama kowa mamaki,jikinta asanyaye ta mika hannunta cikin na mahaifinta,lokaci daya tana sanya hannunta danashi ta share kwallanta,kafin ta dago Fuskar babu fara’a ko kadan ballatana Annuri,Damke hannuwansa tayi kafin ta Furta murya shake”I Truth u Daddylove….and am very srry For wht i did…”,Tafada kai tsaye tana kara nuna dakewarta,jin dadin kalamantane yasa ya Rumgumota yana sakamata albarka,tuni Hajiya binta ta mikamai mayafinta ya saka mata bisa kai,shi da kanshi ya durkusa ya zuramata takalminta mai Dubu ya riko hannuwanta suka Fito daga bedroom din Joda da Hajiya na biye dasu abaya rike da jakar Malika,sai Su Dose da kowacce kowacce rike da jakarsu su murna ta ciikasu zasu koma new House.
Ahaka suka fito har zuwa falon kasa,Gabadayan matan dake wajen suka mike suna sakin guda,waje fa ya rude,haka suketa reramata wakan… Ke kikace kina so,da baki ce kina so ba da bamu baki shi ba.. Ayyiriri guda ga Amarya zamu kaita Gidan miji zata kwana,zamu je musa kida muyita Tsalle…_ Haka suketa rerawa suna rawa da guda,itako Maleka tana Rumgume da Daddy tana jin kamar ta farka ace mata mafarki take ba gaskiya bane.
Haka aka Fice da ita,motar Daddy vibe 2k19 ya saka Malika agidan gaba,shikuma ya shiga mazaunin Direba domin shi zai kaita da kanshi,Sauran jama”a kuma suka shiga sauran motoci domin suje suba idonsu Abinci,lokacin wajen shida ne na yammah ana gabda kiran sallar mangariba.
Motar Daddyce tafaryin gaba,sai na Hajiya binta wanda Joda ke ciki da wasu yan”uwa,dai sauran ayarin motocin wadanda sukayi combain,tare da excorts din malika da motocinta,duka domin Alhaji Abdulmalik yace da komin ta zata tafi,cuz bayaso Malika ta chanza,yarda take rayuwarta na baya haka yake so Ta cigaba.
Suko su Saleem suma koda suka koma gida ya dinke da jama”a anata hidima nan fa lbri ya tashi na irin Dukiyar da’aka narkama Saleem da kuma kyauttukan da Alhaji Abdulmalik ya bamashi saleem,din nan fa wasu sukayita mganganu,donsu harga Allah daga Saleem din har iyayan nashi suna musu kallon kwadayi ne ya kaisu.
Shiko Saleem Dakinsa ya Shige ya kulle kansa,saboda cigaba da Shirinsa,baifi minti talatin da Shiga sai gashi ya Fito,da makullanyen gidan,da Daddy ya bashi dana motar da”aka bashi,da kuma anihin key din motarsa,wacce yake hawa,agaugauce ya samu Abbi ya sanar dashi cewa yanzun nan ya samu waya daga chan headquatersu na zamfara ana nemanshi da gaggawa so yanzu zai tafi ne,Abun yabama Abbi mamaki wani irin neman gaggawa ne haka,bai musa mai ba yamai Fatan alheri,ammh sun rabu akan in komai lafiya zuwa gobe zai tafi katsina chan wajen Amaryan tashi,haka ya shiga wajen Ummi yamata sallama,ana ta mai tsiyan ango guda bazai tsaya agama shagali ba,Shidai yake kawai yake baya mgana.
Sanda Sadiq yaji tafiyan Saleem zamfara yaso ya bashi yaki bashi dama,dole ya kyaleshi ya Shiga mota ya kama hanya,ya bar garin Abuja yakama hanyar zamfara,bayan yakira wata nomba yana Fadin”Inspector Saleh,gani hanyata ta zuwa zamfara juz tell me,karfe nawa flight dina zai tashi…?Banji me aka ce mai naji dai yace “Ok mu hadu a Airport din kawai…”Daga haka ya yanke kiran yana wani killer smile bayan ya sakarma motar gudu.
Awa biyu ya dauka kafin ya isa zamafara saboda gudun dayayi ko headqutern nasu bai shiga ba gidansa ya Wuce,lokacin anata sallar mangariba amsallatai Shiyasa ya tsaya yayi wanka yayi sallah kafin ya chanza kaya zuwa Uniform dinsa,lokaci daya ya koma aninihin ACP SALEEM KABIR KUMO,madubi yake kallo sanda yake kafa hularsa bisa kai Fuskarnan babu Annuri ko kadan.
Cikin Sauri ya dauki wasu takardu,sai pasports dinsa da kuma Atm dinsa ma,’ajiyar kudinsa kenan sai kudi Dollarwanda ya dauka baisan ko nawa bane ya zurasu cikin aljihu ,bai dauki kaya ko daya ba,ya Fito a gaggauce ya kulle gidan,bai bata lokaci ba Shiga cikin headquater nasu nan naga yana ta sallama da ma”aikatan wajen yana barin musu sallahu,Abun da yabani mamaki office dinsa kawai ya Shiga ya dauki wata takarda sai Syestem din shi wanda dukkan Abubuwan aikinsa naciki,ga duk alamu dai kamar Tafiya ce mai muhimmaci Saleem Zaiyi daga yanayin yadda yake musabaha dasu na bankwana ne,suna fatan Allah yabashi sa”a kuma ya dawo dashi lafiya.
Koda yabaro zamfara 7 da wani Abu na dare bai yi wasa ba ya sakarma motarsa gudu yanayi yana duba agogon hannunsa,domin so yake ya isa Katsina kafin goma na dare,domin jirginsa zai tashi ne da karfe 3:30 na daren yau din,jirgin dazai tashi daga kano zuwa kasar CHICAGO dashi aciki,shiyasa yake komai cikin hanzari kuma yana Fatan komai yatafi kan tsari kamar yadda ya tsara.
Alhaji Abdulmalik da kanshi ya Shiga Da Malika har kayatattacen dakinta wanda ya Shiryamata ya kuma mata masauki bisa gadonta,Fuskarta na rufe,ammh kuma tana kallon komai saboda mayafin nada sharashara,kanta kawai ya dafa ya shiga sakamata albarka kafin yayi musu addu”an zaman lafiya hawaye ne yaji suna Shirin tahomai shiyasa yayi saurin Ficewa.
Kowa son barka yake da gidan suna jinjina dukiyar da”aka kashe babu wanda aka bari ya dade duka Daddy ya tararra su su koma gidanshii,Hatta hajiya binta bata dade ba tatafi Joda ne ma sai daga baya tatafi,aka bar malika daga ita sai merry da Dose sai su peter dake Haraban gidan suna mazurai.