MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Shiko Alhaji Abdulmalik bayan ya dawo gida ya kira Abbi yana sanar dashi amarya tana dakinta,nan Yake sanar dashi kiran gaggawan da Saleem ya samu da Wajen aikinsa,bai nuna damuwarsa ba,saima fatan alheri dayayi mai yace zai kirasa yanzu,bayan sun gama waya yayi ta kiran wayar Saleem bata shiga,sai yayi Tunanin kila network ne,bai san ko Tuni Saleem ya saka nombarshi cikin black list din wayarsa,domin game din ya kusa karewa.

Itako Malika tana jin Diran Fitan motocin gidansu tayi zumbur ta mike tana karema dakin kallo,kayan jikintane suka dameta tafara kokarin cirewa bayan tayi jifa da dankwalinta Merry da Dose take kwalama kira,wadanda ke Falo,da gudu suka Rumtumo suna rawan jiki,Jikinta ta nuna musu tana Fadin”Oy up dis Cloths now..”Tafada cikin Tsawa,jikinsu na rawa suka Nufeta suna kiciyar ciremata less din dake jikinta,tsab suka tubeta suka barta daga ita sai pant,da bra wardrope suka bude suka daukomata wata doguwar riga ta roba,wacce bata da hannu suka zuramata,nan da nan ta lafe mata ajiki,ajiyar zuciya ya ta sauke tana baza gashin kanta da hannu tayi musu alama dasu Fice su bata waje,da hanzari suka Fice jikinsu na rawa da sabon Halin Madam dinsu,Fuskarta kwata kwata babu rahama,duk da ada Bata da mutumci,ammh na yau yafi na kullum.


Karfe 9:40 Na dare Saleem ya zuba hon abakin get din gidan da”aka zana amtsayin mallakinsa,Megadi yana lekawa yaga Shine da hanzari ya budemai get din ya sulala ciki,Koda ya isa parking space baiyi mamakin ganin motocin Malika ba,Cike da wajen ba,gefe daya kuma Exscort din tane keta shawagi suna zaro ido,dariya yayi cikin ransa yana ayyana Abubuwa da dama.

Ya dade cikin motan kafin ya Fito cikin azamarsa na cikakkan Namiji kulle motarsa yayi yana saka duka hannuwansa cikin,aljihun bakin wandon dake jikinsa,taku ya farayi zuwa kofaar da zata sadashi da cikin gidan,ko kallon Su peter bai yi ba,wadanda suka kame gefe suna mazurai domin Tun Fitowarsa daga mota kwarjinsa da haibansa ya dake su,Baya su ja suna ayyana kila wannan ne mijin madam ne,balle yadda suka ga ya hade rai kamar an aikomai da sakon mutuwa.

Cikin takama da isa ya sa kanshi Babban Falon gidan yana bin ko”ina da kallo,gabadaya Falon ya cika da kamshin Turaransa na MAN, merry da Dose dake zaune sukayi hanzarin mikewa suna kallonsa,ammh shi ko inda suke bai kallah ba,kuma bai tankasu ba,Steps yafara hawa Still duka hannuwansa na jikin aljihun wandonsa,Har zuwa Dakin daya Haddace cewa Shine na Malika.

Tura kofar yayi batare da yayi sallama ba,har ya Rufeta batayi motsin da zan agane wani ya Shigo ba, dan makullin dake jikin kofan yayi amfani dashi wajen Kulle kofar dashi,gefe daya kuma yana Saka key din cikin aljihub wandonsa, yana juyowa Da Malika yafara cin karo wacce ke kwance bisa gado,Ta na kallon kofa ta baza gashin kanta,Har ya Rufemata ido daya bayan idanuwan nata na Rufe kamar mai barci,ga santala santalan Fararen kafafun ta nan awaje saboda yanayin yadda ta kwanta babu inda ya boye na jikinta.

Kuramata ido yayi yana jin Wani daci tare da bakinciki na zuwamai,nan da nan Abunda ya faru Shekaru biyar ya dawomai kamar yanzu komai ke Faruwa,cikin takun natsuwa ya isa gabanta yadauki kafarsa daya mai dauke da bakin Takalminsa Sawu ciki ya aza bisa gadon,yana girgizashi da kafarsa daya.

Kamar amafarki taji motsi bata bude ido ba tace”Who..? azaton ta su merry ne,ammh sai taji Shuru ranta ne ya baci ya sanya ta bude lumsassun idanuwanta tana bin bakin takalmin dake ijiye gabanta da kallo,kafin ta daga idonta zuwa bakin wandon jikinsa har zuwa rigar Uniform dinsa har zuwa saman kansa,Yadda suka hada 4 eyes cikin wani yanayi na tsana da tashin hankali Saleem ke kallonta yayinda ita kuma Abun yazomata abazata,ammh sai ta dake tana daga kwance tace”Who are u? waya baka damar shigomin gida…?

Baiyi mgana ba illah Saukar da kafarshi dayayi kasa yana kara maida hannunuwansa a aljihu zagaye gadon yafarayi yana Binta da kallo,itama tana kallonshi ammh kuma tana jin jikinta na rawa saboda yanayin yadda yake kallonta,Uwa uba kuma wai yau itace tsaye da mai sanye da Uniform din yan Sanda adaki daya? kai ina imforsble,tafada aranta kafin ta mike ta sauko daga kan gadon da hanzarinta sai gata agabanshi.

Baya yaja kamar yana jin tsoronta kafin yace”No ba yanzu ba Hajiya Malika juz wait nayi miki wani bayani mana…’,Karo na farko daya yimata mgana Zuru tayimai tana kallonshi daga sama har kasa,Zagaye bayanta yayi kafin ya takaro kafarshi da gado,shikuma yasata a tsakiyarsa kafin tayi wani yunkuri ya daga hannu ya zuba mata wani lafiyayye mari mai zafi da gigitarwa wanda sai da tayi luuu zata kife bisa gado yasa hannu ya Fizgota yana huci yace”Kai ne ko? kai kabasu Umarnin su tsaremin motoci ko? Toh daga yau bazaka kara saka atare motocin wani ba,balle motocin Malika malik…”Yafada yana fitar da hucin mganar bisa Fuskarta,

Itako Suman tsaye tayi,ayayinda jini ke biyo hancinta da bakinta saboda yadda marin ya gigitata,kalamanshi take son Tunawa,ammh kafin ta samu damar Sakasu Acikin kwakwalrta ya sake kifamata wani marin kamar Allah ya aikoshi wannan karon bai hanata Faduwa bisa gadon ba,ya barta ta Fada,rajab tana Dafe duka kumcinta saboda Taga gilmawan wasu taurari,bai barta tayi motsi ba ya sanya Kafarsa daya ya take mata dan yatsarta daya ya murje,sosai wanda sai da ta saka ihun azaba da kuka,Hannu  ya sa acikin aljihu ya kwaso kudi dollars ya watsamata afuska yana Fadi cikin Tsawa…

  MALIKA MALIK…Sai na Rama…”! Kin Tuna don Ubaki ko sai nakara Tuna sar dake da duka?

“kin Tunda kakin da kika cima zarafi,..?kin Tuna kakin da kikace basu iya komai ba sai shaye shaye da yi mata Fyade,…?Kin Tuna sanda kika kirasu da Rubbish,..?

“kin Tunsa sanda kikace basu amsa komai ahannun mutane  sai na goro dana sigari,…?kin Tunda sanda kikace Basu da wani amfani akasarki,…?

kin Tuna…?

kin Tuna…?

Kin Tuna Hanyar Dutsenma zuwa katsina,Kin Tuna wani Saurayi da kika shararama mari,kuma kika sanar dashi haka..? Kin Tuna ko baki Tuna ba yanzu na kara Tunasar dake….?

Yafada yana kara murjemata yatsu,bayan ya zubamata manyan idanuwansa wadanda suka suka koma jawur saboda Bakinciki.

Malika data ga Lahira kusa tana ihun azaba ta Furta”Na.Na……Na TU….Tu..Nah….,”Tafada wani tsoro Na Shiganta lokaci daya.

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Shakira.

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Littafin MALIKA MALIK Na kudi ne ki biya akan Naira 200kachal????ki turo ta account Nomba kamar haka 0552179550 JAMILA UMAR GTB bayan kin dauki hoton Sreenshoot din Transaction din,sai ki turomin ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488 shima kai tsaye bayan an dauki hoton katin sai aturo*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button