MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

  NI SALEEM KABIR KUMO NA SAKI EX-WIFE DINA WATO MALIKA MALIK,SAKI DAYA BISA DALILIN CEWA BANTA SONTA BA,ASALIMA NA AURETA NE DON NAYI ALQAWARIN SAI NA RAMA,TOH SHINE BAYAN NAGAMA RAMAWA,NA BATA TAKARDANTA KADA TA DINGA GANTALI DA AURENA AKANTA,ANA ZAGINA,TUNDA TAGAMA MIN AMFANI GWARA NA SAUWAKE MATA,DAGA KARSHE INA MAI NEMAN AFUWARKA DADDY,DAKAI DA IYAYENA BA LAIFIN KOWA BANE SAI MAHAIFINTA DOMIN SHI YA BATA TARBIYAR YARSHI DA KANSHI,DAGA KARSHE INA MAI SANAR DAKU SAI TAYIMIN IDDA,DOMIN NASAN KO BAN FADA BA ZAKU GA ALAMUN NA DORA MATA NAUYINA,GA KEYS DIN GIDANKA DANA MOTARKA NAN BANA BUKATA DAMA ABUNDA NAKE BUKATA KENAN,KUMA NAGAMA AIWATAR DA GUDURINA SO YANZU D GAME IS OVER NOW

                                 Ex huband din yarka Saleem kabir kumo

Haka ya rattaba kafin ya Kamo hannunta ya sakamata cikin tafinta ya damkematashi na tsawon lokacin kafin ya saki,duk da hannu yayi taushi,ammh takardan ta samu matsugguni,mikewa yayi yana gyara tsayuwarshi kallonta yake kafin koma yakoma ya duka ya saka kanshi saitin zuciyarta,sai yaji yana harbawa ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ciro makullin gidan dana motocin guda biyu ya Zubesu bisa jikinta,ko kara kallonta baiyi ba ya saka kai ya fice ransa fayau yana Fadin D game is over Now…..” Yafada yana Ficewa da sauri.

Abun da ya bashi mamaki su merry na Zaune basuyi barci ba,suna ganin Fitowarshi suka mike suna zaro ido,wani banzan kallo ya watsa musu kafin ya wucesu da sassarfa har ya kusa Ficewa Daga Falon ya waiwayo yana kallonsu,Suko suna ganin ya juyo suka kamkame juna jikinsu na rawa,saboda yadda idanuwansa da Fuskarsa suka basu tsoro,tsaki yaja yana Fadin”Oya…”

Yafada yana nuna musu saman Dakin Malika Baima kai ga mgana ba,suka Rumtuma saman da gudu,domin duk ihun da Malika tayi akunnensu,suma tsoro ne yakamasu suka kasa komai,Yana ganin sun nufi sama ya Fice daga falon da gaggawa,Yana zuwa yayi ma motarsa key bai ga kowa ba,kila su gardawan nata sun gaji ne sun kwanta,ya Shiga motarsa hon ya zubama megadi wanda yazo da hanzari ya wangalemai get ya Fice yana kokarin daurama kanshi Seat belt,daidai lokacin daya duba agogon ahannunshi 1:30pm na dare, kawai sai ya karama motar speend,nan da nan ya Fice Daga garin katsina.

Hanyar garin kano ya nufa adaren Ransa Fes sai zuga gudu yake yi Abunshi hankalinshi kwance,cikin  awa daya da rabi sai gashi ya isa cikin babban filin jirgin MALLAM AMINU INTERNATIONAL AIRPORT Yana kokarin fakin din motarsa ne,naga wani wanda ke sanye da bakaken kaya ya, kariso wajen motan,da hanzari ya Fito,bayan ya leka baya ya dauko jakarsa ta brief case dinsa ya sagala akafadansa hannu ya bashi sukayi musabaha,kafin ya mikamai pasport dinshi tare da Visarshi yana Fadin”Yallabai saura minti Talatin ne jirgin naku ya tashi,so zaka jira wajen da masinjoji suke jiran tashin jirgi..”…

Jinjina kai yayi kafin yace”Tanque So much Inspector,aikin ka na farko ya kammallah,saura na karshe plz kafin safe ka tabbatar ka yada wannan lbrin akafafen yada lbrai,kaji ko..”Amsa mai  yayi da Fadin”Insha Allahu yallabai da zarar jirginku ya tashi zanyi yadda muka tsara,Allah ya kaiku lafiya.”Hannu suka kara rikewa kafin Saleem ya damkamai key din motarshi yana Fadin”Sai kajini…”daga haka suka rabu,shi yafada motar Saleem din,shiko saleem ya nufi cikin Aiport din, da sassarfa,daga ganin yadda yake tafiyan zaka san yana cikin niahadi ba kadan ba.

  _____

Dose da Merry,suna bugan kafadan Juna wajen Shiga dakin,Suna shiga suka tsaya agabanta,suna jiran Umarni Tunda sun saba haka take musu,ammh sukaji Shuru,Dose ce ta lura da halin da madam ke ciki afirgice ta nunama Merry jinin data gani ya bata ko”ina.

Tsorata sukayi suka nufeta atare,suna Fadin’Madam..Madam…”Shuru ba mgana,hannunta suka daga yakoma ya kwanta baya Dose taja baya tana FAdin”,Jesus….” Tafada a firgice kamar zata Shide,Kafin ta kalli Merry bakinta na rawa tana Fadin”She is death..”Girigiza kai merry tayi Hankalinta amatukar tashe ta Rumtuma tafito daga dakin Dose ta mara mata baya,suka fito har haraban gidan suna ihu da kuka,sai gasu peter sun Fito suna mazurai.

Suna tambayansu Lafiya,ammh sun kasa mgana sai nuna cikin gida suke suna kiran Sunan Madam,Suma kansu Firgita sukayi Joy keda Nombar Alhaji da hanzari ya latsashi ya kirashi,shiko Daddy yana kwance baisan dalili ba yakasa barci saboda yadda gabanshi yake fadi,sai ga wayar joy,Tunda yaga nombarsa hankalinsa ya tashi da azama yadaga kiran tun kafin yayi mgana joy yace”Alhaji come now,Something bad is happen wit madam oo…”Yake Fada Shima cikin rawan jiki,ko kafin Daddy ya samu zarafin mgana ya yanke wayar.

Agaggauce ya sauko daga kan gadon jkinsa babu inda baya rawa,Hajiya binta ya bubbuga yana Fadin”Hajiya.Hajiya…”Da Sauri tatashi tana mutsike ido take Fadin”Lafiya Alhaji…? Jallabiyansa yake zurawa yana Fadin”Ina fa lafiya,yanxu nan masu tsaron malika suka kirani,wai babu lafiya wani Abu mara kyau yafaru da madam..”

Da wani hautsinawa Hajiya ta diro daga kan gadon tana kokarin yayiman Mayafinta ta aza bisa rigar barcinta tana Fadin”Innalillah..Toh meya faru ne..? Take Fada ammh kafin ma takara cewa wani Abu,Alhaji ya fice da hanzari,Hajiya binta tabishi da hanzari bayan ta dauki Makullin motar dake kan Side drower saboda Rudewa bai tsaya dauka ba.

Ba wanda yasan Fitarsu domin lokacin 4 saura ne na Asuba,hankalinsu tashe suka isa gidan,ko da suka isa sun iskesu duka aharaban gidan,ganin yadda su merry ke kuka ne,yasa daga Daddy har hajiya suka Rumtuma zuwa cikin gidan kamar zasu Ture juna,Daddy shi yafara shiga dakin na Malika halin daya gantane,yasa ya tsaya cak,jikinsa na kyarma,hajiya binta ne takarisa gareta tana karemata kallo daga sama har kasa kafin ta dago hannunta tana Fadin”Malika..Ke malika…”Taji Shuru baya taja ta goge zufan jikinta take Fadin”Allah sa badai kasheta akayi ba…

Fadar haka yayi daidai Da Daddy ya zube kan kafafunshi yana kiran Sunan Allah,Hajiya binta ma Salatin dake,sai alokacin idonta yakai kan jinin dake gefen kafafun Malika da hanzari ta jaye rigar jikinta,Salati ta saka tana Fadin”mun Shiga uku Alhaji Wlh Fyde akayi ma Malika…”,

Jin haka yasa ya mike yana Fadin”Fyade kuma? ya maimata cikin Fitan hayyaci,Gyadamai kai tayi hawaye na zubomata,Hannun Malika ta gani yana matso tayi saurin zama kusa da ita tana dagota tace”Alhaji da Ranta duba kagani hannunta na motsi…”Shiko hankalinshi baya wajenta yanaga makullayan gida dana motar daya damkama Saleem su dazu da rana,mai yakawo su zube kan gadon Malika, Bai gama mamaki ba,ya hangi wata Farar takarda tana kokarin Fadowa daga hannunta lokacin Da hajiya binta ke kokarin dagata tana Fadin”Alhaji tsayuwa ba namu bane,kamata muje asibiti…”…

Kamar wani yajashi sai gashi gabanta ya saka hannu ya dauko takardan Jikinsa na rawa ya warware yafara karantawa a bayyane,ko kafin ya gama hawaye sun gama jikamai Jiki,ga wani jiri dake dibanshi sai daya Dafa bango yana kiran sunan Allah,Hajiya binta ta fashe da kuka tana Rumgume da Malika take Fadin”Kagani ko Alhaji,dama wannan Ranar nake jiyemaka Ranar dakai  Da malika zaku fara girban Abunda kuka Shuka,meyafi wannan Cin zarafi,ace aci mutumcinka adaren aurenka,kuma abaka takardan saki adaren…? take Fada tana kuka harda majina,Shiko Alhaji Abdulmalik zaman dirshan yayi yana kuka Wiwi kamar karamin yaro.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button